← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 75

Sashe 14

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wasiyar Baffa ne, a daran da zai rasu tare da ni da su Saddam ya faÉ—a mana in sun zo mu saurare su in sun nemi gafara mu yi musu afuwa."

Tunda ta ce wasiyar Baffa ne ba wanda ya kara magana
Ummu Salma ta ja Hanan suka shige ciki BaÉ—É—o ta bi bayanta.
Haushi take ji, me ya sa Ammah za ta ta ce a saurare su ta sha roƙon Allah kar ya sake haɗa ta da Habib ko Shamsiya.

Ba ta ƙaunar su san ma abin da ta haifa balle ya zama yana da alaƙaa da su.
Sai ga shi komai ya kwaɓe mata. Ba ta jin za ta iya yafe ma Habib da Shamsiya sun cutar da ita.

Kulle É—aki ta yi saboda Hanan na so ta fita.
Ummu Salma kuka kawai take yi komai ya dawo mata sabo. BaÉ—É—o kuma mamaki kawai take yi na ganin Shamsiya a haka.

"Tab rayuwa Sisna kin ga yadda Shamsiya ta koma?"

Tana jin ta ba ta yi magana ba. Ba wannan ba ne a gabanta ita haÉ—uwa da su ne ba ta so.
Fargabanta ma Hanan ne, za ta iya yin komai domin Hanan ba ta kasance tare da su ba har abada.

*Janafty*
Received at 10:01Reactions: ❤ 16, 👍 2, 🥰 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.

Tunda har Ammah ta ce su shigo a ba su dama sannan a saurare su ba wanda zai yi musu da ita. Ko lokacin Baffa na raye ba ya musa ma umarnin Ammah balle kuma yau da ba ya raye maganar Ammah tana saman na kowa duk abin da ta ce shi za a yi. Balle kuma ta ce wasiyar Baffa ne.

Hamma Abdullahi ya mayar da fusatar shi ya fita can haraba in da su Hamma Jibo ke tare da su Alhaji Sharif ya ɗan duka ta wajen kunnensa yana faɗa masa saƙon Ammah.
Shi daman Hamma Jibo É—an sauki ne ya ce a saurare su.

Hamma Abdullahi ne da Hamma Abdulrahaman sune ke ta bala'i Allah ya sa ma tun a farko ba su gane su ba da ko gaisuwan da suka yi musu ba za su amsa ba.
Su uku ne daga Alhaji Sherif sai Baba Usman sai Habib ɗin da yake ta raɓe raɓe yadda rayuwa ta mayar da shi ne da kuma daman ba wani sanin shi suka yi ba shi ya sa ba su gane shi ba gwara ma Saddam shi ya je gidan Ummu Salma ba adadi sun sha haɗuwa da Habib ɗin amma shi da farko bai gane shi ba sai daga baya ya fara masa kallon sani.

Hamma Jibo kuma ya so ya gane Alhaji Sherif tunda sun taɓa zuwa da Baffa a wancan lokacin amma ya kasa kama suna ballatana ya tuna in da ya san shi. A tunaninsu kawai masu zuwa gaisuwa ne tunda har gobe kafa ba ta ɗauke ba.

Amma sai suka ga bayan sun yi gaisuwan sun yi shuru. Hamma Abdullahi ya fusata ne lokacin da Alhaji Sherif ya gabatar da kan su a matsayin dangin Habib É—in tare ma da Habib É—in sai a lokacin ma suka gane shi.
A lokacin Hamma Abdullahi ya ta shi a fusace ya shiga gidan yana sanar da Ammah abin da ke faruwa.

Hamma Abdulrahaman ya ce su ba za su saurare su ba su ta shi su tafi kawai. Hamma Jibo ne ya ce su É—an dakata tukunna. Habib kawai suke kallo lalle rayuwa juyi juyi na gaba ya koma baya.

Tun daga kayan dake jikin Habib ba sai an faɗa musu ba sun san rayuwa ta juya masa baya. Kallon reni da wulaƙancin ya sha shi a wajen su Hamma Abdullahi.
Lamiɗo ko kallo ɗaya ya yi masa bai ƙara ba wani abu na yi masa rawa a zuciya na haushi da kishi.
Habib kuma ya kasa magana ya kasa haɗa idanuwa da su domin sun yi masa ƙwarjini ga kunya ga nadama sun taru sun natsar da shi a waje ɗaya ba domin Alhaji Sherif ba tabbas zai iya tunkara wannan gidan ba.

"Ku yi hakuri don Allah, mun san abubuwa sun faru a baya mara sa daÉ—i. Ku É—an ba mu lokaci ku saurare mu ku ji da abin da muke tafe da shi."

Alhaji Sherif kenan yana sake roƙon su Hamma Jibo ganin ba su yi maraba da zuwan su ba. Ya san daman haka za ta faru shi ya sa ya ce shi ba zai zo ba. Darajan tsufan Gwaggo ya duba da kuma bakin da matarsa Hajiya Sahura ta saka sannan tare da nadamar Habibu shi ya sa kawai ya amince zai zo amma tabbas abin da ya faru a baya ba mai daɗi ba ne ko shi ne a matsayinsu abin da zai aikata wataƙila sai ya fi na su shi yasa ko kaɗan bai ji haushin su don sun ce su bar musu gida ba.

"Ba komai. Mahaifiyarmu ta ce ku shiga ciki domin a zauna a yi magana."

"Allah Sarki mun gode. Allah ya saka da alheri."

