Sashe 53
Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta yi kewarsa sosai kuma har kewar ya bayyana a idanuwanta. Ƙwallar da suka taru suka sauko mata ta saka hannu ta share, shi kuma yana kwance kansa kawai ya ɗan dago jikinsa ba riga amma ya rufe da blanket.
Ummu Salma ce ta zuro kafafunta ƙasan gado ta saka tattausan silafas ɗin dake wajen.
Yana kallonta yana jin zuciyarsa na tsukewa a waje É—aya. Ta kara masa fari sannan ya ga ta kumbura.
"Me ya same ki? Fuskarki ta kumbura."
"Haihuwa ce."
Ta amsa mishi tana shafa fuskarta.
"Kina lafiya?
"Ba wata matsala?
"Ina Babyn mu?
Ya tambayeta a jere amma a rarrabe.
Received at 15:16Reactions: ⤠14, 🥰 2
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Lafiya lau na haihuwa cikin kulawa baby tana lafiya bari ka ganta."
Ta tashi ta isa in da ɗan gadon jariiyar in da take ciki tana barcinta ta haska mishi ita. Ya ƙura mata idanuwana yana kallonta cikin wani shauƙi.
"She is so cute."
"Kama da kai take yi "
"A'a ke ce."
"Ka duba da kyau Hamma."
Tana cewa shi ne yana cewa ita ce, daga karshe ya sakar mata da cewa da shi take kama duk da shima ya ga haka.
Ɗauko yarinyar ta yi ta koma gefen gado ta zauna tana riƙe da ita suna cigaba da magana.
Nan yake faÉ—a mata Hamma Kabiru na hanya da kuma yankaar da za a yi gobe a can gida Adamawa.
Daman sun yi vioce call da Baɗso ɗazu ita ta ba ma Ammah waya suka yi magana. Ta faɗa mata an siya raguna guda huɗu za a yanka sunan yarinyar suka yi magana ta ce ba su yi magana da Hamma ba tukunna, na zuwan Hamma Kabirun kuma kafin Mami su tafi masauki ta faɗa mata ya yi mata saƙo yana tafe.
Cewa ya yi ta yi ta haska masa baby yana kallonta.
Ta yi masa abin da yake so, ga shi tana da barcinta ba ta ma san ana yi ba.
"Hamma."
Ta faÉ—a tana karkato da wayar a fuskarta.
"Ba ka faÉ—i sunan da za mu saka mata ba! Ko ka faÉ—a ma Hamma Kabiru ne?
"Aa ban faÉ—a masa ba "
"Shima na ce in ya zo ya tambaye ki."
Ya amsa mata yana kafe ta da idanuwansa masu sanyata jin kamar tana jin sanyi.
"Ni zan faÉ—i sunan Hamma?
Ta faÉ—a tana mirmishin jin daÉ—i
"Na ba ki zaɓi"
"Da namiji ne mai sunan Baffa ne, amma tunda mace ce Allah ya ba mu na ba ki zaɓi"
"FATIMA."
"NA ZAÆA MATA FATIMA."
Ta furta tana kallon shi. Sai ya jinjina kai ya gyara kwanciya yana faÉ—in.
"Allah ya raya mana mai sunan Mami, Allah ya yi mata albarka."
Ta amsa da Amin tana dariya.
Shima mirmishin yake yi, Ummu Salma kamar tana shiga zuciyarsa yawanci tana cika muradinsa tun kafin ya furta tun lokacin da na'ura ta nuna mace Ummu Salama za ta haifa a zuciyarsa ya ce zai yi ma Mami takwara, tunda ya yi ma Ammah to ya ba ma Ummu Salma zaɓi ne yana tunanin ra'ayinsu zai zo ɗaya sai ga shi ba ta ba shi kunya ba.
Sun yi shuru kawai suna kallon juna shi ne ya katse ta da cewa ba ta jin komai ba ta da wata matsala ta ce babu nan ta shiga ba shi labarin yadda ta haihu.
