← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 75

Sashe 40

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A falon Ammah aka tattaru kaf yaran Baffa mazan da cikon su Ummu Salma.
Sai Baffa Umaru da Baffa Salihu wakilan Baffa sai wakilan Ammah kuma Umma A'i da Umma Balki.

An buÉ—e taro da addu'a tare da nema ma Baffa gafara a wajen Allah sannan aka fara gudanar da abin da ya tara su. An fito takardun filayen da Baffa ya bari da na gida. Sannan daman lokacin da ya rasu Hamma Abdullahi ya ce ba a bin shi ba shi sai ma shi ne ke bin wasu, to duk sun dawo da kuÉ—in tunda shi ne suke kasuwanci da Baffa ya samu tattara kudaÉ—en da ya mutu ya rabi kudaÉ—e dai tsaba miliyan takwas ne sai gidan nan da suke ciki sai filaye guda huÉ—u sai mota sai kuma gadon shi dake can mubi na gida da gona.

An raba gadon cikin tsarin kamar yadda Ubangiji ya raba gado a cikin suratul Nisa'i. A shari'a namiji ke da kaso biyu mace kuma na da kaso rabi daga abin da namiji ya samu.

Matar da mamaci ya mutu ya bari tana da kashi É—aya a cikin takwas. Tunda yana da yara maza, yan'uwansa maza ba su shigo gadon Baffa ba. Daga ya'yansa sai matarshi da a ce mahaifiyar Baffa na raye za ta shigo ciki a matsayin É—aya bisa shidda amma tunda ta riga Baffa rasuwa babu lissafin ta a rabon gado.

Gida kuma tare aka raba kowa da kowa har da Ummu Salma kuÉ—i ma aka yi kasafi aka raba komai kamar yadda addini ya tsara.
Ana rabon Ummu Salma na sharan ƙwalla, shike nan Baffa ya rasu da gaske ne ba mafarki ba. Kowa ka gani jikinsa duk a sanyaye.
Shike nan fa an yi an gama. Sai dai fatan Ubangiji ya sa mu gama da duniya lafiya.

Sai gidan ya dawo kamar yau aka yi mutuwa. Ammah ta yi kuka irin wanda ko a lokacin rasuwar ba ta yi ba. Hamma LamiÉ—o ne ke ta lallashinta Mami ma kuka har da sauti Liman ya zauna yana ta nasiha tare da ba ma su Hamma Jibo shawaran su haÉ—a kansu ko bayan ran Baffa su kasance Æ´aÆ´a nagari a gare shi. Hamma Abdullahi sai share hawaye yake yi shi da su Hamma Saddam.

Mutuwar Baffa babban gibi ce da har abada ba za su taɓa mantawa da shi ba. Bayan an gama koke koken kowa ya share hawayensa.
Bayan Liman ya tafi su Hamma Jibo sun je sun raka shi sun dawo.

Sai aka sake wani zaman saboda tunanin wanda za a samu da zai zauna da Ammah saboda ɗebe kewa. Ammah kuma na faɗin ita su ƙyaleta za ta iya zama ita kaɗai. Umma Balki ta ce ba zai yuyu ba ko yaya ne a samu wacce za ta taya ta zama.
Received at 08:42Reactions: ❤ 11, 👎 2
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ita Ammah na faÉ—in ba matsala ga Ummin ikki a kusa da ita ga matan su Hamma Abdullahi suna zuwa akai akai ba ta da matsala. Umma Balki ta ce Umma A'i ya kamata ta É—an zauna na wani lokaci saboda ita ce ba ta da kowa a gabanta. Ta amince za ta kara ko da wata É—aya ne kafin ta koma.

Hamma Jibo ya ce shawara kawai cikin Saddam ko Abdulrahim wani ya zo ya yi aure.
A gyara gida ya saka matar shi a kusa da Ammah. Kowa kuma ya aminta da shawaransa.

"Ni fa ba yanzu zan yi aure ba, ban kama aiki mai girma ba sannan ina karatu."

