← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 75

Sashe 1

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"To sun ce ba sa jin barci ki rabu da su."

Baffa ya shigar musu shi yasa ta ƙyale su, ta tafi ɗakin Baffa ta tafi da ruwan gora saboda yana shan ruwa da daddare.
Ta bar su a falonta suna dasa sabuwar hira har da Baffa shima komawa ya yi ya zauna.

Ammah ta sake dawowa ta gansu dirshan suna hira.

"Yau wai meke damun ku? Baffa mu je ka kwanta ka ƙyale yara nan."

Baffa ya amsa da to, Saddam ya kalli Abdurahim suka kalli juna suna kunshe dariya.

"Munafukai."

Ammah ta faÉ—a tana hararansu.
Suka kwashe da dariya Baffa na mirmishi.

"Ammah Baffa fa ba ya jin barci."

"Ya faÉ—a maka?

"To ga Baffan nan a tambaye shi? Baffa wai kana jin barci?

Saddam ya juya yana tambayan Baffa.

"To ko ban ji Saddam tunda Jamila ta ce ina jin barci ai haka ne gaskiyan magana."

"Baffa kai fa mijin ta ce ne na lura."

In ji Abdulrahim yana dariya.

"A'a ba mijin ta ce ba ne shi, mijin kan ta ce ne."

Saddam ya gyara masa, Ammah ta wurgesu da cussion É—in kujera tana cewa su fitar mata a cikin É—aki su kuma suna ta dariya.

"Ammah gaskiya fa muka faÉ—a. Duk abin da kika ce Baffa ba ya iya miki gaddama."

"Ku kuma kuna jin haushi.?

"Aa kawai dai shima Baffa ya dinga nuna ƙwanjinsa."

Baffa na ta dariya ita kanta Ammah dariyan take yi.
Saddam da Abdulrahim shaƙiyan yara ne haka suke tasa su da zolaya.

Baffa ne ke faÉ—a musu, su yi fatan samun mace irin Ammah dukkansu mijin kan ta ce za su zama.

"Tana da kyakyawan hali misalin mace ta gari ce Jamila."

"Awwww.."

Suka haÉ—a baki wajen faÉ—a ganin Ammah na ta mirmirshi jin Baffa na yabon ta.

"Su Baffa an iya kalamai."

Saddam ya faÉ—a yana tsintsira dariya.

"Ammah da kalaman nan ne Baffa ya sace zuciyarki?

Ta wurga masa harara tana mirmishi.
Baffa ne ba su labarin ai haÉ—a su aka yi kuma suna haÉ—uwa ganin farko suka aminta da juna.

"Love at first sight kenan."

Abdurrahim ya faÉ—a yana dariya.

"Ammah ta ga farin bafillace ina za ta yi sakaci."

"A'a itama ai fara ce, ni ne na yi sa'a."

Baffa kenan yana ta wasa Ammah kunya ta ji ta bar musu falon su kuma su Saddam suna ta dariya.
Da gaske yau hira suke ji domin har É—aya saura na dare suna falon Ammah suna hira.
Saddam kawai ya sako wata maganar wai yanzu sai Baban Hanan ya zo ya ce Hanan É—iyar shi ce?

"Haba ai da kunya. Shi da ya ce baya son cikin ?

"Irin su ba su da kunya ina nan da kai zai iya dawowa ya ce ina abin da Auta ta haifa."

"Ai ko da ya ci ubansa wallahi."

Abdulrahim ya faÉ—a da iya gaskiyan shi.
Baffa na gefe bai ce komai ba cigaba da magangansu suka yi Saddam na faÉ—in shi jiran ranar kawai yake yi ranar da Habib zai sako kafarsa a gidan nan sai ya tara matasa anguwa sun yi masa jina jina.
Abdulrahim ya ce daga karshe mu haÉ—asa da jami'an tsaro.

Ammah ta fito lokacin da suke auna irin iziyar da za su yi ma Habib duk ranar da tautsayi ya kawo shi gidan nan.

"Ni na manta da shi, koma yana ina yanzu na tabbata Auta ta fi shi samun rayuwa mai inganci. Ai ba za ka yi zalunci ka sha ba sai Ubangiji ya yi sakkayya tun a duniya."

"Ai Ammah yana can ma yana girban abin da ya shuƙa. Irin addu'o'in bala'in da na dinga auna ma wannan mutumin ai in dai Allah ya karɓi addu'o'i na to yana cikin iftila'i."

Ammah ta ce har Umra ta je ta yi addu'an Ubangiji ya yi ma Auta sakayya kuma da ikon Allah yana can yana gani.

"Kuma wai ko danginsa ba su sake neman ku ba Ammah.?

Abdulrahim ya tambaya.
Ammah tace ba wanda ya sake neman su, ai in shi Habib ya ce ba ya son cikin bai kamata su su juya baya ba tunda sun san jinin su ne.

Sai a lokacin Baffa ya yi magana da cewa shi ya yanke alaqar daga farko.

"A baya ɓacin rai da ganin halin da Auta ta shiga ya sa na ce na haramta ma Habibu da danginsa abin da Auta za ta haifa. Amma daga baya na fahimci na yi kuskure, Hannatu mace ce duk iya abin da za mu yi mata tana bukatar Uba da danginsa."

Kallon Baffa kawai suke yi mamaki ya hana su magana.

"Ko ba a ba shi y'arsa ba watarana ina da rai ko ba ni rai in har Habibu da danginsu suka waiwayi jininsu ku karɓesu ku kuma ba su dama"

"Dama kuma Baffa? Wani irin dama kuma?

