← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 75

Sashe 73

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ta ce ta ba shi tun yana ƙarami har abada ta yi kyautarsa ba ta taɓa nuna duniya ɗanta ba ne. Har Kaduna suna zuwa da yara su yi mata hutu Ammah na Jimeta, tunda ta ƙi yarda ta dawo Daura ta zauna.
Shekara ɗaya da rabi kenan Hamma Saddam ya yi aure, ya auro buzuwa daga adagex gashinta har gadon baya amma irin baƙaƙen buzayen nan ne masu kyau suna zaune a garin Abuja, amma ya gyara bangaren su na gida Jimeta nan suke sauka in sun je gida, Ammah girma ya zo amma tana cikin jin daɗi Baɗɗo haihuwanta uku duka maza su Adda Suwaiba ma duk suna zaune lafiya Hamma Abdullahi ne ya gaji Baffa tunda daman tare suke kasuwanci ya cigaba da gudanar da kasuwancin su har kuma gobe komai Mai martaba Lamiɗo zai yi ta hannun Hamma Abdullahi ne akwai amana a tsakaninsu.

Sannan duk da yanzu LamiÉ—o Sarki ne Amincin dake tsakaninsa da Hamma Kabiru bai rusuna ba.
Shi ne amininsa da zai iya tattauna komai na shi da shi. Hamma Kabiru da iyalansa suna zuwa Daura su yi musu hutu duk lokacin da suka samu sarari suma suna zuwa tunda har naÉ—in sarauta Lamido ya yi masa maji daÉ—in mutanen Daura.

Rayuwa ta yi kyau sai dai godiya Allah Baffa shekarar sa tara kenan da rasuwa amma har a wannan lokacin mutuwarsa na yawan fami ga iyalansa Baffa Salihu ma ya rasu shekaru biyu kenan yanzu Baffa Umaru ne kaÉ—ai ya rage su Umma Balki duk suna nan suna cikin godiya da aminci. Ummi ikki da Ammah amintarsu tun na yarinta babu abin da ya canza sun manyata amma kuma amintarsu bai yi rauni ba.

Rayuwa juyi juyi na gaba ya koma baya, an yi wayi gari yanzu Ammah ba ta wannan rawan jikin ga Bilkisu. Ita dai Ummu Salma ta ga canji sosai ta yi mamakin me Bilkisu ta yi ma Ammah! Duk da ko a fuska ba ta nuna wani abu amma ta rage zaƙewa kan lamarinta ko rawan jikin in suka zo Jimeta, tana so ta yi ma Ammah magana sai ta sha'afa sai da Baɗɗo ta faɗa mata abin da ya faru ta san ba banza ba canjin Ammah, ashe tun tana da cikin Banafsha, lokacin da matar mai martaba sarkin kano ta rasu, Ammah ta kira Bilkisu a waya ta yi mata gaisuwa bayan sun gama mgana ita Ammah ba ta kashe wayar a can bangaren ba, haka itama Bilkisu ta ɗauka Ammah ta kashe ne, ana ta mganar Ummu Salama da su Gimbiya Hadiza, Bilkisu ta buɗe baki ta ce ta tsani Ummu Salma da iyayenta da mganganun da take yi na raina su Ammah, ba ta san Ammah ta gama ji ba tas sannan ta kashe wayarta, Ammah ashe ta sha kuka jikinta ya yi sanyi, ta kasa faɗa ma kowa
Received at 08:05
13 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
kar a yi mata dariya.

Da Ummi ikki kawai ta tattauna mganar ita kuma ta ce ishara ce, gwara ta riƙe ƴaƴanta Ummu Salama dai ɗiyarta ne, haka ma Lamiɗo, Bilkisu kuma ta bar ta da halinta ga ta ga duniyar nan, Ummu Salama kuma da Lamiɗo kuma smutu ka raba. Shike nan Ammah ta kama kanta, yanzu kawaicin duk da take yi ma Auta ta rage sosai da Baɗɗo ke ba ta labari ga dariya ga takaici wato rayuwar nan darasi ne mai zaman kanta abin da ya sa ka dariya watarana kuka zai sanya ka, ta wani bangaren ta ji daɗi da Ammah ta fahimci halin Bilkisun an ce Bilkisun har Ammah ta kira a waya tana tambayan ko ta yi mata wani abu ne ta ga ta canza mata Ammah ta ce ba komai.
Amma tabbas Bilkisu ta sha jinin jikinta, ganin Ammah da ke ta kanta ma yanzu ta daina dole ta yarda makaman yaƙin ta.

Shamsiya ta samu canjin rayuwa ta sillar Ummu Salma, har yanzu tana aiki da su a Foundation ɗin su sannan Habib ya samu aiki a wani kamfani sarrafa takalamin fata anan garin Jimeta sun samu canjin Rayuwa. Suna nan tare da Habiba wacce ta haihu ɗiya mace har takwara aka yi ma Ummu Salma yanzu ta daina adawa itama, tunda ga shi sanadiyar Umma Salma ta samu jari tana kasuwancin online, sannan Habib ya samu rufin asiri ta yarda ta haihu da shi Shamsiya dai har an juya mata mahaifa domin ta yi rauni ta gaji da ɗaukan ciki tana ɓarin shi, Hanan tana zuwa musu hutu in dai ta je Jimeta.

Ta riga ta san cewa Papa ba babanta ba ne, ta tambayi Ammah ta faɗa mata gaskiya sannan ta tambayi Lamiɗo ya amsa mata da cewa shi ne babanta amma mahaifinta Habib ne wanda take ce ma Abba. Duk da ta ji ba daɗi amma ta gode ma Allah, tunda tana da baba guda biyu. Riƙon ta da duka rayuwarta na Hannun Lamiɗo da Ummu Salma ne, amma in ta je Habib da danginsa na iya ƙokarin su wajen kyautata mata duk da sun san ba za su iya yi kwatanta mata gatan da Hanan take da shi ba.

