Sashe 44
Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon kowa kawai take yi a falon cikin jin haushi. Domin ta fahinci ma da wannan bikin ko Ammah ba ta bi ta kanta ba. Kowa ya koma ma Ummu Salma, babban baƙin cikin Bilkisu a ce tana waje amma har tauraruwarta ta dishe sai Ummu Salma kaɗai ake gani, sannan har ana shirye-shiryen fita da ita kasar Cairo ta haihu amma Lamiɗo bai taba faɗa mata ba. Idanuwanta sun cika da ƙwalla ta yi ƙokarin ɓoyewa, ta jima tana fahimtar Lamido ya fi son Ummu Salma a kanta ko daga ganin yadda yarinyar nan ke juya shi, sai abin ta ce shi yake yi.
Wani turiri ne ke tasowa daga ƙasan zuciyanta so take yi ta samu kaɗaici ko za ta yi kuka ta ji sauki.
Received at 08:43Reactions: ⤠7, 😠1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Kamar ta a ce Ummu Salma ta ƙere mata. Ita ta yi nasara ita kuma ta faɗi. Tun tana ƙarama ba ta taɓa yarda wata mace ta fita ba. Nadama take yi nadamar raina Ummu Salma tun farko ga shi ta raina ta, ta zo ta zame mata ciwon ido da damuwa kuncin dake zuciyanta Ummu Salma ce sila domin ta tsani ganinta kusa da mijinta. Jikinta ba in da ba ya rawa saboda damuwa da kishi.
Shi yasa ta tura ma LamiÉ—o sako a waya da cewa tana son ta koma gida ta gaji za ta huta.
Sai ya ce okay, su shirya sai su tafi lokacin Ummu Salma ta shiga ciki. Ta miƙe tana yi ma Sabuwa magana da ta tattara yaran za su tafi.
Daidai Ango na shigowa tare da Saddam ba aboki ko ɗaya Saddam ya ce duk sun koma yau. Ammah ta yi nasiha su Hamma Jibo ma duk sun yi masa nasiha da sake tunasar da shi nauyin da ya hau kansa sai ya yi haƙuri a matsayinsa na namiji kuma shugaba. Lamiɗo ma ya ce yanzu ya zama babban mutum ya yi duk abin da zai yi ya daraja wannan auren da matarshi tare da iyayen shi gabaɗaya.
Ba wanda ya yi masa rakiya ɗakin Amarya sai Saddam dauke da ledojin Kaji da lemuka. Adda Safina na ta cewa Ummu Salma ta fito ta je ta yi siyan baki, ta ƙi fitowa ga gajiya sannan ga sallar mangariba da isha'i a kanta. Tana fitowa wanka ta fara yi sallar mangariba a zaune take yin sallar saboda bayanta ya riƙe kafafunta ma na ta ciwo suna tauna.
Tana zaune bayan ta idar da sallar isha'i ta miƙe kafar kenan ta ji an buɗe ƙofa an shigo ta ɗauka ma Mami ce tana juyawa sai ta ga Gogan ta ne
Ta sakar masa mirmishi ya mayar mata da martani.
"Hamma na."
Ta faɗa cikin shagwaɓa kamar za ta yi kuka tana ware masa hannuwanta daga zaune. Ya tako har gabanta ya duƙa suka rumgume juna.
"Na yi missing É—in Hamma."
"Na yi missing ɗin ƙanwata"
Ya amsa mata kansa na tsakanin wuyanta da kafaÉ—anta, lokaci É—aya hannunsa guda É—aya na saman cikinta yana shafawa.
"How is my girl doing?
"Yau sai tokari na take yi"
Ummu Salma ta amsa masa cikin shagwaba
Tana cigaba da faÉ—a masa bayanta da kafafunta na ta ciwo.
Bai ce komai ba illa sakinta da ya yi ya koma yana matsa mata kafafun yana faÉ—in suna ciwo ne ta ce babu ciwo.
"ÆŠan zirga zirgan da na yi ne kawai fa Hamma."
"To wa ya ce ki yi zirgan zirgan?
Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Kanta ta miƙa masa, ya saka hannu ya cire mata hijabin jikinta. Daga ita sai wata yar shimi rabin cinyoyinta duk a waje ga cikinta da ya yi tsini.
"Hamma bikin BaÉ—É—o ne fa. Dole na yi zirga zirga."
"BaÉ—É—o ta wuce tunanin ka a wajena."
Duk yasan da wannan labarin kamar sake maimaita masa take yi, tana faɗa masa komai na ta Baɗɗo ce akan gaba. Duk abin da ya sameta na farinciki ko na baƙinciki ita ke tare da ita.
Shi dai matsa mata kafafunta yake yi bai yi magana ba. Domin sake tusa masa abin da ya sani kawai take yi.
Ya É—an jima a wajenta yana yi mata maganar ya za a yi da maganar tafiyarsu
Shi yana tunanin za su koma Lagos tare da Bilkisu.
Ita kuma Umma Salma sai ta ce ya bar ta anan sai Visar su ta fito tukunnah.
Ya ce ba ta da matsala za ta iya zama. Bai bar ɗakin ba sai da Bilkisu ta kira shi awaya suna ta jiran shi ta shaƙa ta kusa fashewa daga cewa yana zuwa ya shanya su ta kuma san wajen Umma Salma ya je ya yi zamansa.
Ko da ya fito ya yi ma su Ammah sallama tuni Bilkisu da su Sabuwa suna haraba suna jiran shi a bakin mota.
Bilkisu ta kasa ko da dariya.
Kishin ta ya kasa ɓoyuwa daman kuma ita abin da ke damunta ba ta iya ɓoye shi yana bayyana har a saman fuskarta.
