← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 75

Sashe 35

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ko ka yi wanka zan ji ƙamshin."

"Bana son kamshin komai yana sani amai ƙamshin wannan ƙasar kaɗai nake so."

Ya zura mata idanuwa a zuciyarsa yana faÉ—in dankari .

"Sai dai ka zo ka yi wanka da sabuluna mara ƙamshi, ba za ka shafa mai ba sannan ba za ka fesa turare ba"

"Ba matsala?

Ya tambayeta domin shi gani yake ka yi ta shaƙan kamshin kasa ai akwai damuwa

"Hamma."

"Baby ke so fa ka gane."

Ta gama faɗa cikin shagwaɓa.

"Oh na gane."

Bai gane ba kawai dai ya ce ya gane ne amma ya saboda ciki kawai sai mutum ya ce ba ya son kamshin komai sai na kasa.
Shi ɗakinsa ya ce zai je ya yi wanka ta ce yana da mayuka da sabulan wanka ma su ƙamshi ba ta so haka nan ya shiga wanka a ɗakinta
Received at 17:28Reactions: ❤ 12, 😁 2
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sabulu ne bai taɓa ganin irin shi ba ko kumfa ba ya yi, ba ƙamshin ko kaɗan daga karshe ma ruwa kawai ya watsa ya fito tuni ta kwashe kayan da ya cire ta tura cikin wadrope wai suna ƙamshi, ta fito masa da riga da wando, babu kamshi a jikinsu domin tunda ta dawo gidan ba ta yi amfani da turare ba yana ji yana gani aka hana shi shafa mai wai zai yi ƙamshi ba ta so dole ya hakura.
Ga wani jidali duk in da za ta je tana tafe da gwangwanin kasanta abinci ta ce mai Harira za ta dafa masa?

"Ke nake so ki yi mini girki."

Ya faɗa mata lokacin yana gaban madubi yana tashe sumar kansa. Sai da ya duba ya ga ba komai duk ta kwashe duk wani mai ƙamshi ta ɓoye wannan cikin na gaske ne.

"Bana iya girki Hamma bana son ƙamshi girki"

Ta cikin madubin ya hangeta ta zauna a tsakiyar gado ta tankwashe kafa kawai tana ta shakan ƙasan hannunta

"Cikin nan ya saka ki rama."

"Na sha wahala ne Hamma."

Ta amsa mishi kafin ta fara ba shi labarin irin wahalan da ta sha tana ma kan sha.

"Tun cikin na 2week ya fara bani wahala."

Ya gama abin da yake yi ya taho zuwa gare ta.
Shima ya hayo gadon ya zauna sannan ya janyota jikinsa tana ta shinshina shi.

"Wari nake yi ko?

Ta kalle shi ba ta yi magana ba.

"Wai da sabulunan kike wanka?

Ta gyaÉ—a masa kai.

"Tab dole ki yi baki, sabulu ne? Kamar ƙasa ko kumfa ba ya yi."

Ta fara dariya tana faɗa masa Umma Balki ta aiko mata da shi ta ce a can shiyar sokoto ake samun shi ba shi da ƙamshi ko kaɗan.

"Ummu Salama."

Ta kalle shi, shima ita yake kallo.

"I'm Sorry."

"Na barki, kina ta wahala ke kaÉ—ai"

"Ba ni kaÉ—ai ba ne, kowa na tare da ni kai kaÉ—ai ne na yi missing"

Ya jawo jikinsa ya rumgume.
Yana faÉ—in ya yi mamakin da ba wanda ya faÉ—a masa halin da take ciki.

"Abdullahi kodayaushe sai ya ce mini kina lafiya. Ammah ma ba ta taba faÉ—a mini wani abu ba. Gwara ma Mami tafiyata ba daÉ—ewa mun yi waya ta ce ga shi nan Allah ya bamu wani rabon."

"Lokacin ban gane me take nufi ba sai yanzu."

Ya gama faÉ—a yana kallonta.

"Ammah ba za ta faÉ—a maka ba kunya take ji saboda ni. Hamma Abdullahi kuma ba zai yi tunanin ba ka sani ba. Kowa ma har Mamin za su yi tunanin ka sani na faÉ—a maka tunda ban taba faÉ—a ma kowa abin da ke faruwa a tsakanin mu ba."

"Good, personal life É—in mu ne ba sai kowa ya ji ba."

Ya amsa mata.

"Ba ni labarin abubuwan da suka faru lokacin da bana nan"

Ta ce ba zai ci abinci ba? ya ce sai anjuma.
Nan ta lafe a jikinsa ta shiga ba shi labarin wahalan da ta sha tana yi tana shaƙan kasanta daga karshe ma shi yake miƙo mata gwangwanin yana hannun shi. Ya ji tausayinta sosai yana ta bata hakuri ita in ta ce ya yi hakuri sai ya ce

"Kar ki kara tuna wannan maganar. Na manta da ita har gaban abada."

Amma shi haƙuri yake bata na yadda ya yi dogon fushi da ita a lokacin da ya kamata ya kasance a kusa da ita, ta ce komai ya wuce tana jin kamar ma komai bai taɓa faruwa na faɗa a tsakaninsu ba wannan tazaran da Lamiɗo ke tunanin akwai tuni ya amince da cewa babu ita a tsakanin shi da Umma Salma har abada.

Suna cikin É—akin nan manne da juna kiran sallar mangariba ne kawai ya tashe su. Shi daman a Airport ya tsaya ya yi sallar la'asar ba wanda ya san ya dawo mashin ya hawo zuwa gida.

