← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 75

Sashe 30

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kyaleta da damuwar dake damunta. Ga kewar miji ga kewar Baffa. Tana da tabbacin rashin Baffa sai an daɗe kafin ya zame mata jiki gani take yi kamar Baffa zai dawo ta kasa gasgata mutuwarsa, gani take yi kamar zai dawo wata yar tafiya ya yi. Duk da babu abin da ta nema ta rasa kayan abinci ne ga su nan tsibiri guda a store sai kuma cefane duk wata Hamma Abdullahi zai kawo, su kifi su nama duk da ba ta ci sai dai Harira ta ci ko ta saka ta soya ko ta yi ferfesu ta kai ma su Ammah, wacce yanzu karɓa karba suke yi Umma Balki ta koma yanzu Umma A'i ke zaune da ita, suma ɗin babu abin da ba su da shi naman ne kifin ne sai abin da suka ga dama za su ci.

Kuɗi kuma tun wanda Hamma Lamiɗo ya bar mata da zai tafi ko rabi ba ta taɓa ba, sai in Harira za ta je kasuwa ta ba ta sakon kayan marmari da su aya da goriba tana cin su, a asibiti ma likita ya ce ta yawaita shan kayan marmari saboda za su ƙara mata kuzari wani lokacin ta sha ta zauna lafiya wani lokacin kuma ta yini tana amai sai dai godiya kawai.

Kewar mijinta har ya bayyana a idanuwanta da jikinta daurewa kawai take yi. Amma tana buƙatarsa ga shi ya yi mata nisa amma tana ji a jikinta nisan na ɗan lokaci ne koma mene ne ya kusa dawowa zuwa gare ta. Za ta duƙa har kasa ta ba shi hakurin laifinta kuma bakinta ya yi limzami har abada ba za ta ƙara gangancin furta irin waɗanan kalaman ba, ta yi ganganci ta yi kuskure ta yi kuma nadama tun a lokacin sai dai kuma nadamar ne mara amfani.

*
LAGOS.
MARINE ROAD.
THURSDAY, 12:00PM.

Barcin sa ya yi nisa, hasken da ya dinga kashe masa idanuwa shi ya farkar da shi daga nannauyan barcin da ya kwashe shi tun bayan dawowarsa salla asuba.

Kare fuskar shi ya yi da hannun daman shi yana É—an yamutsa fuska.
Dariyan ta ya ji, daman ya san ita ce.

"Ranka ya daÉ—e pass 12, ka tashi ka yi wanka mu yi breakfast."

Lumsssun idanuwansa da suka shige ciki saboda barci ya buÉ—e yana É—an muskutawa sannan ya É—an tashi zaune yana jinginar da kansa jikin masagalin gadon da yake kwance. Sannan lokaci É—aya yana yaye bargon dake jikinsa.

Sanye yake da dogon wando baƙi, amma wandon bai rufe masagalin kafafunsa ba, ana iya ganin ƙaurin kafafunsa ga ƙananun gargasa nan kwance luf a zararan dogayen ƙafafunsa.

"Yara suna ta jiran ka, suma yau tare da Papa za su yi breakfast"

Bilkisu ta sake faÉ—a lokaci É—aya tana zama a gefen shi.
Ta ci kwalliya cikin ado mai burgewa na riga da wando yan kanti ta naÉ—a wani mayafi mai santsi a saman kanta.

In da ta buÉ—e labulen ya kalla rana ta fito sosai, wajen wani glass ne wanda in ka fita za ka samu wajen shan iska ga kujeru a wajen.

"Good morning Papa."
Received at 07:54Reactions: ❤ 6, 🥰 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta faÉ—a lokaci É—aya tana rumgume shi.
Shima sai ya É—an rumgumota yana amsawa.

"How was your night?

"Am fine."

Ta amsa shi tana masa mirmishi, goshinta ya sumbata ita kuma sai ta sumbaci leɓen shi suna kallon juna cikin mirmishi.
Wanka ya ce zai yi, suka miƙe a tare tana jikinsa tana faɗa masa ta yi kewarsa sosai.

"I'm with you."

Ya amsa mata lokaci É—aya yana sake sumbatar gefen kumatun ta.
Tambayata yake yi yau ba za ta je asibiti ne ta ce za ta je sai after 1 za ta fita

Sakin ta yi ya wuce tiolet ta bi shi da kallo kamar ta kamo shi ta lashe shi da gaske ta yi kewar sosai. Jiya da yamma ya dawo a gajiye yake shi ya sa daga ita har yaran bai wani zauna da su ba da wuri ma ya kwanta a bangaren shi ita kuma sai ta bar shi ya huta ta koma bangaren ta, ta kwana da safe ma daya ya dawo masallaci barcin ya koma.

Yanzu ma ganin sha biyu ta gota shi ya sa ta zo ta she shi. Ta san in har aka yi azahar zai yi mata faÉ—an me ya sa ba ta tashe shi ba. Lamido zai iya asaran komai bai damu ba amma ban da asaran salla a cikin jam'i.

Bargon ta É—an janye tana gyaran gadon, baya so su Hidaya na shigar masa bangaren shi tun suna ma wancan gida ba wannan ba. Shi yasa in dai yana nan za ta É—an gyara amma fa in baya nan Hidayar ke gyarawa ba za ta iya ba.
Bayan ta É—an ninke bargo ta ajiyesa a gefen gado ita ta koma ta zauna wayarsa dake saman side drower ta É—auka wayarsa babu tsaro shi ya sa ta samu damar duba abin da take nema.