Har suka isa gida ba ta yi magana ba duk da ko Lamiɗon ya yi mata magana ta kalle shi kallon tara saura kwata zuciyanta na zafi ta kauda kai. Tunda ya ga haka sai ya ƙyaleta ba daga Bilkisun har Ummu Salama ba wacce bai san halinta ba ya san halin Ummu Salma ciki da waje ya san kuma halin Bilkisu. Kawai shi dai mutum ne da ba ya son yana takura ma mutane, yana nuna kamar bai san komai ba ne amma babu abin da bai ankara da shi ba.
Received at 08:43Reactions: ⤠8, 🥰 1

Ya san Ummu Salma da Bilkisu ba sa shiri amma tunda ba faɗa suke yi ba no need ya shiga ciki. In dai za su daraja junan su to zaman su a haka bai zama illa a gare shi ba. Ya san Bilkisu tana da zafin kishi ba ta ɓoye kishin Ummu Salma saɓanin ita Umma Salma da ba ta taɓa nuna masa tana kishin Bilkisu ba, kuma ya san tana yi kawai ba ta nunawa ne. Yau ɗin ma abin da ta yi masa ya san kishi ne saboda ya tsaya wajen Ummu Salma. Ba ya son fitina ko kuma shi na shi ran ya ɓaci shi ya sa kawai ya ƙyaleta.
Da suka koma gidan ma ɗakinta ta shige ta rufe ƙofa shima sai bai neme ta.
Duk da ba aiki zai koma wannan satin ba amma yana buƙatar su koma gida ya huta sosai kafin visar su ta fito. Sai dai kafin su tafi zai je Daura. Shi yasa washegari da safe ya bi jirgi zuwa Katsina daga can aka zo aka ɗauke sa zuwa Daura.
Yana zuwa Daura akai akai saboda jikin Mai martaba duk ya sasaabe duk da ba kwantar da shi cutar ta yi ba amma ta jima a jikinsa kafin ta bayyana.
Amma yanzu likitocin dake duba sa a kasar London sun tabbatar da Lever ɗinsa ta taɓu 50% amma tunda ana kan magani akwai yuyuwar ba za ta cigaba ba.
Daman yana ta fargaban kar Mai martaba ya ɗauko masa wancan maganar. Sai kuma aka ci sa'a Mai martaba bai yi masa zencen ba. Sun dai jima suna hira suna tattaunawa game da sha'anin mulki da sarkaƙaƙiyar dake cikin ko wace masarauta.
Fulani ma ta ji sauƙi amma itama suna shiryen shiryen suwa Saudiya itama a can take ganin likita tare da Hajiya Kilishi da Hajiya Zeenatu za su tafi.
Washegari da Safe ya dawo Adamawa. Ya nema musu ticket, a ranar da karfe shidda na yamma suka koma Lagos shi da Bilkisu da yaran gabaÉ—aya.
Sun zo gida sun yi ma su Ammah sallama Bilkisu ta yi kamar ta yi bindiga lokacin da Ummu Salma ta yi musu rakiya har tana riƙe hannun Lamiɗo kuma bai hana ta ba.
A masu rakiyar har da Amarya BaÉ—É—o Hamma Abdullahi ne ya kai su filin jirgi washegari suma su Hamma Jibo duk suka koma garuruwansu da ilyalansu gida ya rage daga Ammah sai Ummu Salma da Mami, Umma Balki da Umma A'i ma sun koma Mubi
Sai Amarya BaÉ—É—o da angonta sai Hamma Saddam.
Amarya da ango suna ta cin amarcin su. Suna bangarensu amma ko wani safiya BaÉ—É—o za ta shigo ta gaishe da Ammah da Mami ba ta fara girki ba Adda Suwaiba na aiko mata da abinci. Haka ma Adda Ummu Suleim nan gida kuma Harira tare da Barira suke girkawa wani zubin kuma Mami ko Islam tunda ta iya girkin itama.
Sai Ummu Salma da kan shiga wajen BaÉ—É—o in Abdulrahim na bangaren Ammah su sha hira.
Washegari Daddy ya zo, bai samu zuwa ɗaurin auren ba domin ba ya ƙasar. Bai kwana ba a ranar ya koma tare da Islam da Faruk
Barira kuma za ta zauna tare da Ammah kafin su Mamin su dawo daga Cairo.
*
LAGOS.
BAYAN KWANA HUÆŠU.
Tunda suka dawo Bilkisu ta canza masa. Ba ta sakin masa fuska, ba ta zama da shi ko a dinning suka zauna cin abinci haka za su zauna su ta shi amma ba wani hira ko sakin jiki ya fahimci tun suna Adamawa ne ta canza masa. Ba ta kwana a bangaren shi ya ɗauka tana buƙatar lokaci ne sai da aka kwana huɗu sai ya fahimci sai sun zauna sun yi magana wata kila akwai rashin fahimta. Shi ya sa ya yanke shawaran zai yi magana da ita domin su fahimci juna.
Ba ta nan ta je asibiti, ya yi niyar cewa zai faÉ—a mata har maganar tafiyar su Egypt to da yamma ma kafin ta dawo ma aka tura masa sako Visar su ta yi ready, za su tashi nan da kwana uku. Tunda kamfanin da ya nemi Visa package ne gabaÉ—aya har da kuÉ—in jirgi da komai da komai.
Ya tura ma Ummu Salma saƙo tunda ya kira ta bai same ta a waya ba. Ya kamata zuwa gobe su taho Lagos tunda ta nan jirgin su zai ta shi. Ya samu Mami a waya sun daɗe suna tattaunawa. Sun rabu da cewa zai neme musu Ticket gobe su taho Lagos jibi sai wuce gabaɗaya.