← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 75

Sashe 7

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummu Salma kuma da su BaÉ—É—o suna É—akin Baffa tare da su Adda Suwaiba.
Sauran mutanen Mubi kuma suna tsakar gida wasu daga cikin iyalan su Umma Balki da sai bayan an yi jana'iza suka iso suna cikin É—akunan barcin Ammah da na Ummu Salma, wasu kuma suna cikin É—akin tsakar gida.

Ana zazzaune ana ta amsa gaisuwa an yi jugum jugum, kowa ka gani fuska a koÉ—e gwanin ban tsausayi.

Baɗɗo na gefen Umma Salma ba ta barta ba, domin Gimbiya  Shahida ta ce a zauna tare da ita a kula da yanayinta.

Tun bayan da aka fita da gawan Baffa Ummu Salma ta ji kanta ya yi wani irin sarawa, ta ji kamar an ɗora mata wani ƙaton dutse a saman kanta sara mata yake yi irin sarawar da ba ta taba jin irin shi ba. Ita dai tana biye da duk wanda ya riketa ne duk in da aka bi da ita can take zuwa.

Tana zaune ne hawayenta sun ki tsayawa. Wani irin abu ne mai zafi da maƙaƙi ya tokare mata a zuciyarta da kirjinta ba ta taɓa jin abu mai zafi irin shi ba ko lokacin da Habib ya saketa ba ta ji irin haka ba wannan abun ya ninka abin da ta ji a wancan lokacin sau dubu

Tantama take yi tana shakkun cewa wai yau ba Baffa? Jiya fa sun yi magana da shi ashe ashe Allah ya yanke ganawarsu gani take yi kamar a mafarki gani take yi kamar a ce ta farka ta ga komai bai faru ba. Ta ga lokacin da aka tafi da gawan Baffa daga lokacin ta ji komai ya tsaya mata duniyar ta tsaya mata cak ba ta jin daɗin komai bakinta ya yi wani takaf ɗaci daci ma take ji jikinta ya yi mata nauyi, cikin jikinta ya dunƙule a waje ɗaya maranta ya ɗaure haƙoranta na karo da junansu tana jin kamar jikinta na kamewa a waje ɗaya Baffa zai dawo wasa ne bai mutu ba haka take gani amma in aka shigo yi musu gaisuwa ta ji ana cewa Allah ya jikansa sai ta ji kukanta ya ƙaru da gasken kenan babu Baffa yanzu shike nan ya tafi ya bar su.

Ta jima tana jin labarin irin raɗaɗin rashin wani na kusa dakai, ita da ta tashi uba ta rasa a lokacin da ba ta taɓa kawo masa mutuwa ba ko a mafarki ko a hasashe ta yi hasahen rasa Ammah ko Baffa sai zuciyarta ta ƙuntata ta ji labarin ɗacin mutuwa ita sai yau ta ɗanɗani wannan ɗacin ta sha jin waɗanda aka yi ma rashin irin ta uwa ko uba suna faɗin har abada ba za su taɓ mantawa ba yau itama wannan rashin ya risketa tana jin itama har ta koma ga Allah ba za ta daina kuka ba har abada ba za ta ƙara dariya ko wani farinciki ba tana ganin farincikinta ya ƙare tunda ta rasa Baffa.

Baƙi suna ta zuwa maza da mata, wasu daga can Mubi ne wasu iyalan su Baffa Umari ne da su Umma Balki mata da maza dake can wasu garuruwan suna aiki sai gida ya sake kacamewa da koke koke ba yadda za a yi domin Baffa ya rasu ba kuma zai taɓa dawowa ba.

Har bayan azahar ba wanda ya sha ko ruwa a cikin waɗanda mutuwa ta shafa sai dai wasu na can gefen da ba su damu da mutuwar ba, domin sun ma kafa dandalin hira ne ba ko nuna jimami ga waɗanda aka yi ma wannan rashib, wasu ma sun fara ƙorafin su yunwa suke ji wasu ma wayarsu suke dannawa. Shi gidan mutuwa kaɗan ne daga ciki ke cikin jimami da ka mutu an kai ka an binneka shike nan taka ta ƙare sai iyalanka ne za su jima suna kukan rashinka.

Sai da duk aka yi salla sannan Ammah ta yi magana da Adda Nauwara tunda ita ce Babba ta ce su dafa abinci ko saboda yara.
Su kansu sun san an yi mutuwa sun natsu a waje É—aya.

Harira na tare da su Sabuwa yaran kuma duk suna tare da su.
Sultan da shi aka je makabarta tare da sauran yaran su Hamma Jibo suna can haraba tare da iyayensu wajen zaman gaisuwa.
Received at 09:59Reactions: ❤ 13, 😭 4
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Adda Nauwara ta fito ta yi ma Adda Suwaiba magana suka tattara kansu surukan gidan suka yi maganar ɗora abinci , duk da ma daga maƙota duk an fara kawo abincin wasu har sun fara wawaso, wato yanzu gidan mutuwa ya koma gidan da ake ci a sha, barin ma in a ka ga gidan akwai maiƙo.