Hamma Saddam ya yi saurin faÉ—a.

"Kuma ni ai ƙarami ne Abdurahim ne ya dace ya yi aure, kuma shi ai ya gama karatu har ya kama aiki."

"Kuma yana gaba da ni."

Ya faÉ—a har yana marairaicwa.
Umma Balki ta ce ai ya isa auren shima

"Umma Balki ban isa aure ba fa."

Tana cewa ya isa yana cewa bai isa ba diramansu ta ba ma kowa dariya.

"Ai na ce ka turo mini CV É—inka zan tura ma Maimartaba za ka fara aiki in sha Allahu "

LamiÉ—o ya faÉ—a yana kallon Saddam nan da nan ya washe baki ya ce ya sha'afa ne amma zai tura maasa daman ko aikin Abdulrahim daga Masarautar Daura aka samar masa.

Abdulrahim da aka tuntuɓe shi ko yana da budurwa karaf Ummu Salma ta ce yana da shi.

"A Abuja take anguwar su Hamma Jibo "

"Tabbas haka ne, suna ma raba dare suna waya a kwanaki can amma yanzu na ga kamar ba sa waya."

Hamma Saddam ya karɓe maganar.
Abdulrahim na ta hararan shi.

"To kai Abdulrahim ya ake ciki ne?

Hamma Mustpha ya tambaye shi yana dariya.

"Ko an ka sa ka ne?

Hamma Abdulrahaman ya faÉ—a yana dariya.

"Kamar ka sani, ba ni da kuÉ—i ta bar ni ta auri wani mai kuÉ—i bayan rasuwar Baffa ta yi aure."

"Subhanallah."

"Abu bai yi daÉ—i ba."

"Sannu Allah ya mayar kaffara ne"

Har da Hamma Kabiru a masu yi masa jaje.
Mami na yi masa tsiyan ko bai iya soyayya ba ne ya ce ya iya mana ana ta dariya.
Ammah na mirmishi kafin ta ce" Ita ce ta tafka asara ka ji, yanzu dai ka yi haƙuri ka zo ina da matar da zan ba ka kuma na san za ka ji daɗin ta."

Kowa ya zura mata ido yana jiran ya ji sunan da za ta kira. Umma Salma ta yi jagale daman tunda ta ji Abdurahim ya ce budurwansa ta yi aure take wani tunani.
Sai kuma ga maganar Ammah.

"Wace ce?

Abdulrahim ya tambaya yana addu'an Allah ya sa ba a ƙauye ba ne.

"Aisha ce."

"Aisha?

Kusan duk falon suka tambaya a tare.

"Aisha yar wajen Aminiya."

"BaÉ—É—o tawa?

Ummu Salma ta faÉ—a tana zaro idanuwa har tana dafa kafafun Hamma LamiÉ—o domin tana kusa da wajen kafafunsa ne a zaune

"Ita, ni da mahaifiyarta aminai ne, ka je ka neme ta in kun daidaita ina maraba in kuma ba ku daidaita ba, ba tilastawa."

"Gaskiya tana da hankali Aisha."

Saddam ya faÉ—a yana dariya. Abdulrahim ya ture shi da kafar shi ya koma gefe yana dariya.
Hamma Abdullahi ya ce shi ya É—auka ma soyayya suke yi da Saddam

"A'a ni wallahi ba soyayya muke yi ba. Ni fa bana son farar mace."

Ya faÉ—a da iya gaskiyarsa

"Ka yi mata yaro da yawa ma."

Ummu Salma ta shigar ma ƙawarta tana hararan shi.

"Ke ni ne yaron?

"Yaro ne mana ai gwara Hamma Abbdulrahim muma kai ba ajin mu ba ne "

Ya taso yana jijiyar wuya ana ta dariya.