Ammah ta tambaya cikin mamaki.
Received at 09:09Reactions: ❤ 9, 👍 1, 😱 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Damar ya nemi afuwarku sannan ku ba shi dama ya haÉ—u da jininsa."

"Cewa ya yi ya gane ya yi kuskure Baffa? Kuma cikin da ya ce ba ya so ne za ka ce a ba shi dama ya ga jininsa?

"Ban sani ba amma ina ji a jikina lokacin ya kusa. Ko da ina rai ko ba ni da rai wasiyya ce Jamila. Hannatu mace ce wata rana za ta yi aure tana bukatar mahaifi da dangin shi in har Habib ya gane kuskuren shi ku karɓe shi ku yafe masa muma mutane ne muna yin laifi Ubangiji na yafe mana to babu laifi in ya yi laifi kuma ya gane kuskuren shi ya tuba."

Da alamun maganganun Baffa sun sanyaya musu jiki har da Ammah ita kanta

"Baffa ni ban gane maganganun ka ba, ka haÉ—u da Habibun ne ko ya kira ka a waya ne?

"A'a ban sake ganin shi ba kuma da ya kira ni da na faÉ—a miki. Kawai tunasarwa ne domin na san ko a jima ko a daÉ—e Habibu zai dawo ya nemi Ummu Salma tare da bin kadin cikinta jikinta. Jininsa ne zai yi nadama ko kuma alhaki zai bibiye shi, alhakin ne kuma zai kawo shi nan kusa."

"In har ya zo kar ku yi masa rashin É—a'a. Ku yi masa kara sannan ku ba shi dama. Muma damar Ubangiji ke ba mu da babu wata damar da duk rayuwarmu ba ta kawo yau cikin farinciki ba."

Shuru suka yi kowa na saƙa maganganun Baffa a zuciyarsa

Ammah dai cewa ta yi Baffa na jin barci ya zo su kwanta sai ya miƙe yana faɗin kanshi ke ɗan ciwo ta duba masa panadol.
Saddam da Abdulrahim suka miƙe suka fita tare da Baffa suna yi masa sallama.

"Allah ya tashe mu lafiya."

Suka amsa da Amin suka tafi bangaren su

Baffa kuma ya shiga É—akinsa tiolet ya shiga ya kama ruwa ya zo ya sauya kaya zuwa jallabiya ya kwanta Ammah ta shigo da maganin ta tashe shi ta bashi ya sha ya kora da ruwa ya koma ya kwanta.

Ammah ta yi zuru tana kallon shi domin a cikin lokaci ƙalilan sai ta ga duk Baffa ya sauya ya yi wani sanyi da shi.
Da ta tambaye shi sai ya ce ciwon kan ne ya É—an dame shi.

"Kuma shi ne tun É—azu ba ka yi magana ba? Ko rashin barci ne Baffa?

"A'a yanzu nan ne ciwon kan ya fara amma na san zuwa safe zai bari.'

Ta yi masa Allah ya sauwaƙe
Ta rufa masa bargo a kafafunsa sannan ta yi shirin barci itama ta kwanta bayan ta je ta rage hasken falonta ta rufe falon.
Kofar turakan Baffan ma sakayawa ta yi, saboda ana sanyi ba ta kunna fanka ba.

Itama ta gaji shi yasa tana kwanciya sai barci.
Can cikin dare ta ji Baffa na kiran sunanta.

Ta tashi cikin barci ta ji yana cewa ta kunna masa fanka zafi yake ji.
Ta yaye bargon ta sauko daga kan gadon ta kunna hasken É—akin

Sai ta ga Baffa na ta zufa abin mamaki sanyi fa ake yi.
Ba ta yi musu ba ta kunna masa fankar tana duba agogon bangon dake É—akin Baffa uku saura na dare.
Gefen Baffa ta zauna tana miƙa hannu tana share masa gumin da ya taru a saman goshinsa.

"Baffa ciwon kan ne?

Sai ya É—an buÉ—e idanuwansa yana kallonta.

"Na ga kana ta gumi ne! Ko akwai zazzaɓi a jikin ka ne?

Ta faÉ—a lokaci É—aya tana dafa goshinsa.
Sai ta ji jikinsa ya É—an yi É—umi.

"Baffa ina jin zazzabi ne zai kama ka jikin ka ya yi É—umi."

"Ba komai ki koma ki kwanta."

Baffa ya faÉ—a a sanyaye muryansa ta yi wani iri.
Ammah ta ji kawai gabanta na faÉ—uwa ko Baffa na ciwo bai saba yi mata magana da wannan muryan ba.
Sai hankalinta ya tashi ta fara cewa ko ta ƙaro masa maganin ne ya yi mirmishi ya ce ciwo kan ya sauka kawai zafi ne yake ji ta koma ta kwanta.
Ba ta yarda ba sai da ya rike hannunta duka biyu gam a cikin hannayensa.

"Ki koma ki kwanta na ji sauƙi zafi ne kawai na ke ji kuma da kika kunna fankar ba ki ga na daina gumin ba."

Ba ta kwanta ba zama ta yi da shi tana riƙe da hannayensa.
Abin da ya ƙara tsorata ta ganin ga iskar fanka amma shi yana ta gumi ita ke share masa gumin ma da hannunta.

Zuwa can kuma sai ya samu barci sai da ta ga yana mumfashi a hankali sannan ta koma ta kwanta a zuciyarta tana faɗin da sassafe za ta kira Baba ya zo su je asibiti da Baffa ba ta taɓa ganin ya yi irin haka ba.
Chapter 1 · 0% Book details