← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 75

Sashe 34

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya sake tambaya yana mai ƙureta da idanuwansa.
Yana jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa? Me ya sa ba a faɗa masa ba? Kuma dalilin da ya sa ya ke turo Abdullahi kenan amma sai ya ba shi tabbacin lafiyanta lau, me ya sa ta rame? Gabaɗaya ta sauya masa ta yi baƙi kamar ba Ummu Salama ba.

"I'm asking you. Ba ki da lafiya ne?

Ya sake maimata tambayar wannan karon muryansa ta É—an buÉ—e.
Ba ta so hawayen da suka kawo mata su zubo, hancinta kuma ya gaji da shaƙar iskar ƙamshin turarensa zuciyanta na yunƙurin amai kawai sai ta juya baya daidai lokacin da hawayen suka taho mata.

"Lafiya ta ƙalau Hamma."

Ta amsa shi da raunin murya kafin ta kwashi sauri tana mai rufe baki zuwa É—akinta amai ne ya taho mata take saurin isa tiolet kafin ta sake shi anan shi kuma tunanin shi ko ta gudu ne sai ya taka ya bi bayanta. Yau ba gudu ba duk wani rashin fahimta dake tsakaninsu za su warware shi.

Yana shiga ɗakinta ya ji ƙakarin amai a tiolet da sauri ya ajiye rigar hannun shi a saman gado ya buɗe ƙofar tiolet ya shiga tana durjushe a tiolet ɗin tana ta kwarara amai duk tuwon da ta ci ne shi ne take amayarwa daman ya sani ba ta da lafiya yana ganinta ya fahimci haka kamar ba jini a jikinta.

Bai damu da kar ta ɓata shi ba, bai damu da warin amai ba, haka ya shiga tiolet ɗin ya riƙeta lokaci ɗaya yana rankwafawa yana yi mata sannu.
Received at 17:28
8 people reacted with ❤
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta ba shi tausayi yadda take amai, kamar hanjin cikinta zai zazzage daga ƙarshe ma sai ruwa kawai ke fitowa, shi bai san shi ne ciwon ta ba ƙamshin jikinsa da take shaƙa shi ke ƙara saka mata hararwa ta rasa kuma yadda za ta yi masa bayani ya fahimta.

Jikinta sai rawa yake yi, tana mayar da numfashi sama sama in ta yunƙura ta yi aman ba ya zuwa sai wahala take sha, shi kuma yana ta faman yi mata sannu.

Ta jingina da bango tana mayar da numfashi.

"Sannu."

Ya faÉ—a yanan mikewa tsaye.

"Ki tashi ki wanke jikin ki, mu je asibiti."

Ta kalleshi hawaye suka kece mata a saman fuskarta.

"Hamma."

Ta kira shi cikin raunin murya.

"Na'am."

Ya amsa yana kiran nata na ratsa duka jikinsa da zuciyarsa

"Ciwo na yanzu ba shi da magani."

Ta faɗa tana yi masa mirmishi. Ji take yi kamar za ta yi amai amma ba komai a cikinta ba ta son ƙamshin nan tana so ta ce ya fita ta kasa.

"What? Akwai ciwon da ba shi da magani ne?

"Akwai."

Sai kawai ya zura mata idanuwana yana kallonta kirjinsa na duka, ta ga fargaba da tsoro a kallon da yake yi mata.

"Hamma."

Ta sauke numfashi.

"Ka je waje, zan yi wanka ne."

Ta gama faɗa tana yunƙurawa kamar wani aman zai fito amma kuma babu komai.
Ya kalleta sai ta gyaÉ—a masa kai shi kuma sai ya fara nannaÉ—e hannun rigan shi wai zai taimaka mata ta gyara jikinta.

"Aa."

"Zan iya da kaina."

Ganin kamar ba ta so sai ya ƙyaleta ya fito ya janyo mata kofa, yana fita ta rarrafa ta yi floshing ɗin aman da ta yi ya wuce rigar jikinta ma duk ta ɓaci da amai cire kayan da ta yi ta watsa ma jikinta ruwan sanyi.