"Ammah kamar kin shiga zuciyata. Ina ta so BaÉ—É—o ta samu miji cikin yayyena ni da har Hamma Abdulrrahaman na yi ma sha'awarta ma"

Da ya ballo mata wata harara sai da ta sunne kanta kafafun mijinta tana dariya.
Mami ta ce ai ta samu mijinta Abulrahim ƙin kowa ƙin wanda ya rasa shi dai ya yi shuru ya kasa magana kowa na tofa albarkashin bakin shi. Su Hamma Jibo duk sun ce zaɓin Ammah ya yi har da su Baffa Umaru ma.

Umma Balki ta ce da tana da yar auta mace da ta ba ma Saddam yana tura baki ya ce ba ya so

"Kai ka sani irin su Saddam ne, in ka ga matansu sai ka juya baya ka ɗauka yan aikin su ne saboda shigen zaɓe zaɓe."

Aka saka dariya gabaÉ—aya shi kuma yana kumfar bakin cewa za a ga matar da zai aura kaf surukan Ammah ba kamarta.

"Ba kamarta kam."

Hamma Abdullahi ya faÉ—a yana dariya Saddam ya kasa magana.

"Hamma wallahi ka amsa za ka ji daÉ—in Aisha sosai tana da kunya ga hankali ga natsuwa."

"Uhm kina yi ma ƙawarki yaki ne?
Received at 08:42Reactions: ❤ 7, 😁 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Hamma Abdullahi ya faɗa Ummu Salma ta fara dariya tana faɗin ba yaƙi ne ba ne sai gaskiya Hamma Lamiɗo ta kalla tana faɗin bai ce komai ba.

"Me zan ce?

"Ka faÉ—a ma Hamma Abdulrahim sa'ar da ya yi na samun Aisha a matsayin matarsa."

Ya yi shuru bai yi magana ba yana kallonta.
Sai ta marairaice fuska kamar za ta yi masa kuka.

"Hamma ka yi magana mana."

Har tana rumgume kafafunsa ta manta ma a inda suke ta É—auka suna gidansu ne shi kuma da sauri kamar jani talau ya ce to sannan ya juya yana kallon Abdulrahim da duk aka saki baki ana kallon su.

"Abdulrahin ka ji ko? Aisha is a good girl ka yi abin da Ammah ta ce kawai.'

"Ko abin da Ummu Salma ta ce ba."

In ji Hamma Kabiru yana kallon shi
Aka kwashe da dariya a falon har Ammah sai da ta murmusa sai a lokacin da Ummu Salma ta san abinds ta yi da sauri ta saki kafafun Hamma LamiÉ—o ta koma tana sunne kai a jikin Mami.

"ÆŠan Ammah dai ya shiga hannu "

Mami ta faÉ—a tana dariya.

"Ai ya zama jani talau kuma laifin Fatima ne."

Umma Balki ta faÉ—a tana dariya. Haka ma Hamma Jibo ya ce nan duk ana magana bai saka baki ba amma Auta na marairaicewa ya bi umarninta yana jin su kawai mirmishi yake yi bai yi magana ba.

"Amini ai ya canza sosai ni yanzu ma ina tsoron yin hira da shi kar ya kwashe ya faÉ—a ma yarinyar nan ta dinga mini kallon biri ni kuma ina yi mata na ayaba."

"Wallahi ka kiyaye "

In ji Hamma Abdulrrahaman
Falon sai dariya ake yi shi kuma gogan bai yi magana ba illa Hamma Kabiru da ya kalla ya ce.

"Bana faÉ—a mata komai fa."

"Ban yarda da kai ba."

"Wallahi Hamma ba ya faÉ—a mini hiran ku, hiran mu kawai muke yi ko Hamma? "

Ummu Salma tana kallon Hamma Lamiɗo har tana yi masa fari da gaske ne ba ta sanin komai kai in dai wajen zurfin ciki ne da riƙe magana ba ta ga kamar Hamma Lamiɗo ba.

"Tell him."

LamiÉ—o ya faÉ—a yana kallon Hamma Kabiru.

"Kai dai ka kiyaye kawai tsakanin miji da mata.."

Su Hamma Abdullahi suka ƙarisa da sai Allah ana ta dariya.
Chapter 40 · 0% Book details