Saddam aka tura cikin gida ya fara sanar da su Ammah shigowar maza.
Daman falon daga Ammah ne sai Umma Balki da Ummin ikki. Sai Mami sai su Gwaggo da Shamsiya da suka zo daga baya.
su Adda Nauwara suna dawowa daga makabarta suka bi su Adda Suwaiba gidajen su.

Islam kuma tana ɗayan ɗakin tana ta fama da waya a hannunta. Ummu Salma kuma tana ciki ta rufe ƙofa ita da Baɗɗo da Hanan.

Daman da hijabai a jikinsu sai kawai suka ce su shigo.
Hamma Jibo ya yi ma su Alhaji Sherif jagora har falon Ammah shi dai a saman kujera ya zauna tare da Baba Usman amma Habib a ƙasa ya zauna daga can gefe ya takure ko idanuwana ya kasa ɗagowa.

Ammah kallo É—aya ta yi masa ta kauda kanta haushin shi take ji a baya amma a yanzu da mutuwar Baffa ta gama zare mata jin haushin kowa tausayin ma ta ji ganin yadda ya koma.
Received at 11:37Reactions: ❤ 14, 🥰 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ummin ikki kan haka take hararan shi bai sani ba tunda kansa na duƙe ne, Mami dai fuskar nan ba fara'a ba domin an ce wasiyyar Baffa ba ne da itama ba za ta amince da zuwan waɗanan mutanen a gidan su ba.

Su Hamma Jibo ma duk sun shigo sun zazzauna. Hamma Kabiru na kusa da LamiÉ—o.
Shi kuma yana fusƙarta ɗakin da Ummu Salma take ciki ne yana tunanin halin da take ciki wataƙila ma tana can tana kuka haka kurum zuciyarsa ta fara zafi yana jin ɓacin ran da bai san dalili ba.

Bayan gaisuwa da kuma ta'azziya Alhaji Sherif ya kalli Hamma Jibo yana faɗin ina mahaifiyar ta su take anan? Hamma Jibo ya nuna masa Ammah dake zaune a ƙasan cafet da Hijabi.

"Sannu Hajiya Allah ya gafarta masa Allah ya sa ya huta."
Ammah ta amsa da Amin Amin.

"Mun gode Allah ya ba da lada."

Sai falon ya yi shuru, Shamsiya ce kawai ake jin É—an jan majinanta na alamun tasha kuka.

Alhaji Sherif ya juya kaf bai ga Ummu Salma ba ya san ta tunda lokacin in dai Habib zai zo gaishe shi tare suke zuwa kuma abin da suka zo da shi ya shafeta ya kamata duk abin da za a tattauna tana wajen, Habib ya ba shi tabbacin an ce duka suna gida saboda wannan rashin da aka yi musu balle ma ya ce ai É—an gida take aure yanzu.

"Na ce in ba damuwa ina son duk abin da za mu tattauna a nan wajen a ce ita wacce abin ya shafa tana wajen nan."

Alhaji Sherif ya faÉ—a yana kallon fuskokin su Hamma Jibo.

"In ba damuwa ina so ta fito itama domin abin da ya kawo mu saboda ita ne."

Ammah ta ce ba komai, Mami ta yi ma magana akan ta kira Ummu Salma.
LamiÉ—o kamar ya ce ba sai ta fito ba sai kuma kawai ya fasa bai yi magana ba.

Habib kuma tunda aka ce aka kira Ummu Salma kirjinsa ke duka.
Shamsiya kanta na kasa tana tsiyayar hawaye ko daga ganin Ummu Salma ta san ta ga cigaba a rayuwarta sabanin su, to ko ba ta faɗa ba ita fa ɗan Sarki take aure wani jin daɗi ne ba ta cikin sa. Ita da suka cuta ne ita ce Ubangiji ya yi ma sakayya su kuma da suka cutar da ita sun girbi gwargwadon abin da suka shuka in da suka gode ma Allah sun yi saurin gane kurkurensu sun tuba ba sai lokaci ya ƙure musu ba.

Sai da Mami ta yi knooking ƙofar sannan Baɗɗo ta tashi ta buɗe mata, duk da Umma Salma na mata tsawan kar ta buɗe ta yi banza da ita ta zo ta buɗe ƙofar sai ga Mami ta shigo cikin ɗakin

Ta samu Ummu Salma na zaune gefen gado tana ta kuka ga Hanan ta saka kafafunta ta matse ta, ta hana yarinya kuka sai hawaye take yi, domin cewa ta yi in dai ta yi mata kuka sai ta yi mata duka shine Hanan ta kama bakinta amma tana ta hawaye tana son fita ne Ummu Salma ta hana ta.

"Me ye haka?

Mami ta faÉ—a tana jawo Hanan daga kafafun Ummu Salma.

"Mami kin ga ni ko! Tun ɗazu nake yi mata magana tana ƙin kula ni."

Baɗɗo ta gama faɗa cikin jin haushi. Ita fa ba zuwan su Habib take ji ma haushi ba sai Umma Salma meye na zama kina kuka a kan waɗanan mutanen? A yadda ta ga Shamsiya tun kafin ta ga Habib ta san haƙƙin Umma Salma bai bar su sun zauna lafiya ba.

Mami ta hau share ma Hanan hawaye wacce ta yi lamo a jikinta tana sauke ajiyar zuciya.

"Ba ki da hankali ne Ummu Salma.?

Mami ta faÉ—a tana mai kallon ta. Sai kawai ta fashe da kuka har da sauti.
Chapter 14 · 0% Book details