Ta fito ɗaure da towel har lokacin yana ɗakin zaune bakin gado yana jiranta. Bedroom din na ta ma ya gauraye da ƙamshin sa

Da hanzari ya taso ya nufe ta, sai ta yi baya da sauri tana toshe hanci wallahi kamar za ta mutu haka take ji shi kuma mamaki ya sa kawai ya tsaya yana kallonta ya kasa magana.

Dube-dube take yi ina ta baro ƙasanta shi kawai za ta shaka ta zauna lafiya. Sai ta tuna yana falo da gudu ta fita shima sai ya bi bayanta yana tunanin ko bayan baya nan aljanu sun shafeta ne

Ya tsaya kawai yana kallonta ganin ta ɗauko gwangwanin madara ta buɗe ta kafa kai tana shaƙa har wani lumshe idanuwa take yi. Ya ɗauka ma madaran ne a ciki take so ta sha har hankalinsa ya kwanta amma sai ya lura koma mene shaƙan shi take yi ba sha za ta yi ba

Ita ba ma ta shi take yi ba shakan ƙamshin ƙasan take yi kamar da zuciyarta. Har wani daɗi daɗi take ji.
Harira ce ta fito daga kitchen sai ta yi kiciɓis da Yarima ta yi ƙasa da sauri tana yi masa sannu da zuwa

Ya juya ya kalleta sau É—aya ya amsa.
Ya koma ya kalli Ummu Salama ya fara tunanin akwai abin da ke faruwa da ita wanda shi bai sani ba.

Kamar zai tambayi Harira sai kuma ya fasa itama ta tashi ta koma kitchen ƙarisawa ya yi kusa da Ummu Salma ba ta ma sani sai ganin kan shi kawai ta yi ya leka gwangwanin hannun ta.

"Ƙasa.?

Ya faɗa a saman leɓen shi cikin mamaki. Ita kuma matsowan shi kusa da ita yasa ta yi tsalle ta koma gefe har towel ɗin jikinta na neman faɗuwa ta tare shi da hannu ɗaya.

"Hamma."

"Ka tsaya anan"

Idanuwansa a kanta innalillahi tabbas wani abu ya same ta wanda bai sani ba. Me ta ke yi da ƙasa kuma? Ko Depression ne ya kamata ko wani cuta a ƙwakwalwarta amma in ba haka ba me ya sa za ta yi ta shinshinar ƙasa sannan ta hana shi ya matso kusa da ita.

Tausayin ta ya lulluɓeta koma mene ne ya faru duk shi ne sila da ace tana tare da shi da ba ta samu wannan laluran ba.
Ya yi tsaye kawai yana ganin ta tana ta shinshinar ƙasa.

"Me kike yi haka?

"Kasa ne fa"

Ya faɗa muryansa na yin ƙasa.

"Ina so ne."

Ta amsa mishi, sannan ta kalle shi tana yi masa mirmishi.

"Come here."

Ya faÉ—a yana ya fito ta da hannunsa guda É—aya.

"Hamma."

"Ƙamshin turarankaa ne ke saka ni amai da tashin zuciya."

Ya sake yin sakayau kawai yana kallonta.
Ya kasa gane abin da ke faruwa.

"Meke damun ki?

"Ciki gare ni."

Ta ba shi amsa kai tsaye sannan ta bi ta bayan kujera ta wuce.

"Ka jira ni anan."
Received at 17:28
15 people reacted with ❤
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ba ta so ya biyo ta É—akin, kamar daman umarninta yake bi ya yi tsaye yana kallonta har ta shige É—akin, shi ba ma wannan ba sai ya ji kamar da ya tambayeta abin da ke damunta ta ce ciki gare ta amma sai wata zuciyar ke tunanin bai ji daidai ba ne

Yana nan tsaye ta fito É—auke da wata farar takarda a ninke ta zo ta ajiye a saman kujera.

"Hamma ka yi hakuri ka duba wannan sai mu yi magana."