Kayan abinci akwai su danƙam a store ɗin kitchen cefane ma akwai domin kwana uku da ya wuce Hamma Abdulrraham ya yi cefane.
Suka É—ibo kayan miya suka gyara babban tukunyar Ammah mai lamba talatin suka É—ora a wani babban murhun gawayinta a tsakar gida gawayin ma akwai shi tunda lokacin bayan lokacin Ammah na amfani da shi.
Wajen ukun rana suka gama abincin aka zuzzuba anan cikin gida sannan aka zuba aka fita da shi waje daman kuma an kawo katan katan na ruwan gora da lemu sama da katan hamsin a cikin gida bayan wanda aka sauke a waje an samu abin da ake so tuni gidan mutuwa ya koma gida cin abinci da kuma hira , ana ci ana hira ana korawa da lemun gora da ruwa. Yara dai duk an saka musu sun ci tunda su yara ne ba ma su san abin da ke faruwa ba.

WaÉ—anda mutuwar ta shafa ko ruwa sun kasa kaiwa baki. Ko su Fulani ma sun kasa cin abinci ruwa kawai suka sha.
Ammah ma ba ta ci ba, ba ma wanda ya yi mata magana ganin yanayinta Ummu Salma ce BaÉ—É—o ta matsa mata ta ci abinci sai dai kawai ta kalleta hawaye na kwaranyo mata.

"Ba zan iya cin abinci ba BaÉ—É—o. Abinci ba zai wuce ba, bayan na san Baffa na cab cikin kabarinsa a yau ba zan iya ba."

Ta sake fashewa da kuka, mutanen dake ɗakin suna ta ba ta baki amma ta kasa ci, wai ta ci saboda cikin jikinta ta ce ba za ta iya ba su ƙyaleta.
Kukanta ya dawo saboda tana yi tana shessheƙa.

Bayan la'asar Mai martaba za su koma tare da Fulani da Gimbiya Amratu za a bar Gimbiya Shahida da Saleem sai an yi addu'an uku za su koma Daura.
Har cikin gida Mai martaba ya shigo sake yi ma Ammah gaisuwa da yin sallama.

Hamma Jibo ne ya yi masa jagora. Mata suka dare sannan Mai martaba ya shigo tare da Waziri da shamaki dogarai suna dake a bakin ƙofar ɗakin Ammah ya shiga har ciki ya zauna a saman kujera.

Ammah na gefe kanta na kasa su Umma Balki sun bar falon sai Mami ne kawai tare da su Gimbiya Shahida sai Ummin ikki da su Bilkisu

Ya yi ma Ammah gaisuwa tare da ba ta haƙurin wannan rashin da suka yi gabaɗayansu tare da tausasan kalaman hakuri da cin wannan jarabawan

"Allah ya jiƙan shi, Allah ya ba ku haƙurin rashi."

"Amin ranka ya daÉ—e mun gode Ubangiji ya mayar daku gida lafiya."

"Ammah Mai martaba ya ba da kuÉ—i masu yawa ya ce a siya kayan abinci da duk abin da za a nema a wajen zaman makokin nan"

Hamma Jibo ya faÉ—a yana zaune daga gefen Ammah.

"Allah ya ba da lada. Mun gode ranka ya daÉ—e."

Bai amsa yana da cikin rawaninsa idanuwansa da wani farin gilashi ya kalli Mami da ta jingina da jikin kujera a rana É—aya kawai ta wani faÉ—e kamar wacce wani cuta ya kamata. Kamar ma ba ta san abin da ke faruwa a falon ba hawayenta ne kawai ke zuba da motsin carbin hannunta.

"Batula ya haƙurin mu?

Mai martaba ya tambayeta yana mai kallonta ta cikin rawaninsa.
Tana ji ashe ba ta É—ago ba amma bakinta ya yi motsi alamun ta amsa.

"Allah ya jiƙan shi, Allah ya ba da haƙurin rashi."

Ta amsa da Amin tana mai rufe bakinta da tafin hannunta guda ɗaya wani kuka ne ke ƙwace mata kawai sai ta kifa kanta a jikin kujera tana faman rerewa kukan da ya kashe ma duk wanda ke ɗakin jiki barin ma Mai martaba da ba ya son jin kukan Batula kukanta na tuna masa da shekaru talatin baya
Ɗakin Ammah kawai suka shiga daganan suka fita ya ce sai ranar addu'an bakwai in ya samu dawowa in kuma bai dawo ba zai turo wakili shima nan da sati uku zai tafi ganin likita a ƙasar London.

Tawagan wakilan Gwmnan Jahar Adamawa ne suka kwashe su zuwa fadar gwammati daga can za su wuce filin jirgi su koma Daura.

Da gaske dai Baffa ya rasu, tun da ga shi har an yini an kwana Baffa ya yi kwanan kabari. Barci ko ɓarawo bai saci Ummu Salma ba haka Mami ma, kuka kawai take yi ba saurarawa.
Ammah kuma kwana ta yi salla domon nema ma Baffa rahama da gafara a wajen ubangijinsa.
Received at 09:59Reactions: ❤ 13, 😭 4
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Duk anan suka kwana har Bilkisu mazan kuma a can bangaren su Saddam da safen ne Hafiz da matarshi Salima suka iso ya ce a status ɗin Hamma Kabiru ya gani ashe ba rabon ganawarsu da Baffa a ranar ma mota biyu daga Mubi sun sake zuwa amma ba su kwana ba kama daga yan'uwan matan su Hamma Abdulrhaman tare da abokan ayyukansu duk sun taho gaisuwa gida ya sake cika danƙam
Sannan abokan aikin su Hamma Jibo daga Abuja, Gombe Taraba duk sun taho gaisuwa. Kuma suna shigo da su cikin gida domin su yi ma su Ammah gaisuwa.
Chapter 7 · 0% Book details