Sashe 48
Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga lokacin Masarautar aka fara yaɗa jita jitan magana duk da ba wanda ya san asalin abin da Mai martaba yake son aiwatarwa amma maganganun nata ta shi tunda ba a taɓa ganin Mai martaba ya yi irin waɗanan ganawar cikin sirri haka ba, ba kuma wanda ya sani waɗanda suka sani ɗin kuma ba su da ikon cewa komai.
Manyan majalisar zaɓen fada da suka yi ta shiga suna fita su ne su Waziri, Madaki, Galadima da Yarima Lamiɗo, sai Sallama musamman mai sharia da zuwansa fada wajen su uku.
Kuma ga shi ba wani magana da ta fito daga fada daga yawun Mai martaba amma mganganu na ta tashi. Gimbiya Shahida ta so tambayan Mai martaba abin da ke faruwa ba ta samu fuska ba, ba ma ita ba duka sauran mata ya ce su jira lokaci kawai.
Gimbiya Hadiza har ta kira Bilkisu ta faɗa mata wani abu zai faru Yarima ya zo Daura kuma Mai martaba na ta ganawar Sirri da Manyan wakilan fada. Ga shi daman Bilkisun ba ta samun shi a waya har ta shaƙa da kishin ya tafi can wajen Ummu Salma ya manta da ita ashe yana Daura, kuma bai faɗa mata zai zo Daura ba.
"Ya Hadiza me ke faruwa ne? Bana samun wayar LamiÉ—o wajen kwana uku kenan?
"Ba za ki same shi ba, ba shi da lokaci ana ta tunanin ko sabon Sarauta Mai martaba zai yi masa"
"Akwai Sarautan da ta fi Yarima ne?
Gimbiya Hadiza ta ce" Ko Chiroma zai yi masa, kin san Sarautar Yarima ba dole sai wanda zai gaji Sarki ba ita kuma Sarautar Chiroma magajin Sarki ne kuma babban ɗan sarki ake ba ma wannan Sarautar na fi tunanin wataƙila tunda Mai martaba na son ya gaje shi bayan ba shi shi yasa ya yanke shawaran yi masa wannan sarautar yanzu."
Bilkisu ta gamsu kamar yadda itama Gimbiya Hadiza take tunani. Ba ma su ba kowa tunanin da yake yi kenan. Ba wanda ya yi tunanin Mai martaba zai iya tsallake gurbabe masu girma har ya kai matakin da ya yanke a yanzu.
*
Ummu Salma ma daga nan Egypt hankalinta duk a tashe tunda LamiÉ—o ya tafi bai kira ta ba, itama ta kira shi ba ta same shi ba. Hankalinta ya É—an kwanta ne da ta kira Fulani ta ba ta tabbacin yana lafiya har a lokacin yana Daura wasu azurori ne masu girma suka sha masa kai, shi ya sa ta É—an kwantar da hankalinta.
Amma mamakinta kwana uku huɗu a ce Hamma bai kira ta ba, ko Daura ya je ba ya kwana bai neme ta ba in ma an kwana ba za a yini ba. Amma har kwana huɗu shuru babu wayarsa sannan abin da ya ba ta mamaki daɗewarsa a Daura ahalin ya ba ta tabbacin in ya daɗe ne ya yi kwana biyu. Ga shi Fulani ta ce wasu uzirori sun riƙe shi, da ta kasa gane wasu irin uzirori take magana, suma can Adamawa suna video call ko vioce call suke yi da su ko ta wayar Baɗɗo ko ta wayar Hamma Saddam suma ɗin sun ce ba su yi magana da Lamiɗon ba.
Har Ammah ta ce tun saukarsu da suka yi magana ta kira wayarsa a kashe a bakin Mami ma take jin Mai martaba ne ya kira shi yana can Daura. Babu wanda ya yi tunanin a halin da Lamiɗo yake ciki ba ya ma tunanin su, tunanin tarin wasu nauyin alummar dake ƙoƙarin rataya a wuyansa yake yi. Waya ma ya manta da ita. Barci sai dai ɓarawo kawai ke iya fizgan shi.
Yana cikin damuwar, kuma dole ne ya cika Umarnin Sarki ko yana ko ba ya so.
Mami ce dake tare da Ummu Salma ke kwantar mata da hankali. Domin ba a so kuma ta shiga damuwa har jininta ya É—aga. Hankalinta ya kwanta tunda yana can Daura ta tabbatar yana lafiya amma nemanta ne da bai yi ba zuciyarta ba daÉ—i.
Received at 18:55
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ranar talata da suka cika sati É—aya a kasar na Egypt, ya kama kwanan LamiÉ—o biyar da tafiya kenan cikin dare 8 ga watan November misalin uku na dare Ummu Salma ta haihu, Alhamdulillah kawai za ta ce da godiya ga Allah.
Kamar wasa tana cikin barci naguda ya tashe ta daman akwai wata na'ura ta emergency dake gefenta an faɗa mata in wani abu ya taso ta danna wannan na'uran zai yi ja, ya yi ƙara domin a san tana buƙatar taimako.
Da ta ji ciwon baya ga maranta ya riƙe ta so ta miƙe ta kasa da wani ciwon maran ya tirniƙeta ba ta san lokacin da ta matsa abin nan ba ya yi ƙara cikin lokaci sai ga likitoci da Nurses sun cika ɗakin da take ana gwadata aka ce haihuwa ce ta zo gab. Ba ta taɓa tunanin za ta iya haihuwa da kanta cikin lokaci haka ba.
Da fara naƙudarta da haihuwarta mintina talatin ne ta haifi ɗiyarta mace kyakyawa ƙatuwa da ita kamar Lamiɗo ya yi kaki, kuma cikin ikon Allah ko ƙaruwa ba ta yi ba.
