← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 75

Sashe 18

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammah ma sai da ta tsaya da kukan Mami da Umma Balki har suna haÉ—a baki wajen kiran sunan shi a firgice.

"Ƙul kar na sake jin wannan maganar a bakin ka."

Mami Ta faɗa cikin ƙaushin murya.
Hamma Jibo ya ce abu bai yi daɗi ba tunda ran Lamiɗo ya ɓaci sai ya ce Kabiru ya janye su fita waje

"Gaskiya ya faɗa abin da ta nuna kenan sai ya sake ta, ta je can ta ƙara ta."

Ammah ta faÉ—a da iya gaskiyanta.

"Haba Ammah."

Hamma Abdulrahim ya faÉ—a, da tunda aka zauna bai ce komai ba sai yanzu.

Hamma Kabiru ya ja hannun LamiÉ—o yana faÉ—in ya zo su fita.

"Ba ta kyauta ba, Amini kar ka biye mata."

Ummu Salma ta ga tunda ta rasa Baffa sai me don ta rasa LamiÉ—o? Tunda ya iya cewa zai iya sakinta ai ya yi rugurugu da yardan dake tsakanin su.
Sai kawai ta miƙe tana kuka.

"Sai me in ka sake ni? Ka sake ni mana ai ba zan mutu ba, na rasa ma Baffa ban mutu sai me don na rasa ka? A baya ma an sake ni kuma ban mutu ba yanzu ba.."

Ba ta kai ƙarshen maganar ba Mami ta buge mata baki.
Received at 11:37Reactions: ❤ 9, 👍 2
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Rufe mini baki, ba ki da kunya ne?

"Umma Salma kin yi hauka ne?

In ji Hamma Jibo.

"Sisna.."

BaÉ—É—o ta kira sunan ta a zafafe domin ta fahimci ta fara zarewa.
LamiÉ—o kuma cak ya tsaya ya juyo suka kalli juna.
Ya ga duk abin da take faÉ—a a cikin idanuwanta kenan da gaske ne zarginsa ta fi son Habib akan shi.

Da gudu ta ruga ta shige ɗaki ta kulle kanta ta kwanta a saman cafet tana wani irin kuka mai cin rai da ƙuna ga gunji. Tana jin mikin ta na aiki na yi mata zafi amma ba ta jikinta take yi ba kuncin dake cikin zuciyarta ne ya fi raunin da ke waje zafi.
A falo kuwa LamiÉ—o bai sake magana ba ya fita lokacin ma har an fara kiraye kirayen sallar mangariba.

Suma sauran mazan fita suka yi domin É—aura alwala suwa masallaci. Ammah kuma É—akinta ta shige.
Mami ta zauna tana faɗa ma su Umma Balki Umma Salma na cikin damuwa su yi mata uziri. Ga shi a gaban su Islam aka yi duk sun yi wiƙi wiƙi.

Umma Salma kuma ta ƙi buɗe ƙofa Baɗɗo ta yi ta magana shuru.
Daga karshe ma Ummin ikki tabi suka koma gida Ammah kuma kamar an yi mata fami ta shige cikin ɗaki tana ta kuka haka su Adda Nauwara suka dawo gidan duk a rikice Adda Safina ce ta kora musu abin da ya faru suma jikina su duk ya yi sanyi.
Lamiɗo kuma bai dawo cikin gida ba sai da safe a gidan shi ma ya je ya kwana tunda Hamma Saddam ya zo ya karɓi key ɗin bangaren Bilkisu a daran.

Da safe kuma jirgin karfe goma ya bi zuwa Katsina
Ya shigo ya yi ma Ammah da su Mami Sallama.
Mami ta bi shi har haraba in da Hamma Abdullahi ke jiran shi zai kai shi filin jirgi

Wai kar ya biye ma maganganun Umma Salma tana cikin halin tausaya mata ne. Shi mai zai ce ban da ya ce to kawai.
Mamin na faɗa masa sai da safen nan Ummu Salma ta buɗe kofa ta damu kar wani abu ya same ta. Ko a fuska bai nuna ga yanayin da yake ciki ba, amma tabbas kalaman Umma Salma sun dake shi matuƙa.

Shi na shi maganar ya faɗa ne cikin ɓacin ran abin da ta yi, amma ita ba cikin bacin rai ta furta na ta kalaman ba, har a zuciyarta ne.
Zai yi mata abin da take so, tunda ya fahimci ta fi son zama da Habib É—in sama da shi. Bayan tafiyan shi Baffa Kabiru da iyalansa suka É—au hanya, kusan lokaci É—aya suka wuce da Hamma Mustapha.
Zaman da suka ce ma za su yi kafin tafiyarsu abin da ya faru ya sa bai yuyu ba.

Kowa ya yi banza da Umma Salma Mami ce kawai ke shiga wajenta.
Umma Balki ma ta ce abin da ta yi rashin kunya ne.
Su Adda Safina duk sun shiga sun yi mata sallama tana kwance idanuwanta har sun kumbura saboda kuka.
Ba nadamar maganganunta na jiya take yi ba.

Tunanin yau Hanan ta kwana can tare da mutumin da ta yi alƙwarin har abada ba zai kusanci ƴarta ba.

Me ya sa ita ba za a ga damuwarta ba? Ai itama tana da haƙƙi me ya sa ba za a bari a ji ta bakinta ba.
Duniyar ne gabaɗaya ba ta mata daɗi, abinci ma Mami ce ta matsa mata ta karya saboda shan mangunguna amma yadda ta ji rayuwar ma ta fita kanta ba ta ƙi ta mutu ba.

Baƙinciki take ji yadda duk yadda ta sadaukar da zuciyarta ga Hamma Lamiɗo ya kasa fahimtarta.