Tana gama faɗin haka ta koma ɗaki sai da ta bubbuɗe window amma duk da haka ƙamshin na nan Allah yasa ga kasarta a gefe tana ta shaƙa shi ne ya saukaka mata.

Shi ko takardan ya ƙarisa ya ɗauka tsoro har ya bayyana a saman fuskar shi.
Yana buÉ—ewa ya bi rubutun dake ciki daki daki kafin ya gama karantawa ya ji hannunsa na rawa

Ummu Salama tana da ciki, ashe abin da ya ji ta faɗa gaskiya ne. Date ɗin ya duba tun tafiyar shi ne ba daɗewa. Ko bai yi lissafi ba ya san ranar da suka samu matsalan nan ne ashe akwai rabo mai nauyi a tsakaninsu idanuwansa suka ƙankance da hanzari ya shiga ɗakin nata har ta saka kaya doguwar rigar Abaya.

"Why?
Ta juya tana kallon shi.

"Me ya sa ba ki faÉ—a mini ba?

"Ba wanda ya faÉ—a mini kina da ciki Umma Salama."

Ya gama faÉ—a kamar zai yi kuka. Ba ta yi tsammani ba kawai sai ganin shi ta yi a gabanta tana kallon shi da idanuwanta masu ruwan hawaye.

"A ina zan faÉ—a maka?

"Ka rufe ni ko na kira ka bana samun ka."

Ta gama faÉ—a hawayen na kece mata da kuka.
Sai kawai ya rumgumota a cikin jikinsa ƙamƙam tare da takardan a hannunsa kamar tana jira ta saki kukanta mai sauti wannan kukan da kewar wattani biyun da ba ta samu kafaɗan da za ta yi kuka ba, yau shi take yi duk da ƙamshin turaransa na tsinke mata zuciya ba ta damu ba, tana bukatar kafaɗan da za ta yi kuka a lallasheta.

"Hamma.."

"Ka yi hakuri."

"Shii."

Ya faɗa yana ɗan bubbuga bayanta alaman lallashi ita kuma tana ƙara shigewa jikinsa tana rirrikeshi lokaci ɗaya tana kuka.

"Na yi kewarka, na yi kukan rashin ka."

"Wallahi na yi nadaman kalaman da na faÉ—a maka tun a ranar."

"Na yi nadama."

Take faÉ—a tana gunjin kuka.

"Is Ok."

"I'm Sorry."

"Na barki ke kaɗai. Am sorry bana tare dake a lokacin da kike buƙata ta."

"I'm Sorry Ummu Salama. I'm sorry."

Shima yake faɗa kamar ya yi kukan haka yake ji, Ummu Salma ta yi ta kuka kukan dake fitowa daga ƙarkashin zuciyanta bai hanata ba ya barta ta yi kukanta har sai kukan ya dawo shessheƙa.

Ya É—ago fuskarta yana share mata hawaye da gefen hannun rigansa.

"I'm sorry."

Ya sake faɗa, ta ƙamƙame hannuwan shi.

"Hamma."

"Yes"

"Ka yafe mini."

"Komai ya wuce Umma Salama."

"Ka yafe mini?

"Na daÉ—e da yafe miki."

Ya faÉ—a yana kallon cikin idanuwanta. Wasu hawayen suka sake kece mata.

"Shi ne ba ka nemi ni ba! Ba kira ni ba?

"Am sorry."

"Im here ba zan sake tafiya na bar ki ba."

"Ka tabbata?

"Na tabbata."

Sai ta fara mirmishi tana hawaye, yana share mata.

"I miss you. I miss everthing about you expecially wannan craying face É—in na ki."

Ya gama faÉ—a yana jan hancinta amai ta ji ya taso
mata sai ta bar jikinsa ta rarumi gwangwaninta tana shakan ƙamshin ƙasan ta.

"Warin turare na ne ba ki so?

Ya tambaya cikin kulawa.
Sai ta É—aga masa kai

"To bari na yi wanka ko na sauya kayan ne?
Chapter 34 · 0% Book details