Cikin awa É—aya nurses suka gyara ta, tare da Baby gabaÉ—aya É—akin ya dawo fes kamar ba a haihu ba.
An yi ma jinjirar wanka an saka maka kayan sanyi masu kyau daman kayan haihuwan da suka taho da shi suna cikin drowers ɗin cikin ɗakin. Nan da aka kawo ƙaramin gado na jariri aka saka ta a ciki sai wuntsila kafafu take yi irin na yara amma kafin nan sai da aka ba ma Ummu Salma jaririyar ta rumgume ta ji ɗuminta tana hawayen farinciki.
Ta ba ma Nurses É—in wayarta suka É—auke su hotuna sannan suka yi ma jaririyar hotuna itama
Ko kafin Asuba har ta koma barci, kamar ba ta haihu ba.
Ummu Salma ta tabbatar wannan asibitin wajen kulawa da ba ta ki duk haihuwanta ta haihu anan ba, ga shi jininta bai hau ba sun ce 120 sannan su za su yi maka komai kamar kana É—akin mahaifiyarka.
Ga abinci mai rai da lafiya da zai ingata lafiyarka.
Karfe shidda na safe ta tashi barci Nurses suka tashe ta, ta yi wanka ta gasa jikinta sosai suna faÉ—a mata kar ta yi amfani da ruwa mai zafi sosai saboda BP. ta ce musu to amma ba ta sauraresu ba, ba za ta biye musu ba gwara ta gasa jikinta. Da harshen turanci suke magana tana ji sai dai mayarwa ne take amsa musu da iya abin da ta iya kuma suna ganewa
A karo na farko Ummu Salma ta ji ra'ayin son komawa makaranta domin maganar Hamma Kabiru gaskiya ne ilimi ginshiƙi ne na rayuwa akwai in da za ka je ka ga ana yi babu kai.
In ta ga yadda Mami ke turanci sai ta ji ta burgeta har ta ji wataƙila ta sauya ra'ayi ta koma makaranta. Sun yi ma jinjirar wanka an sauya mata kaya ba su damu da nono ba har sun fara ba ta madara. Ita ma daman ruwan nonon bai zo ba har matsawa ta yi sai dai kaɗan kaɗan, Itama sun ba ta abin kari mai kyau ta karya sannan ta karɓi jinjirar ta rumgume tana yi ma Allah godiya. Bayan fitan Nurses ɗin ne ta samu damar kunna data, Lamiɗo ta so ta fara kira amma baya online sai kawai ta tura masa hoton jinjirar. Sannan kira Mami domin ta ga tana online.
Video call ne Mami na É—auka sai ganin Ummu Salma ta yi da jinjira a hanunta baki ta saki.
"Me zan gani? Daughter kin haihu ne?
"Mami na haihu, abin mamaki Mami na haihu."
Ummu Salma ta faɗa tana washe baki idanuwanta sun cika da ƙwalla.
Mami ta yi kabbara tana jera Hamdala Ummu Salma na ji Mami na ƙwalama Harira kira sai kuma ta katse wayar.
BaÉ—É—o ta so ta kira sai ta ga ba ta online sai kawai ta tura mata hoton su da aka yi mata da jinjirar lokacin da ta haife ta.
"Alhamdulillah É—iyarki ta zo duniya jiya da daddare"
Ta so ta tura a gidan Baffa da Ammah kunya ya sa ba ta tura ba.
Kafin ta kashe datar sai da ta koma ta kira lambar Hamma shuru ba ta same shi ba tana farikciki amma ya É—an samu nakasu, tunda ba Hamma a kusa da ita. Ta haihu amma bai sani ba ta kira shi kuma ba ta same shi ba.
Hoton jinjirar ta tura ma Gimbiya Shahida sannan ba ta kashe datar ba ta koma ta kwanta ba kawai ta yi zaune tana ta kallon jaririyar tana ta barcinta hankalinta kwance.
Mami da Harira suka baro hotel suka hau Taxi zuwa cikin asibiti.
Suna cikin tafiya ne Mami ta shiga instagram saƙon da ta ci karo da shi yana yawo ne ya firgita ta.

BBC HAUSA suka fara fitar da sanarwan sannan sauran gidan jaridu suka fitar tare da sauran mutane suna ta sawa. Hannunta na rawa ta fita ta shiga goggle ta yi searching Masarautar Daura sai ga labarin ya fito, ta zaro ido cikin mamaki.
"Kai.."
Ta faɗa da ƙarfi har Harira na tambayanta ko lafiya ta kasa cewa komai da ta shiga wasop ta ga Hajiya Falmata ta turo mata.
Sannan Hamma Kabiru ma ya turo mata.
"Mami is this true?
"Na kira wayar Amini a kashe"
Itama abin da ta gani kenan amma ba ta da tabbacin domin ba ta san komai ba tunda kuma ga shi ana yawo da shi gaskiyan kenan.
Suna isa asibitin waya a hannunta ta shiga É—akin da Ummu Salma take suka same ta ga jaririyar kwance gefenta ga kuma wayarta a hannunta.
Suna shigowa ta É—ago tana kallon su.
"Mami."
Ta kira ta da ƙarfi.
"Mami wai Hamma ya zama SARKI?
Ummu Salma ta faɗa cikin ƙarajin da muryanta cikin ruɗewa Mami ta ƙarisa kusa da ita Harira kuma ta sandare a tsaye.
"Mami da gaske ne?
"Nima haka na gani."
Mami ta amsa mata tana jin wani abu a ƙasan zuciyanta da ta rasa ko mene ne.