Da ya fita salla mangariba sai da aka yi isha:i ya dawo lokacin har Umma Salma ta sake wanka ta sauya kaya wani riga da wando masu taushi. Abinci kuma Harira ta saka ta dafa masa ruwan tea da ya ji kayan kamshi daman ta yi farar shinkafa da miya da nama sai ta ce ta zufa masa har da salat.
Lokacin da ya dawo É—akin shi ya shiga ya yi waya da Bilkisu yana ta mamakin ta wannan karon har da murnanta da ya ce mata zai taho Adamawa ya zauna ya yi tunanin dalilin murnan nata ne bai samu lokaci ba.

Abinci shi kaɗai ya ci a dinning tunda Ummu Salma ba ta son ƙamshi ita kuma sauran tuwonta aka ɗumama mata. Shi ko iya kallon tuwon ya kasa yi da bakar miyar nan zai je ya yi magana da Ammah me ya sa za ta dinga cin wannan abincin? Sannan shi ba ya son tana shaƙan ƙasan nan kar wani cuta ya kamaata ga dariya ga tausayi lokacin da take faɗa masa wai kasar kofar gidan Baffa ne kaɗai take ƙamshi, na anguwan nan Harira ta
Received at 17:28Reactions: ❤ 16, 🥰 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
ɗibo mata babu ƙamshi.

A daran Saddam ya zo ya kawo mata goro da ƙasar sai ya ga Lamiɗo. Kasar ma kamar ta roƙa a wata leda ce ƙarama ta ce ya mayar kawai ita da take da shi da yawa.
Har tana sa Harira na É—auko masa ya gani yana dariya Hamma LamiÉ—o na dariya kasa ne rabin buhun baggo ina lafiya.

Anan ya ci abinci kafin ya tafi Hamma LamiÉ—o ya ce sai gobe da safe za shigo ya gaishe da su Ammah ya amsa da to zai faÉ—a musu.

Da wuri suka yi shirin kwanciya saboda wannan sabulun ko wanka bai sake marmarin yi ba. Kayan barci ma sai da aka zabo waɗanda ba sa ƙamshi bayan an gama shinshinawa aka ba shi ya saka.

Halin da take ciki ya sa bai nuna yana son kaÉ—aicewa dai ita ba, duk da yana muradin haka.

Sai ita ce suna kwance maƙale da juna hiran na ta ya ƙare shuru na wani lokaci hannunsa dai na kan cikinta yana shafawa.

"In sha Allahu wannan karon za mu samu mai sunan Baffa.'

"In mace ce fa?

"Ki zaɓa mata suna. Gaba in mun samu namijin mai sunan Baffa ne."

"Allah ya jiƙan Baffa."

Ya faÉ—a cikin wani irin amo.

"Amin Ya Allah."

Shuru ya sake wanzuwa da ta fahimci ba zai taƙaleta ba.
Sai ta ƙara shigewa jikinsa tanakiran sunan shi.

"Hamma."

'uhm"

"Ka taƙale ni"

"Ba matsala ?

"Ko Baby shima ba ya so.."

Ba ta bari ya ƙarisa ba ta fara sumbatar bakin shi, shima sai ya mara mata baya

Ya ɗauka shima baby baya son wannan taƙalen ne sai ga shi ya fahimci yana so sosai ma, domin ta nuna masa hakan kuma ya gani dukkansu sun yi kewar junansu domin gangar jikinsu ta tona musu asiri.
Sai da suka yi wanka suka samu tsarki sannan suka koma suka kwanta.

"Hamma."

"Uhm"

"Ba ka jin ƙamshi a jikina ko?

"I don't care "

"Wari nake yi ?

"Ki bari. Bana so."

A kausashe ya faɗa shi yasa ta san da gaske baya so. Hannun shi na saman cikinta suka yi barci amma ta yi ta tashi cikin dare tana shaƙan kasanta da asuba ma sai da ta yi amai abincin da ta ci amma tunda ta ɗan gutsiri goron da Ammah ta aiko mata da shi ta ɗan samu saukin tashin zuciyar.

Da safe kasa cin komai ta yi, ta ce Harira ta yi zamanta ba sai ta yi mata tuwon ba za ta je gida kila su Ammah sun tara mata kanzo daman suke shanya mata ya bushe Ammah daga zaune ta daka mata a ƙaramin turmin ƙarfe.

Shi ne kawai ya sha tea, karfe goma da rabi suka bar gida key É—in duka motocinsa yana hannun Umma Salma ne, Hamma Abdullahi ya kawo mata.
A toyota É—in suka fita suka bar Harira a gidan.

Daman tun jiya Saddam ya sanar da su Ammah zuwan LamiÉ—o zuwansa bai yi musu ba zata ba. Gidan ba kowa Saddam da Abdulrahim duk suna wajen aiki.
Sai Ammah kaÉ—ai da Umma A'i sai Ummin ikki sun shigo ba daÉ—ewa sai ga ta tazo gidan

Kanzo nan ko Umma A'i ta daka ma Ummu Salma ta saka mata gishiri da farin magi ta É—an yayyafa mata ruwa ya yi taushi shi ta ci abu kamar magani amma ita ya yi mata daÉ—i.
LamiÉ—o na zaune mamaki kawai yake yi Bilkisu ta haihu sau biyu amma bai ga wannan matsalan tare da ita ba.

Cikin farko ma bai kai wannan cikin wahalar da Umma Salama ba. Sai da ya yi ma Umma A'i mgana wai kar ta zo ta samu wani cuta ba ta cin abinci mai gina jiki ga shinshinar ƙasa.

"Ko wani ciki da na shi salon Lamiɗo. Auta da tunda ta samu cikin nan take wahala kuma in ka ga irin haka wataƙila har ta haife shi tana laulayi nan."

Ya zaro ido irin abin ya ba shi mamaki

Ammah na gefe tana dariya ba ta yi magana ba.
Chapter 35 · 0% Book details