← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 75

Sashe 65

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BaÉ—É—o ta samu ciki har ya fito. Tana gida tare da Ammah, da yake kasuwancinta na online ne tana gida tana cigaba da kasuwancinta.
Da babbar salla ba su zo salla ba tunda Ammah bata nan sai da ta dawo suka taho gabaÉ—aya har da Mai martaba da yaran suka yi mata sannu da zuwa Banafsha, ta yi wayau har ta fara zama tunda yanzu tana wattani na biyar cikin na shidda ne da haihuwa, Mai martaba kwana É—aya ya yi ya koma sune sai da suka yi sati Bilkisu kuma daga nan Kano ta wuce tare da su Sultan Hanan kuma an kaita gidan babanta.

Shamsiya ta faɗa ma Ummu Salma ta samu ciki wata biyu da kwanaki ta yi ɓarin shi, har tausayi take ba ma Ummu Salma, ga wahalan rayuwa tana tunanin in dai ta buɗe foundation ɗin ta, Shamsiya za ta shiga cikin waɗanda za ta fara tallafamawa, sannan ta roƙeta yan ajinsu na makaranta suna ta tambayan lambarta tana neman izinin ta tura musu? Ummu Salma kuma ta ce ta ba su ba komai ikon Allah kenan yanzu tunda ta zama matar Sarki kowa neman ta yake yi an mayar da ita group na makaranta girmamata suke yi ranki ya daɗe sama da ƙasa ba mai kiran sunanta ko kuma su ce Sarauniyar Daurama.

Ita dai sama sama, duk wanda ya kira ta za su gaisa amma tun daga kan Shamsiya ta daina aminci da yarda da ko wata ƙawa.
Received at 19:42
8 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Tana da Baɗɗo ba ta neman kowa a halin yanzu, amma in abu ya faru na buƙatar taimako tana taimakawa iya ƙarfinta ko kwanaki wata class mate ɗinsu ta samu hatsari za a yi mata aiki a kugu ana neman dubu ɗari takwas, mijin ba shi da karfi ana neman taimako ta yi ma Mai martaba mgana ya ba ta kuɗi ta tura musu dubu 1M mazan su da matansu haka suke yi mata godiya. Sannan sun ce suna so su shirya haɗuwa na mates ɗin su, ta ce su shirya ba sai sun jira ta ba, ƙarshen shekara aka ce ta ce lokacin suna Abuja bikin Saleem amma daga can za ta zo Adamawa.
Saleem zai auri Æ´ar sarkin zazzau ne kuma a garin Abuja za a yi duka bikin angon ma a can za su zauna tunda anan yake aiki.

Sagir ne ma ya dawo garin amma ya koma ya ce sai ya haÉ—o Phd É—insa Yazeed kuma yana masters ne. Mai martaba mai murabus kuma ya samu lafiya da kwanciyar hankali ya dawo yana gida yana hutawa.
Ummu Salma su ta riƙe a matsayin iyayen ɗakinta duk sati tana hanyar zuwa, da abinci domin Mai martaba mai murabus har jiran girkinta yake yi Lamiɗo ya faɗa masa abin da take so kenan harkan girke girke Mai martaba ya ce za a buɗe mata har gidan abincin in dai tana so tana ta godiya. Burinta ya kusa cika ta kai in da take so ta shahara, ta samu ƙwarewa daga mabambamta makarantu na online sun fi biyar sannan ta zo ta yi online class na mutane ɗari sannan bayan an gama ta raba musu dubu hamsin hamsin ta ce su je su ja jari ko wacce ta je ta kafa abin da ta iya.

Wannan dalilin ya sa ta yi suna sosai kaf arewa a cikin masu girke girke za ka ji ana zencen Sarauniyar Dauramas Kitchen, cikin ƙanƙanin lokacin sunanta da komai na ta ya tafi viral tuni mutane sun fara yarda matar Sarkin Daura ce wasu har sun lalubo hotunanta ana yawo da shi, yanzu social medi ba tsaro in suka taso ka gaba sai Allah.

In da ta gode ma Allah ba ta samu ciki ba ga shi har Banafsha na shirin shekara har ta fara tafiya ba in da ba ta zuwa. Shi yasa sai komai ya zo mata da sauki BaÉ—É—o ce kamar P.A É—inta Mami kuma mai ba ta shawarwari ita da Hamma Saddam kuma tana jin daÉ—in haka sosai.
Har sun fara maganar foundation da Hamma Abdulrahaman ya ce zai haÉ—a ta da wata Barrister Salamatu Doma, a nan Abuja take tana aiki da suprime court Abuja, itama suna da wata foundation da take jagoranta za ta taimaka mata sosai. Yanzu sun ajiye mganar in suka je Abuja bikin Saleem za ta je har gida ta samu Barrister Salamatu Doman su yi magana.
A karshen watan november BaÉ—É—o ta haifi É—a Namiji ya ci sunan Baffa, suna kiran shi Junior.

Ummu Salma ta zo suna, Bilkisu lokacin ba ta nan ta je Canada hallatar wani Seminar na su na likitoci. Da za ta koma da Islam ta koma ta gama jarabawar fita babban sakandiri kafin sabuwar shekara za ta fara jami'ar a Kasu dake Kaduna in da Mami ke aiki.

Tana komawa Daura ta fara zazzabin dare sai amai ana duba ta sai ga ciki har ya yi wattani uku ma ba ta san da shi ba. Duk da tana jin canje-canje a jikinta.
Ta ji daɗi amma ba ta ji ba saboda cikin zai yi mata cikas da shagalin biki, sannan ga shi Mai martaba ya yi mata alƙawarin zuwa Saudiya, yanzu kuma ciki na ɓulla ya ce sai ta haihu yaro ya yi ƙwari, sai da ta yi kuka ta so ta je Saudiya ta yi ta ibadu tana roƙa ma Baffa gafara a harami.