Kwata'kwata babu sunan Umma Salma a call long ɗin shi. Ta duba bangaren sakonni ba ta ga wani sabon sako ba tun wanda ta gani ne wancan dawowar da ya yi ne anan ne ta tabbatar da zarginta wani laifi ne mai girma Ummu Salma ta aikata masa, zuciyarta ta yi mata tsalle lokacin da ta ga saƙon Ummu Salma na ya sake ta ranar dakyar ta iya barci saboda farinciki ta fara zargin ya yi sakin amma ba tare da kowa ya sani ba ko kuma an sani an rufe maganar ne saboda ba al'adar gidan Sarauta ba ne sakin mata.

Tun wancan dawowar ta bincike wayar nan tas, nan ta gano rikita shin Umma Salma ke yi a baya da hotuna da videos tare da chart na kalaman soyayya ai dole ya rikice akanta amma ta duba date wajen wata biyu kenan ba su ƙara magana da juna ba, ba waya ba saƙo kenan zarginta ya zama gaskiya.

Saurin ijiye masa wayar ta yi tana ɗan yarfa hannuwanta sama alamun murna, Allah ya ga zuciyarta ya kawo mata masalaha a cikin sauƙi, duk a wancan dawowar na shi ma ta yi ta dukan ruwan ciknsa ta ji wani magana game da Umma Salman bai faɗa mata ba daman ta san ba zai taɓa faɗa ba.

Miƙewa ta yi, tana juyi a cikin bedroom ɗinsa mai kama da ɗakin turawa komai cikn tsari. Wannan gidan ya fi wancan girma sai biyu ma.

Ga dai shashen Umma Salma can a rufe amma ba za ta dawo mata gida ba. Tunda suka dawo ta yi sallama da damuwa da tashin hankali ta mayar da jikinta kamar ba ita ba. Ganin Umma Salma kawai a gidan ta, tana giftawa barazana ne ga zaman lafiyanta amma yanzu ita shar, Hanan ce kawai ta rage kuma Ya Hadiza ta ce ta ƙyaleta kawai me yarinya ta sani? Ba ma haka ba Lamiɗo ba zai taɓa yarda ya mayar da Hanan ba duk da a surutun yarinyar ta ji tana faɗin Abba da Anty sai ta yi tunanin wataƙila yarinyar ta haɗu da ubanta na gaskiya ne sai ta kira Ammah daman tana kiran ta bayan ko wani kwana biyu suna gaisawa shi ne ta ɗan kawo mata zencen Hanan ɗin nan ko Ammah ta kwashe komai ta faɗa mata amma ba ta faɗa mata hatsaniyar da Umma Salma ta yi ba nan ta tabbatar da wataƙila nan gaba kaɗan Hanan ɗin ma za ta bar mata gidanta da mijinta da yaranta ta koma gidan su. Saboda son jin kwaf irin na Bilkisu har tambayan Ammah take yi ya wajen su Ummu Salma? Sai Ammah ta ce suna lafiya lau da yake Ammah na da kunyar fulani, ba ta faɗa mata zencen cikin Umma Salma ba, ballatana ta ji labarin cikin sai kawai ta cigaba da zama cikin yaƙinin ta cewa Lamiɗo ya saki Umma Salma ba, ko a can Masarauta Ya Hadiza ta ce ba ta ji wani labari ba kenan suna ɓoyewa ne aamma duka alamomin sun tabbatar da wani abu ya faru.
Received at 07:54Reactions: ❤ 6, 👍 1, 🤗 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Duk da ta fahimci su Sultan sun shaƙu da Hanan ɗin ba ma su har Lamiɗon da su Hidaya kowa Hanan saboda kazar kazar ɗinta kuma zamanta a tare da Beena ya sake saka ma Beena himma sosai, ba ita ke kula da yaran ba amma dai tana duba su lokaci bayan lokaci ta fahimci Hanan tana da ƙokari kuma sannan bayan dawowarsu an yi Parents day ta je musu anan ne headteacher ɗin su Hanan ta ke cewa yarinyar na da ƙokari suna tunanin yi mata jumping zuwa nursery 2 ajin su Beena ta ce a barta a in da take ba ta so daga zuwan yarinya ta zo ta fi yaranta ƙokari shi ya sa ta faɗa ma Anitha ta dake ma da Beena ta daina wasa da karatu ba ta son a fita sannan ba ta son a fi yaranta gwara ma Sultan shi ba ta jinsa. Amma Hanan irin masu kaifin kwaƙwalwar nan ne sau daya za a yi mata karatu ta ɗauke shi ko a Qur'ani duk ta iya ƙananun surorin nan ga shi ta iya salla ta iya azkar ta ce Mami ta koya mata daman ai Mami ba ta da wasa.

Har Safina matar Kabiru Bilkisu ta kira ta ji ko da gasken LamiÉ—o ya saki Umma Salma amma ba ta ji wata magana ba. Ba saba waya suka yi ba shiya sa suna gama gaisawa da tambayan yara suka yi shuru Bilkisu kuma ego É—in ta ya hana ta tambaya dole suka yi sallama.
Murna kawai take yi farinciki ya cikata.

Tana nan tsaye har ya fito daga tiolet sanye da rigar wanka.
Ta juya tana kallon shi cikin wani shauƙi, Ummu Salma ta zo ta yi mata aiki kuma ta tafi ta bar mata mijinta da gidanta. Ta yi mata aikin dawo da Lamiɗo irin yadda take so, Lamiɗon da ba zai sanya wani hijabi a tsakaninsu ba.
Chapter 30 · 0% Book details