← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 75

Sashe 26

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Me ya sa ma ta je ta same shi? Da ta san haka abubuwa za su lalace da ba za ta je ba. Haushi ta ji haushin yadda ya yi banza da ita ta je da nufin ta bi kadin abin da ya yi mata kuma ya bige da ribatanta har ta ba shi dama a kanta, dariyan da yake yi mata ne ya tunzarata. Ba ta ma san mganganun dake bakinta ba kenan ita dai a harzuƙe take a lokacin shi ya sa aka ce in rai ɓaci hankali ke neman shi magana kuma dafi ne kaifin dafin ta yafi kaifin takobi.

Ita dai maganganunta kaifin dafin sun soki Hamma Lamiɗo sokewar da bai taɓa tunani ba.

"Na shiga uku ni Ummu Salama."

Ita kaɗai take maganarta tana kuka, ta rasa wa za ta kira akan wannan matsalan duk in ta je ta faɗa to ita ce a kasa, ta yi tunanin kiran Baɗɗo sai ta tuna yadda suke ba daɗi ma, yanzu tana faɗa mata abin da ta yi abubuwa ne za su ƙara lalacewa.

Ta koma tana sake tura masa sakon ban hakuri.

"Ka yi hakuri Hamma suɓul da baka ne. Wallahi na yi nadama kuma na janye kalamai na"

"i'm Sorry ba zan ƙara ba."

Amma da alamun ma bai san tana yi ba, ta kasa barci ta yi kuka kamar me, daman a kwanaki nan ta ƙulla abota da kuka nadamar abin da ta faɗa kawai take yi.
Ta yi wankan tsarkin najasan dake jikinta sannan ta yi shirin kwanciya ta kwanta amma ta kasa barci a daran kuma ba ta san sau adadin nawa ta kira lambar Hamma LamiÉ—o ba amma kuma ya yi rufe ta da alamun ba za ta same shi ba.

Ga ta kwance kawai amma ta kasa barci sai tsiyayan hawaye. Tana mai ganin laifin kanta da ta yi hakurin da kowa ya ce ta yi da yanzu ba ta cikin nadama shima ya ba ta hakuri amma taurin kai da kafiya suka hana ta ganin hakurin da ya ba ta, sai ga shi da kalaman bakinta cikin mintina ƙalilan ta bata komai

Juye-juye kawai take yi da ta kasa barci dole ta miƙe ta shiga tiolet ta ɗauro alwala. Dole ne abubuwa su rikice mata ta manta da Ubangijinta. Tunda abubuwa nan suka faru da ita sai dai ta zauna tana koke koke ba ta tunawa da keɓe kanta ta faɗa ma Allah kukanta. Shi ya sa ta zama sai a hankali sai fama da zafin zuciya da fushi. Salla ta fara yi raka'a shidda ta yi sannan ta rufe da shafa'i da wutiri.

Ta ɗaga hannuwana sama tana kuka tana neman ma Baffa gafara tare da fatan Allah ya sanya jaririnta da ta rasa ya zama mai ceton su ranar gobe ƙiyama sauran addu'o'in nata duk akan Hamma Lamiɗo Allah take roko ya sassauta zuciyarsa akan ta, Allah ya yi ramgwame a cikin fushin sa zuwa gare ta. Ita dai ba ta da sauran kalaman kare kanta duk abin da za ta faɗa ta riga ta gama ɓata komai tun daga farko.
Sai uku da rabi na dare ta koma ta kwanta, tana kallon rufin É—akin kafin barci ya kwasheta ta share hawaye ba ta san iyaka ba.

*

A bangaren Lamiɗo kuwa yadda ya fita a cikin fushi ba ƙaramin ƙokarin iya sarrafa fushin sa ya yi har Allah ya kai shi gida lafiya ba.

Kalaman Ummu Salma na zuwa da dawowa a cikin kunnuwansa, shi bai damu da cewar da ta yi bai damu da rasa jaririnsu ba, amma cewar da ta yi bai san zafin da ta ke ji a zuciyarta ba, tunda shi bai rasa uba ba.

Maganar ta zo masa cikin bazata ne, bai taɓa tunanin haka daga Ummu Salama ba. Da gaske ne ba ta da kunya duk ya shanye rashin kunyarta ya ɗau ƙankanta ya bar mata girman don a zauna lafiya amma duk bai isheta ba sai da ta yi masa gorin ba Baffa ne ya haife shi ba.
Received at 07:52Reactions: ❤ 7, 👍 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ba domin ita ba ce, da wani ne da yau sai ya gane kuskuran shi. Amma duk da haka itama zai koya mata hankali, in taƙamarta rashin kunya da rashin iya magana to zai koya mata yadda za ta iya magana da shi, yadda anan gaba duk abin da za ta faɗa masa sai ta tauna shi ta tantance shi kafin ta faɗe shi.

Haka ya shiga bangaren Bilkisu a fusace yara duk suna falo har da Hanan suna ganin shi suka nufe shi suna kiran sunan shi da Papa
Amma duk yadda yake son yara bai tsaya kallon su ba.

Bilkisu na yi masa sannu da zuwa bai juyo ba ya shige daki ya banko kofa ya saka key, baya son kowa a kusa da shi saboda yana cikin fushi shi kuma in ranshi ya ɓaci ya fi son zaman shi kaɗai fiye da komai

Gefen gado ya zauna yana dafe kan shi da ya ji yana sara masa.