Allah ya sa ma cikin bai ba ta wahala kamar na Banafsha ba. Shi ya sa har ta samu daman shiga ciki ana ta shirin biki da ita.
Gimbiya Shahida da ya'yanta suna girmamata shi yasa itama ba ta sanya a duk abin da ya shafe su. Islam sun haɗe da Amira da su Hafsat, da yaran Sakeena, Amiran ma wannan shekaran za ta yi candy Hajiya Zaliha suke da biki a zaria ƙanwar mijinta ne Saleem zai aura.

Tun a satin biki suka tafi Abuja, akwai gidan Mai martaba acan suka sauka ana ta shirin biki.
Ango kuma yana Daura sai sun É—aura aure a zaria za a taho da Amarya Abuja a yi dinner. Saddam na cikin abokan ango shi da Hamma Abdulrahim sun saje da yaran manya nan ma tare da Adda Nauwara ake yin komai tunda suna gari.
Received at 19:42Reactions: ❤ 7, 👎 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Kowa ya ga Ummu Salma ko ba ta faÉ—a ba sai a ce tana da ciki, ta yi kiba kamar ba ita ba. Gimbiya Shahida na Daura nan za ta yi taron ta sai ranar Dinner za ta taho.
Ammah da Ummin ikki Daura suka fara sauka.
Daga can ne ranar É—aurin aure suka taho Abuja a jirgi suna isowa ba daÉ—ewa ango da tawagarsa tare da amarya da danginta suka sauka.

An sauketa a ƙayattacen gidanta mai kama da aljannar duniya A daran aka yi wata lafiyayyiyar Dinner a ɗaya daga cikin manyan hall na garin Abuja, an barar da dukiya kamar ba san zafinta ba an ƙure adaka ankon leshi ne amma kowa ya saka kalan na shi Ummu Salma ta yi makeup, duk da ba ta ji daɗi ba Baɗɗo ba ta zo ba saboda jego, Hamma Abdulrahim ƙiri kiri ya ce ba za ta zo ba ga shi ta saka rai.

Bilkisu ma ta zo, yaran ma duk tare da su suka zo suma sun kure adaka, Hanan da Beena sun girma in ka gansu kamar wasu yan biyu, yanzu Mahma suke kiran Ummu Salma tunda suka ji Hanan na faÉ—a Bilkisu kuma Momi, LamiÉ—o kuma Papa, Sultan an girma shekaransa sha biyu yanzu amma yana da girman jiki da tsawo kamar É—an shekara sha biyar.
Mawaƙa sun zo sun baje kolinsu sun kwashi kuɗi.
Anan ne Ummu Salma ta haÉ—u da Hajiya Hauwa Inuwa Aminu(Anty Hairi) daga haÉ—uwarsu suka gaisawa shikenan suka yi ta hira da Ummu Salma, Anty Hairi sune tawagan amarya daga masarautar Zazzau, sai ga shi har suna sharing contanct. Anty Hairi akwai kirki sosai mace ce mai karamci Allah ya kara wadata ya kuma raya mata zuru'a Amin.

Ummu Salma ta tura ma LamiÉ—o hoton ta ita da yaran da ta É—auke su, sai dare ya duba ya tura mata emojin harara. Cewa ya yi sun tafi sun bar shi, ta ce ya zo shima ya ce in ya tafi wa zai bar ma Daura, ta yi ta masa dariya.
Amma ya ce ta yi kyau sosai ya yi kewarta. Ummu Salma ma har videon Bilkisu ta ɗauka a wajen ta tura masa, ita ba ta da wannan Ummu Salma ce komai da ruwan ka, kuma a hakan Lamiɗo ke son kayansa ba Bilkisu kaɗai ba har video ta dinga masa tana tura masa wai kar ya ji kewa shi bai zo ba, gwara ya ji kamar yana wajen shi dai ta saka shi mirmishi kamar wani yaro ƙarami.
Shi dai na shi karɓo aure ne kuma sun je Zaria sun karɓo aure sun dawo Daura.

A garin Abuja suka ci bikinsu suka suÉ—e, daman ita Ummu Salma Jimeta za su wuce tare da su Ammah, amma kafin tafiyarsu sai da ta je ta gana da Barrister Salamatu Doma.
Hamma Abdulrrahaman ya tura mata lambarta ta kira ta, adireshinta ta tura mata direba ya kaita sai da suka haɗu a a fili sannan ta ga kirkinta da Hamma Abdulrrahaman ke faɗa, sum yi batutuwa sosai ta ba ta shawarwarin yadda za ta tafiyar da ƙudirinta, kuma ta ji daɗin magana da ita sun rabu da cewa za su dinga tattaunawa ta waya in sha Allahu.

Sun bar Abuja 28 ga wata ne, tunda bikin 25 ne aka yi, ta je Jimeta saboda talatin ga wata za su yi class reunion ɗin su kuma yadda suke kiran ta ana buƙatarta a wajen da ta faɗa ma Mai martaba ya ce ta je ba matsala dalilin wucewarta Adamawa kenan amma Bilkisu Daura ta koma, ita kuma Ummu Salma ta taho da yaran Adamawa tare da Harira yar amanarta da duk in da za ta je tana tare da ita Islam na Abuja tare da su Hafsat Daura za su koma ta ce ba za ta je Jimeta ba.
Chapter 65 · 0% Book details