Sai dai su yi abin da za su yi Hanan ko kayan jikinta kaɗai ka kalla kasan yarinyar yar gata ballatana fatar jikinta, ga turanci ga labarci ga tarin ilimi, Habib ya saduda ya fahimci rayuwa ya gane kuskuren shi  ya fahimci cewa Ummu Salma na sama shi kuma yana ƙasanta.

Har yau har gobe tana ɗora girke girke a shafukanta na yanar gizo, ta samu jama'a ta samu duniya sai godiya sannan har Pandora award ta karɓa a wancan shekarar a matsayinta na jajircacciyar mace mai tallafama gajiyayyayu da marasa ƙarfi sun je tare da Mai martaba Lamiɗo da yara suka karɓo award din tare, da aka bata shi ta ba mawa domin ta ce duk abin da ta kai a yau kafaɗarshi ce ta cinciɗata.
Haka ta faÉ—a a wajen bayan yan jaridun sun tambaye ta ya take ganin nasaranta ko matakin da ta kai a yau?

Hotunansu suka dinga trending a kafafen yaÉ—a zumunta ana faÉ—in sun bala'in dacewa ga shi suna kama da juna aka fara yawo da faÉ—in yan'uwan juna ne shi ya sa suke kama da juna, ga yaran su gwanin sha'awa kamar ya'yan turawa
A garuruwa da dama sun ba da an yi rijiyoyi da bohol sadakatul jariya ga Baffa ta yi sannan suma yayyenta duk sun yi.

Sau uku ta je Saudiya Umra kuma ba ta san adadi ba.
Fulani ma a England ta haifeta wannan haihuwan ta ce a Saudiya za ta haihu. Bilkisu ma haihuwan Ali a Abuja ta haihu.

Kasashen ƙetaren da ba ta je ba kaɗan ne sai ga ta har ƙasar Jordan ta kai ma Jamila Umar takwaran Janafty ziyara sanadin marubuciyar nan ta online ta san ta. Namesake tana da mutumci da girmama baƙonta Allah ya ƙara ma rayuwa albarka.

Rayuwa ta cika da tarin ni'ima sai godiya.
Lamiɗo na gudanar da mulkinsa cikin tsanaki, talakawa da mutanen gari suna son shi Yazeed da Sagir duk sun dawo gida sun yadda makaman yaƙin su, sun zo sun haɗa kai domin cigaban Masarautarsu.
Sun yi aure sannan Lamido ya yi musu sabon naɗe naɗe, gabaɗaya manyan hakiman yan gidansu ya ba mawa, tunda kwanaki rigima ya ta so yaran ƙannen marigayi tsohon Sarki Muhammad Shitu kakansu Lamiɗo, sun ta so suma sai Sarauta ta dawo gidan su. Tuni su Lamiɗo suka haɗe kai suna fatan har nan da shekaru tamanin sune za su cigaba da mulkan kasar Daura. Burin Mai martaba kenan yau kuma burin shi ya cika.
Received at 08:05Reactions: ❤ 4, 👏 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Amir ne kawai ke Delhi yana can yana karatun likita, Amira ma tana Base Abuja, Hafsart ce ta yi aure tana auren yaron Sarkin Adamawa.

Sarakuna sun sha kawo ma Mai martaba Lamiɗo tayin auren ƴa'yan su amma ya ce baya buƙata shi mijin mata biyu ne a duniya Bilkisu da Ummu Salma, sun ishe shi rayuwar duniya har abada. Har bangaren Sarki mai murabus an sha zuwa shi kuma sai ya ce ai Lamiɗo Sarki ne ba wanda zai yi masa dole in yana ra'ayi zai yi in kuma ba ya ra'ayi babu matsawa, har a cikin ƴaƴan dangi ma ana ta kawo masa ya ce ba ya buƙata ba zai iya kara ma kansa wata hayaniyar ba, kuma daman ba shi da ra'ayin haka sannan har gobe kawo masa ake yi ba su haƙura ba.

*

Sai bayan isha'i ta gama girkin, ta so har cake ta yi to ba lokaci ne. Duk shekara tana haÉ—a masa walima daman wannan shekaran ma dalilin dawowarta daga makaranta kenan.

Girki ta yi masa kala uku, tuwon shinkafa da miyar agushi, ferfesun kayan ciki pepe chikcken sai ferfesun dankalin turawa mai hanta, ta yi zoɓo da kunun aya sai lemun kankana da fruit salat, a ko wani shekara in za su yi irin wannan walimar can gidan shi na cikin gari suke zuwa gidan da Mai martaba ya mallaka masa gidan da Mami da tsohon Sarki suka yi rayuwa gidan da aka haifi Lamiɗo.

Bayan ta gama girkin, ta bar ma Harira ta haɗa mata su a cikin kwanduna ta tura ma King ɗinta saƙon dawowarta tun ɗazu so take sai ta isa can gidan sai ta kira shi tunda yana fada.

Yaran suna bangarenta bayan sun ci abinci suka koma suna kallo a falo, ta shiga ɗaki ta yi wanka bayan ta idar da salla ta zauna ta tsantsara kwalliya, wani leshi ta saka mai kyau da tsada, daman ta yi ƙunshinta ja tun daga katsina ta yi saloon an yi mata gyaran gashi. Ga shi tana tashin ƙashim turarre daman ba ta wasa da kayan gyaran Surayya akai akai tana siyan kayanta yanzu haka ma suna can a fridge a katsina ta siya ta fara amfani da shi.
Chapter 73 · 0% Book details