Ta ce ta rasa jaririnta amma bai damu ba saboda yana da wasu yaran?
Ta manta shi ne uban jaririn, ta manta irin soyayyar da yake yi ma cikin nan tun kafin ya zama gudan jini

Shi fa namiji ne ta ya zai zauna yana nuna mata rauninsa alhalin tana mace, zai iya rantsuwa abin da ya ke ji akan rashin jaririn su ita ba ta ji irin shi ba, ko don bai faɗa mata ba? Ko saboda bai zauna ya yi mata kuka ba? Wani abin ba ka sanin zurfin shi. Wani ciwon ba ya iya bayyanuwa a fatar baki zuciya kaɗai ke iya riƙewa.

A lokacin da ta faɗi maganar ta zo masa da zafi sosai, yana shirin ya dakatar da ita sai ta ɓata komai.

Har Baffa ya koma ga Allah bai taɓa jin sa ba a matsayin mahaifinsa ba. Rashin Baffa gibi ne shima a rayuwarsa domin shi ya fara sani a uba kafin Mai martaba. Yau shi Umma Salma ke yi ma gorin bai san zafin mutuwar uba. Ya runtse idanuwana ya buɗe bai san adadi ba, ya nutsa hannayensa cikin sumar kansa ba adadi huci da fitar da numfashi kamar zai shiɗe sai da ya ta shi ya shiga tiolet ya sakar ma kansa ruwa sannan ya ɗan samu sauƙi sauƙi.

Wayarsa tana silent ne sai da ya fito ya ga kiran Ummu Salma rututu, bai ma san yadda ya ke ji a zuciyarsa ba. Amma for now ba ya son ganin ta ko jin muryanta ta bar shi ya samu nisa da ita ko zuciyarsa za ta huce.

Blooking ɗin ta ya yi, ba ya son ma ya ga sunan ta tana kiran shi saƙon ta kuma ko ɗaya bai buɗe ba.
Ba ta kuma da sauran abin da za ta faÉ—a masa.
Maganganunta suna neman goge duk wani alherinta a gare shi.

A hankali a hankali ya ke jin kamar ta saka katanga ta katange duk wani hangen shi da zumuÉ—in shi a kanta, wannan soyayyar da kaunar da suka faro ta, tun daga farko yana jin tana yi masa nisa wannan kalmomin na ta sun sanya tazara mai yawa a tsakaninsu tazaran da suke tunanin sun daÉ—e da haÉ—e shi.

Bilkisu tunda ta ga yanayin shi ba ta neme shi ba, shima kuma daman haka yake so ya fi son ya kaÉ—aice shi kaÉ—ai
Ba ya son ya ganta ballatana ya ji kalaman bakinta gani yake yi yanzu duk abin da za ta faÉ—a ba zai zama mai daÉ—i daga gare shi ba.

A daran ya siya musu tiket ɗin zuwa Lagos. Tsarin shi ya ruguje kalaman Ummu Salma sun yi nisa da abin da ya shirya. Da ita ya so su koma a tare a sabon gida da ita domin su gina kyakyawan rayuwa a can har su mayar da jaririn da suka rasa amma a dare ɗaya ta ruguza wannan yaƙinin na shi akanta. Ba zai iya tafiya da ita ba, ko ta je can ba zai taɓa sauraranta ba yana bukatar lokaci mai tsawon da zai yi tunani amma shi ba zai sake yarda da ita ba, sai ta goge waɗanan munanan kalaman nata zuwa gare shi, kuma goge kalamanta abu ne da ba zai taɓa yuyuwa ba magana zarar bunu ce tunda ta fita ba za ta koma ciki ba.

A daran ya canza duka tsarin shi da ita. Ba yanzu ba wataƙika sai ya huce ko zai iya sauraranta amma yanzu ta zauna a gida hakan shi ne mafitarsu gabaɗaya.

Jirgin goma sha É—aya na safe za su bi zuwa Lagos.
Bayan ya dawo daga masallacin Jumma'a ya shiga É—akin Bilkisu ya sanar da ita akan su shirya akan lokaci.

Bai yi mata wata magana ba, kuma ba faɗa mata aka yi ba a jikinta take jin koma me ya ɓata masa rai to Umma Salma ne, zuciyarta kamar farar takarda tana ta addu'an Allah ya sa ba da ita za su tafi ba.
Received at 07:52Reactions: ❤ 14, 👍 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta fahimci tunda Baffa ya rasu ta kuma haihu ba É—a shi kenan ta ga ta É—an yi sanyi ta rage tsiwa da yi ma mutane kallon reni da ta je ta ganta shekaranjiya duk ta fita kammaninta sai da ta yi dariya ta tabbata a haka babu kuma abin da za ta birge LamiÉ—o da shi.

Ba ta tambaye shi ba, ta san in ma ba tare da Umma Salma za su tafi ba za ta ga ni in lokacin tafiyar ta yi. Da wuri suka shirya jikinta ya yi sanyi da ta ji ya ce tare da Hanan za su tafi to za a tafi da É—iya ne a bar uwarta anan sai murnan ta ya koma ciki.

Amma suna zuwa gidan Ammah ta samu amsar tambayanta.
Ammah ce da kanta take tambayan shi, shi ya ce Ummu Salma ta zauna anan sai ta sake warwarewa?
Chapter 26 · 0% Book details