← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 75

Sashe 36

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba komai duk abin da ka ga tana ci shi ne zaman lafiyanta tunda shi take so. Ba kuma abin da zai sameta da yardan Allah."

Ummin ikki ta amsa mishi.
Su Ammah suka amsa da in sha Allahu.

"Haihuwar ce nake fatan Allah ya ba ta da sauƙi. Allah ya sa wannan karon ta haihu da kanta ba sai an farka ta ba."

Umma A'i ta faÉ—a Ummin ikki na amsawa da Allah ya sa.

"Ai ba anan ƙasar za ta haihu ba. In sha Allahu a Egpyt za ta haihu kusa da kwarrarun likotoci."

tana cin kanzon ta sai da ta kalle shi ya gyaÉ—a mata kai daman a wancan cikin a can ya tsara za ta haihu shi da Mami sai Allah ya yi ikon sa kafin ma cikin ya isa haihuwa.

Umma A'i ta ce hakan ma ya yi, tunda dai tana da matsaloli a wajen haihuwar gwara aje kusa da ƙwarrarun.
Received at 17:28Reactions: ❤ 12, 👏 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sun bar wannan hiran sun koma hiran Mai martaba Ammah na tambayan yanayin jikinsa.

"Da sauki Ammah har yanzu dai yana kan shan magani."

A tare suka yi fatan Allah ya ƙara lafiya. Ya ce yana so zai je ko bai kwana ba ya dawo a ranar nan da kwana biyu shi da Umma Salama za su koma Lagos.
Ummu Salma ta yi zaraf ta ce za ta je Daura.
Ya ce ba za ta je ba saboda yanayinta ta bari da salla, sannan akwai wata tafiyar a gaban su tunda kuma ya ce ba za ta je ba da gaske yake yi.

A gidan suka yini har dare barin ma da su Saddam suka dawo ga su Hamma Abdullahi kusan duk dare suna gidan saboda É—ebe ma Ammah kewa sai wajen goma na dare suka koma gida Harira ta sha zama ita kaÉ—ai.

Washegari a gida suka yini ba su fita ko'ina ba
BaÉ—É—o ce ta zo ta kawo mata garin goriba da aya daman ita ta ce ta siyo mata lokacin LamiÉ—o na barci ba ta wani daÉ—e ba ta tafi ba zama yanzu tunda ta zama yar kasuwa.

Ranar Laraba jirgin safe LamiÉ—o ya bi zuwa Katsina ya kwana É—aya ya dawo alhamis da safe.
Ya ce kuma a gobe za su wuce Ummu Salma ta ɗauki ƙalilan abin da za ta buƙata.
Sai gashi tana faÉ—a masa za ta yi guzirin kasa a jirgi kallonta kawai yake yi ya ma kasa magana.

Tunda ya dawo daga Daura ta ganshi sai a hankali ya shge É—aki ya fi awa huÉ—u ta É—auka ma barci yake yi sai da shiga ta same shi idanuwansa biyu.
Gefensa ta zauna tana kiran sunan shi ya É—an muskuta yana kwance ne daga shi sai bakin dogon wando jikinsa ba riga.

"Meke damun ka?
Tunda ka dawo ba ka da walwala! Ko wani abun ne ya faru? Ki jikin Mai martaban ne?

Duk a jere ta yi masa tambayoyin tambayar ta ƙarshe na da alaƙa da damuwarsa amma ba zai iya faɗa mata ba.
Kawai sai ya jawo ta jikinsa ya ce ta zo su kwanta.
Lokacin wajen biyu ne na rana.

Ba ta yi musu ba ta lafe a jikinsa yana so hankalin shi ya É—auke daga tunanin tattaunawar da suka yi da Mai martaba a daran jiya ne.

Shi yasa ya ce ta yi masa hira ko wani iri ne, sai ta fara ba shi labarin littafin da ta fara saurara daga tashar tsakar gida na ÆŠingishin kwaÉ—o.

"Yanzu kuma an daina kallo an koma jin littafin?

"Kallon ne duk baya mini daÉ—i yanzu."

Mirmishi kawai ya yi, ya tuna a baya yadda har wani shauƙi Umma Salma ke jin in tana kallo ita ta koya masa anma sai yana tare da ita in ba sa tare baya ma tunawa da wani kallo ba shi ke gaban shi ba.

Labarin take ba shi, amma ba ita yake saurarawa ba.
Ya tafi tunani ne, tunanin maganganun Mai martaba kamar na wasiyayya kamar na jaddadawa kamar na umarni.

Sun daÉ—e ba su yi wannan maganar ba sai jiya ya É—ago masa.

"Muhammadu ina maganarnmu ta kwana? Da gaske nake yi ina so ka gaji wannan karagar, a yan'uwana babu namiji duka mata ne kuma mace ba ta mulki, ɗan mace ba zai yi mulki ba in dai akwai ɗan namiji. A cikin ya'yana kai ne Babba kuma kai ne nake ganin yafi dacewa da ya gaje ni. Bana so sarautar gidan Shitu ta suɓuce mana, ka je ka sake yin tunani wannan shine magana ta ƙarshe. Zan yanke hukunci kuma duk abin da na yanke za ka bi umarnina ne."

Kalaman Mai martaba suna nufin ya ajiye mafarkinsa da burinsa ya zo ya yi sarauta.
Ba zai iya ba, kuma ba zai iya faÉ—a ma Mai martaba ba zai iya ba É—in amma ya shiga damuwa bai san dalili ba yana ji kamar Mai martaba zai iya aiwatar da abin da ya faÉ—a. Maganar ya ce daga shi ne sai Ubangijinsu ko Fulani ba ta san sun tattauna wannan maganar ba ya je ya yi tunanin in ya sake kiran shi Umarni kawai zai bi.