A wannan halin da ta ke ciki ta É—auka zai fi kowa fahimtarta. Rashi ta yi na uba da jaririnta amma bai damu da wanman ba har yana faÉ—in zai sake ta, shi ne zai kalleta ya ce zai sake ta in ta tuna da kalamansa sai ta ji ba ta ma son ganin shi, tunda dai shi ya kasa fahimtarta to kowa ma in bai fahimceta ba ba za ta damu ba.

Ya sake ta ɗin ai ba mutuwa za ta yi ba. Ita tunda ta rasa uba ma da jaririnta in ta ƙara rasa wani ai ba mutuwa za ta yi ba.

*Janafty*
Received at 11:37Reactions: ❤ 6, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Hanan kuma tunda Shamsiya ta fita da ita take kuka, kuka har da hawaye da majina. A cikin mota ma kukan take yi duk ko da yadda Shamsiya da Gwaggo suke lallashinta ba ta yi shuru ba, su É—in baki ne a gare ta in ta juya ta sake juyawa ta ga ba wanda ta sani sai ta sake fashewa da kuka.

A motar Alhaji Sherif suka zo daman. Su matan suna baya gaba kuma Alhajin na tuƙi Habib da Baba Usman suna mazaunin gaba.

Kukan take yi amma in Gwaggo ta miƙa hannu domin ta ƙarbeta sai taƙi yarda da ita har gwara ma Shamsiyan ta ƙamƙameta amma ba ta daina kuka ba.
Habib ya kasa motsi idanuwansa sun yi jajir ta madubin gaban motan yake kallon Hanan kukanta ma daɗi yake yi masa zuciyarsa ta yi wani irin ɗumi ya rasa yanayin da yake ciki na farinciki ne ko na ɗimaucewa da sanin abin daman hasashe ne da yaƙini kawai amma ba shi da tabbas ɗin Ummu Salma ta haifi wannan cikin.

In ya kalli Hanan sai Fargar jaji ya sake kama shi, lalle da ya zama cikin masu asara da ya yi sanadiyar zubewar cikin nan, da haƙƙin Hanan ba zai taɓa barin shi ya sake rayuwa cikin sukuni ba.

Hajiya Sahura tana ta cewa Ubangiji mai yadda ya so, ashe dai cikin nan sai da ya zo duniya.
Gwaggo na amsa mata da cewa Allah ya ce zai rayu ai bawa bai isa ya hana ba. Habiba na gefe tana ta taɓe baki tana hararan Shamsiya ganin yadda take wani zakewa a zuciyarta ta ce ai daɗin abin ma ba yarta ba ce, takaicinta ɗaya da ya kasance Yaƙinin Habib ya zama gaskiya ta so har abada kar ya samu abin da yake so.

Gidan Gwaggo suka sauka gabaÉ—aya nan Gwaggo ta dinga kiran kannen Habib a waya tana faÉ—a musu su zo gida su ga É—iyar Habib.
An tasa Hanan a gaba ana kallo cikin birgewa da sha'awa ita kuma tana ta kuka. Shamsiya ce ta É—auketa ta goyata da zani tana faman lallashinta.
A ɗakin Gwaggo ana ta mayar da magana Baba Usman na faɗin bai taɓa zaton ahalin Ummu Salma suna da sauƙin kai haka ba.

"Ai mahaifinta dattijon arziƙi ne. Mutumin kirki ne Allah ya yi masa rahama."

Alhaji Sherif ya faɗa sannan ya cigaba da faɗin" Ni da man na san cewa ba za su zubar da cikin ba, Habibu ka ga ikon Allah ko? Ka ƙara gode ma Ubangiji na son ka."

Ya gama faÉ—a yana kallon Habibu da ya sunkuyar da kansa ya kasa magana domin wani farincikin ma ba a iya magana.

"Nima haka na ce, Allah yana son shi da Rahama."

In ji Gwaggo, dukkansu kuma suna mai sake yi ma Habib É—in nasiha da kuma cewa ya lura da rayuwa, ga shi dai yana ganin abubuwan da suka faru

"Ni uwar ce ma ta ba ni tausayi tana ta kuka."

Hajiya Sahura ta faÉ—a domin da gaske Ummu Salma ta ba ta tausayi.

"Nima sai da na yi mata ƙwalla, ga rasuwar uba ga shi kin ji an ce ta haihu ba rai, abubuwan ne suka yi mata yawa, sannan abin ne ya zo a lokaci ɗaya ni kaina ban taɓa tunanin za su kawo maganarka ba, tunda muna zuwa yarinyar ta shigo ko ba a faɗa ba ga kama nan da Habibu, shima kuma ya ki magana tunda yana ganin tunda shi ya ce ba ya so ba shi da ikon tambaya sai ga shi uwar ta ce a ɗauko ma na Hannatun. Sun yi mana karamci Ubangiji suma ya karrama su ranar gobe ƙiyama."

GabaÉ—aya suka amsa adduar Gwaggo da Amin Amin.

"Tunda sun yi mana kara muma mu yi musu, ta yi kwana biyu kowa ya zo ya ganta ku mayar da ita wajen mahaifiyarta "

Alhaji Sherif ya faÉ—a yana kallon Gwaggo ta amsa da in sha Allahu.

"Ai ka ji mahaifiyar Ummu Salman ta ce a can Lagos suke zaune komawa za su yi."

"Can uwar ke aure?

Hajiya Sahura ta tambaya.

"Ina jin can take aure, ai É—an'uwanta take aure yaron sarkin Daura ne."

"ÆŠan Sarki?

Hajiya Sahura ta sake faÉ—a da sigar tambaya.
Chapter 18 · 0% Book details