Sashe 68
Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummu Salma ta yi kasaƙe, tana jin Habib ya amshi wayar ya yi sallama da muryansa, wacce ba za ta bace mata ba muryan da a baya ta kasance lu'u lu'u a gare ta amma a yanzu ba muryan da tsana sama da muryansa.
Ta ji ya yi sallama ya ƙara yi ta yi shuru ta kasa amsawa daga ƙarshe ma sai ta kashe wayarta. Tana gani Shamsiyar na sake kiran ta ba ta ɗauka ba.
Received at 08:04
12 people reacted with â¤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ba ta fatan wata mu'amala ta sake haɗa ta da Habib har abada Shamsiya ma kawai saboda Hanan ne sannan tausayinta take ji amma ko ita ba ta son ta shigo jikinta har abada ƙawancen dake tsakaninsu ya ƙare tun a shekarun baya.
Sako ta tura ma Shamsiyar domin ba ta so nan gaba ta sake yi mata wannan gangancin.
"In kina so na cigaba da amsa wayarki ki nisanta ni da mijin ki, ba ni da wata alaƙa da shi, laifi ne ya roke ni tuntuni na ce na yafe ba bukatar wani abu kuma. Don Allah mu girmama junan mu ko saboda Hanan."
"In sha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba. Ki yi haƙuri."
Shamsiya ta turo mata reply ta karanta ba ta bi ta kanta ba. Habib yana cikin wani shudaɗɗen babi ne na rayuwarta ya shuɗe har abada yanzu Lamiɗo ne a rayuwarta saboda haka ba ta buƙatar tuna rayuwarta ta baya Hanan ce tana zuwa wajen su amma har abadan ba za ta ba shi ɗiyarta ba kamar yadda ya ce ya bar mata, to haka ne Hanan ɗiyarta ce har gaban abada sai dai ya dinga samunta a matsayin aro.
Habib daman ya san Ummu Salma ba za ta yi magana da shi ba Shamsiya ce ta matsa masa saƙon ma na Ummu Salman suna tare ya shigo shi yasa ya gani.
"Ka yi haƙuri."
Shamsiya ta faÉ—a tana kallon shi, ya girgiza kai kawai yana É—an mirmishi.
"Ba komai ni daman ban matsa ba, mai muhimmamcin yafiyar ne kuma tunda ta yafe shike nan."
Bai sake magana ba ya tashi ya fita ta bi shi da kallon tausayi tana hawaye.
Ko bai fada ba ta san yana son Ummu Salma har yanzu, sun sha suna mu'amalan aure ta ji yana kiran sunan Ummu Salma ba ta taɓa nuna masa ba, ita kaɗai take shan kukanta, koma mai ya faru ita ce sila, ita ce ta yi shuru amma Habiba ƙara ta kawo shi gidan su wai yana tare da ita amma yana tunanin matar auren da har ya mutu ba zai sake samun zama da ita ba, ta tona masa sirrin shi a idanuwan kowa har sakinta ya so yi Shamsiya ce ta hana shi ta danne shi. Habiba kaɗai aka bar Habib da jarabawarta mai zafi ce a gare shi, bayan wasu matsalolin rayuwa musamman talauci da halin babun da suke ciki, aikin koyarwa ne sai karshen wata karshen watan ma kafin nan duk an ci ba shi ga albashin babu yawa.
Godiyarsa Allah Shamsiya tana taimaka masa shi yasa in ya kalleta sai ya gode ma Allah da ya sa itama bai rasa ta ba da yanzu rayuwarsa na cikin uku, yana karɓan sakamakon abin da ya aikata daki daki, ga takardun amma aiki ya gagara har ya gaji da tura CV Alhaji Sherif ma duk ya karɓa ya tuttura amma ba a dace ba a hakan ma godiya yake yi ma Allah da ya barsa da lafiyarsa. Lafiya jari ce in da ya rasa lafiya da komai ya kwaɓe masa. Shi ya yakice Ummu Salma a cikin rayuwarsa yana tunanin ita ce za ta shiga garari sai ga shi, ita ce ke cikin ni'ima shi kuma rayuwarsa na cikin garari, soyayyarta dake zuciyarsa ma kaɗai ishara ce ga masu hallayar irin na shi.
*
Ummu Salma da yara sun koma Daura bayan watan January ya raba tsakiya. Ko da ta koma ba ta samu Islam ba ta koma Kaduna za ta fara registration É—in fara jami'ar Kaduna.
Ranar da suka dawo ko bangaren Mai martaba ba ta je ba, tana idar da sallar isha'i barci ya rinjayeta.
Washegari sai ta je can bangaren tun mangariba saboda cutar barcin dake damunta yanzu ko ita ba ta iya yi ma kanta wani abu, girkin ma Harira ce ta kama mata suka yi.
Ko da ya shigo bangaren daga Fada har ta kwanta ta fara barci amma barcin bai yi nisa ba, ta kunna littafin Rufaffen Duma na marubuciya Ummulkhairi Sani Panisau a tashar tsakar gida tana sauraro, ta fara ji amma barci ya tafi da ita, wato kana girma rayuwarka na canzawa yanzu ko da kuÉ—i aka ce ta tsaya ta yi kallo ba za ta yi ba, karatun ma sai dai ta ji Audio.
Ta san dai sun yi magana da Hamma amma ba za ta tuna me ta ce masa ba barci ya fizgeta sai da ya dawo daga masallaci ne sallar asuba tana zaune saman darduma tana azkar lokacin da ya shigo, ya cire babban rigan shi da wani farin harami sannan ya hau saman gado ya É—au wayarsa yana dubawa.