Addu'a yake yi Allah ya ƙara ma mai Martaba lafiya ya yi tsawon ran da zai yi ta mulkin jama'ar garin Daura.

Washegari Jumma'a da za su tafi, Ummu Salma sun je asibiti tare da LamiÉ—o ta yi ma likitan bayanin za ta koma Lagos can za ta cigaba da ganin likita ya yi mata rubutu a wata takarda ya ce duk asibitin da ta za ta koma tana ba su wannan takardan za su san matsalolinta su dora daga in da suka tsaya.

Ba su ɗauki kaya da yawa ba akwati ɗaya ne sai ƙaramar jaka na Harira
Ƙaasarta kuwa dakyar Lamiɗo ya lallaɓata bata ɗauka ba ya ce wa zai barta ta shiga jirgi da ƙasa ta bari zai sa ko Hamma Abdullahi ya sako ƙasar a mota a kawo mata har Lagos sannan ta haƙura.
Received at 17:29Reactions: ❤ 17, 🔥 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Shima dai ya faÉ—a mata ne amma wayau kawai ya yi mata. Sun koma gidan sun yi musu sallama kanzonta an dake mata shi sai ta É—auka ta saka cikin kaya
Shi ya tuƙa su zuwa filin jirgi a can ya bar motar Hamma Abdullahi zai je ya ɗauka daga baya.
Jirgin karshe 12:30pm suka bi zuwa Lagos.

*

Sun sauka a Lagos bayan azahar ƙarfe ɗaya da wasu mintina. James ne ya zo ya ɗauke su daga filin jirgi zuwa gida.

Sai ga su a sabon gida. Daman ai sun zo gidn tun lokacin da za su duba gabaÉ—ayansu. Da aka saka funitures ne lokacin sun taho Adamawa
James da Baban adila suna gaisheta cikin girmamawa suma sun ji daÉ—in ganin ta.

Yara suna gida ba makaranta sun shigowa falon suna kallo ai suna ganinsu yaran suka rumtuma wajen Umma Salma sai da LamiÉ—o ya janye Sultan yana faÉ—in su yi mata a hankali ba ta da lafiya. Hanan ta san uwarta sai murnan ganinta take yi tana kiran sunanta Mahma.

Hayaniyar yaran ya fito da su Sabuwa gabaÉ—ayan su.
Suka duƙa suna yi ma Umma Salama sannu da zuwa ita da Lamiɗo.
Bilkisu bata nan tana wajen aikinta.

"Welcome back second Madam."

In ji Debora, haka Anitha ma ta yi ma sannu da zuwa
Harira suka rumgume ita da Hidaya daman ta su ta fi zuwa É—aya.

LamiÉ—o bangarenshi ya wuce ya ce Sabuwa ta raka Umma Salma bangarenta.
Sai kallo gidan take yi, wato funitures É—in da aka saka masu kyau yan waje duk haÉ—uwar wancan gidan da ta fara ruÉ—ewa ranar da ta gan shi sai da wannan ya fi mata haÉ—uwa.

Key É—in bangarenta na jikin kofar korodin É—in da zai kai ta cikin bangarenta buÉ—ewa kawai suka yi suka shiga. Falon ta ya yi kyau kalan blue ne kujerun da fentin ma irin na zamani ne irin waÉ—anda take gani a fina finan turawa. Falon ba shi da wani girma amma ya tsaru ga faskekiyar plasma ta shiga duba bedroom É—in su masha Allahu babu abin da babu, kitchen É—in ya fi birgeta. Har da store ga kayan abinci sai ka ga dama za ka fita can main falo.

Ta zaɓi ɗakinta ta ce Harira ma ta zaɓi ɗaya ta shiga.
Na kusa da ita ta shiga ta ajiye kayanta.
Salla suka yi sannan aka gabatar musu da abinci Ummu Salma ta ce ba ta ci, kanzonta da ta yi guziri ta ce da yamma za ta jiƙa ta ci.

Barci Umma Salma ta kwanta sai la'asar ta tashi shima É—in Hamma LamiÉ—o ne ya shigo har É—akin sai ji ta yi ana yi mata tafiyar tsutsa a kafarta tana buÉ—e idanuwa ta gan shi da shirin shi na tafiya masallaci ya ce ta tashi ta yi salla.

Bayan ya fita ta miƙe ta faɗa tiolet Allah ya sa bangarenta ba a taɓa amfani da shi ba. Ba ƙamshin komai sai na sabin kaya. Bayan ta idar da salla ta dauko kanzonta ta fito, ta jira Harira a falo ta ba ta, ta ce ta jiƙa mata da maggi kawai da gishiri.
Shi ta samu ta saka ma cikinta tana cikin cin ne ma sai ga su Sultan sun shigo

Beena da Hanan suka saka rigiman sai sun ci sun É—auka wani kayan gabas ne tana ba su, cin farko suka fara shirin dawo mata da shi.

"Ai sai kun ci shi."

Take faÉ—a tana musu dariya.
Hanan ta zubar da na bakinta.
Beena ta bi bayanta suna yamutsa fuska.

"Karyan tsiya kuke yi, kun san ba za ku ci ba kuka ce za ku ci?

Kamar za su yi kuka suka yi tsuru-tsuru sai ta koma tana yi musu dariya Sultan na taya ta.
Sai suma suka fara dariyan Harira ce ta gyara in da suka zuzzubar.
Chapter 36 · 0% Book details