"Hamma abin mamaki ko awa É—aya ban yi ina naguda ba na haihu, kuma jinina normal na haihu lafiya"
"Alhamdulillah."
Ya faÉ—a yana cigaba da sauraran ta tana cigaba da ba shi labarin Mami ta matsu su koma gida saboda wai ta yi mata wankan jego na gargajiya, sannan ruwan nonon ta, bai zo da yawa ba ta ce in sun koma gida a nemi maganin gargaji yanzu Baby sai dai ana haÉ—a mata da madaran yara. Shi kuma ya ce za su dawo gida in dai likitoci sun tabbatar da ba matsala in Hamma Kabiru ya sauka zai yi masa waya kawai ya jira su taho tare.
"Hamma wani suna za mu dinga yi ma Baby alkunya?
"Ni kuma? Ta ya zan sani"
"Mu kira ta Baana tunda muna da Beena?
"Baana?
Ya maimaita cikin sigar tambaya.
"Mene ne ma'anarsa?
Ta fara dariya tana faÉ—in ba ta sani ba.
"Nima ban sani ba ko Beena Bilkisu ce ta saka mata."
"Ki samu suna mai ma'ana kar ki je ki saka ma Æ´ata sunan mayu."
Ya faÉ—a har yana yi mata gargaÉ—i da hannu ta fara dariya har sai da baby Fatima ta farka ta yi saurin danne bakinta.
Cewa ya yi ta ba ta nono yana gani sai ta ajiye wayar ta saita a saman ɗan drower ɗin dake gefen gadon ta fara ba ta nono yana kallon su cike da sha'awa da kewa ba domin wannan sarautar ba da yana tare da su a halin yanzu. Ita kuma tana so ta tambaye shi Hanan tana jin kunya, ta san ko ta nan ko ba ta nan Hanan tana cikin ƙoshin lafiya.
Kallon su kawai yake yi, Ummu Salama ce ke magana shi dai na shi kallo ne da ji, sai da ta gama ba ta nonon ta ƙoshi sannan ta je ta kwantar da ita aɗan gadon ta saboda ta koma barci.
Sannan ta dawo ta É—auki wayar suka cigaba da hira.
"Hamma."
"Matar Hamma"
"Kana cikin damuwa ko? Na sani ba ka san sha'anin mulkin. Amma ina so ka sani haka Allah ya kaddaro mana ba mu da yadda za mu yi."
Ta dakata tana kallon shi yana lumshe idanuwana yana buÉ—ewa.
"Gani nake yi kamar ba zan iya ba. Akwai wahala mulki Ummu Salama akwai wahala."
Ya gama faÉ—a a muryansa za ka gane yana cikin kasala da sanyin jiki.
Received at 15:16Reactions: ⤠17, 🤗 2

Sannan ya ga Hamma Saddam online jin yana gida sai ya kira video call na gabaÉ—ayan su a group na Ammah da Baffa, waÉ—anda ke kusa suka É—aga kamar Hamma Saddam da Hamma Abdulrraham da Hamma Abdulrahim sai Hamma Abdullahi Hamma Mustapha ne bai É—aga ba sai LamiÉ—o, Ummu Salma ma ta kama a wayarta.
Hamma Saddam ya je falon Ammah tana tare da Umma Balki da ta iso a daran jiya, shi kuma Hamma Abdulrahin yana tare da BaÉ—É—o ne.
Kowa na ganin kowa nan ya ce ga shi ya iso har an yi ma yarinya huÉ—uba da Fatima.
"Allahu akbar Allah ya raya mana Fatima."
Ammah ta faÉ—a tana cigaba da addu'a. Umma Balki ma ta yi fatan alheri tunda har Ummu Salma tana kai.
"Gimbiya Auta ya jikin na ki?
Umma Balki ta faɗa ta saka kowa dariya sai yi ma Mami tsiya take yi wai ta yi takwara baki yaƙi rufuwa.