Received at 08:04
14 people reacted with â¤

Ta shafa addu'arta a duka jikinta sannan ta miƙe ta yaye hijabin jikinta, rigar jikinta fara ce mai santsi ta ɗora zani a saman rigan da za ta yi salla duka ta cire ta watsa su saman kujeran dake bedroom din sai jin ta kawai ya yi a saman jikinsa.
"Good morning my king."
Ya kalleta amma kuma bai bar kallon wayarsa ba.
"Kin tashi lafiya?
"Sarauniyar barci."
Ya gama faÉ—a yana É—an jan karan hancinta.
Mirmishi ta yi kafin ta ce" Babynmu ne ke saka ni yawan barci da kasala."
Ta gama faɗa tana jan hannunsa zuwa ƙasan maran ta dole ya ajiye wayar ya tallabeta, shafa cikin yake yi ita kuma tana shafa hannunsa, cikin na ta har ya ɗan turo.
"Shi ne ya sa shekaranjiya aka ƙyale ni ko?
"Ban ma san na yi barci ba."
Ta gama faÉ—a tana yar dariya, ta cigaba da ba shi labarin barcin da ta dinga yi a Jimeta har Ammah na faÉ—in kamar wata kasa.
"Ba fa na gajiya ko yini zan yi na kwana ina barci fa."
"I see."
"Jiya ina mgana shuru, kina ta dai kiran sunana na gaji da amawa na ƙyale ki."
Ta ƙyalƙyace da dariya tana shafa ƙirjinsa.
"Ni dai na san na ji muryanka amma ban san abin da ya faru ba."
"Kina magagin barci."
"Ga waya a kunne sai da na kashe"
Ya ba ta amsa yana shafa gashin kanta zuwa wuyanta ƙamƙame shi ta yi
"I miss you."
Ya yi shuru bai yi magana ba amma ya É—ora kan shi a saman kanta, ita kuma tana kwance a saman jikinsa ya yin da shi yake kwance a saman gado.
"Ka ji."
"Na ce na yi kewar ka? Ko ba ka yi kewata ba ne?
"Na yi"
Ya faÉ—a muryansa a dishe kamar mai jin barci ta É—ago tana kallon shi akwai haske a É—akin suna masu kallon juna cikin idanuwansu.
"Ba ka yi ba."
"Who tell you! I miss you sosaai."
Ya faɗa yana sumbatar bakinta, ta yi masa mirmishi da fari, kafin ta koma ta kwanta a saman ƙirjinsa.
"Ina son Hamma na "
"I know."
"Nima kin san ina son ki ko?
Ta gyaÉ—a masa kai, sai ya gyara mata kwanciya a saman jikinsa.
Yana faÉ—in su yi barci, ta ce to wayarta dake gefe ta zura hannu ta jawo ta shafa haske ya kawo hoton hannunsu ne tare da Banafsha wanda suka É—auka a Jimeta tun tana jaririya shi ne a fuskar a wayar in ta buÉ—e wayar hoton su ne ita da Hamma LamiÉ—o ranar graduation É—in su na catering school É—in da ta yi a Lagos tana son hoton nan sosai.
Shi ya lumshe idanuwa kamar mai barci ita kuma tana duba wayarta, saƙonnni take dubawa sai ta ga Mami ta turo mata hoto tana shiga ta ga hoton Banafsha ne sun je park tare da Mami da Faruk, sai ta ɗago tana kallon shi lokaci ɗaya tana kara masawayar.
"Banafsha an zama yan kaduna."
Ya yi shuru bai yi mgana ba ya buÉ—e idanuwansa ya kalla ya koma sake ya lumshe idanuwansa
"Hamma "
"Uhm"
"Ko za mu bar ma Mami Banafsha ne?
Ya yi shuru kamar bai ji abin da ta ce ba.
"Ba ka ce komai ba?
Sai da ya É—an muskuta sannan ya ce" Me kike so na ce? A' a in kina son ki ba ta ita go ahead daman ke ma a wajenta na gan ki."
Kai tsaye ya yi maganarsa amma sai da ta yi dariya
"Aa a É—akin Ammah ka fara gani na dai."
"Ina zuwa Kaduna saboda ina son Mami sosai."
"To masu Mami ni ma dai ina da tawa Ammah."
Ta fara dariya tana faÉ—in ita ba ta ce ba shi da shi ba
"Kafin ki ce ne na faÉ—a miki."
Ta mike zaune daga kan jikinsa. Ta zauna a gefen shi ta yi kwanciyar ruf da ciki da sauri ya ce" Na hana ki ko? Ba ki ga kina da lalura ba ne?
Sai ta yi saurin mirginawa suna fuskantar juna.
"Na bari."
"Better."
Ya gama faÉ—a idanuwansa na sake lumshewa.
"Ya aiki? Akwai wahala ko Mulki?
Ta gama faÉ—a tana shafa sajen fuskarsa.
"Na fara sabawa, shekara É—aya kenan ina matsayin Sarkin Daura."
"Haka ne Allah ya kara tsare mana kai ranka ya daÉ—e."
Ya amsa da Amin a fatar bakinsa ta fara masa tambayiyo daman aikinta kenan yana amsa mata, yau ma masarautar katsina zai je, akwai taron sarakuna na yankin katsina da zamfara da za a yi.
Ya gaji ya ce mata su kwanta ta kara shigewa jikinsa har ya fara barci ta tashe shi da kiran sunan shi.
"Hamma."
"Ummu Salama."
Ya kirata cikin ƙosawa, ya gaji yana so ya kwanta ba ya son hiran nan a yanzu.
"Na ce miki mu kwanta ko? Bana son magana."