"Ina shi Lamiɗon na ɗauka ni zai yi ma takwara sai ya yi ɗanwaken zagaye? Idona idon sa sai na ci ƙaniyarsa."
"Umma Sarki ne fa, yanzu ko magana kika faÉ—a mara daÉ—i dogarai za su yi miki ladabi."
Hamma Saddam ya amsa mata ana ta dariya bayan ta ce ƙaniyarsa. Tana faɗin suna murna ga Lamiɗo Allah ya ta ya shi riƙo.
Sannan da cewa yaushe za su dawo? Mami ce ta amsa da cewa sun kusa dawowa ƙila ma su dawo tare da Hamma Kabiru gabaɗaya.
Bayan an gama ganin juna da gaisawa aka haska ma Umma Balki da Ammah takawaran Mami suka ganta, sauran duk sun bar video ca É—in tunda Hamma Abdullahi ya ce zai zo gidan yanzu da masu yanka mahauta kenan za a yanka ragunan a gyara.
Ammah ta ce ta faɗa ma maƙota da sauran abokan arzuƙa za ta ɗan yi taron suna a yau ɗin Mami ta ce hakan ma ya yi.
Daga karshe BaÉ—É—o kawai aka bari da Ummu Salma suna magana, Hamma Abdulrahim ya bar mata wayarsa.
"Sisna, Allah ya raya mana takawaran Mami ko na ce Sarauniyar Daurama."
"Amin"
Ummu Salma ta amsa tana mirmishi.
Tana yi ma BaÉ—É—o tsiyan ya amarci ta ce gamu cikin shi Ummu Salma ta ce Allah ya ba da sa'a.
"Wani inkiya za mu dinga kiran takawaran Mami?
"Banafsha na daÉ—e ina son sunan nan."
"Miye ma'anarsa? Mai Martaba Sarkin Daura Muhammad LamiÉ—o ya ce kar na saka ma É—iyarsa sunan mayu."
Ta faɗa ƙasa ƙasa kar su Mami su ji Baɗɗo ta fara dariya.
"Suna ne mai kyau da tarihi. Sunan larabawa ne, kuma yana nufin mace mai kamewa da natsuwa"
"To shike nan, ki faÉ—a ma kowa sunan da za mu dinga kiran takwaran Mami Banafsha."
BaÉ—É—o ta amsa da yanzu kuwa sun rabu bayan ta ce Umma Salma ta É—auki hoton Banafsha ta tura mata, tana hannun Mami ne, likitocin ma ba sa bari ana É—aukanta sosai sun fi son ta a kwance a É—an gadon ta.
Sai da Nurses suka shigo sannan Banafsha ta dawo gadon ta lokacin Ummu Salma ta É—auke ta hoto an yi mata gayu da wasu fararen kayan sanyi. Nan take ta tura ma BaÉ—É—o itama a karo na farko ta yi status da hoton Fatima(Banafsha)
"Alhamdulillah it's a Baby girl. Today, we named her Fatima, Fatima Muhammad Nasiru(Banafsha.)"
Haka ta yi status, waÉ—anda suka gani suna ta Allah ya raya. Hamma Saddan ne yan gaba gaba tuni ya É—auka shima ya yi status da shi.
Sannan Iklima da su Kaltume duk sun gani sun yi mata barka tana da lambar Hajiya Falmata itama ta gani ta ce haihuwar na su ne tunda takwaran Mami ce daman ta yi mata barka da suka yi magana ta wayar Mami.
Sai su Adda Suwaiba suna ta Allah ya raya tare da tambayan yaushe za su dawo ta ce an kusa.
Ta tura ma Hamma LamiÉ—o hoton, ya tafi sai dai kafin ya duba ne aiki a baya ma ana fama ballatana yanzu. Ba ta yi wani mamaki da Bilkisu ba ta yi mata barka ba, ba su da lambar juna amma ai haihuwa ta wuce wasa.