Sashe 33
Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Harira ta sanyo hijabinta ta fita Ummu Salma na cewa ta yi sauri karma ta shiga gida ta ce to.
Ta bar Umma Salma ita kaɗai TV na ɓaɓatun shi.
Fitan Harira ko minti talatin ba ta yi ba sai gata ta dawo, ta ce ta manta ba ta ɗau leda ba tunda suna da ledojin na cefanen da ake kawo musu, a hanya ta tsaya ta siya bakko ta kusa yin rabin ta da ƙasa.
Jikin Umma Salma har yana rawa ta dinga shinshinawa.
"Kai Harira aikin ki na kyau ta wajena."
Tana shinshina ƙasar har tana sauke ajiyar Zuciya.
Nan ta ce Harira ta É—auko mata leda ta É—iba ta jika mata shi da ruwa.
"Ba ki dai shiga gida ba ko?
"Ai kin ce kar na shiga ranki ya daɗe. Mutane ne dai na ta kallona sun ga ina ta ɗiban ƙasa."
Ummu Salma ta yi dariya kafin ta ce.
"Ai sai ki ce lalura ce ba da gangan ba ne."
Harira ta amsa da ba su mini magana ba amma mamaki suke yi na me zan yi da ƙasa haka, mai adaidaitan da yakai ni ma ya jirani sai da ya tambaya na ce masa na mai ciki ne ya ce wallahi shima matarsa ƙamshin yashi take so.
"Gwara da kika faÉ—a masa kar ya ce na asiri ne."
Dukkansu suka yi dariya. Sannan Harira ta tafi kitchen ta ɗauko mata roban gwangwanin madara da ya ƙare ta ce bari kawai a zuba a ciki ta huta da leda
"Kuma fa hakane, to zuba da sauri ki jiƙa mini, wannan kuma ki ɓoye mini a cikin kitchen"
Harira ta aiwatar da duka umarninta.
Lokacin da ta kai hancinta tana shaƙan kamshin har jikinta sai da ta ji ya samu natsuwa cikinta kuma ta ji kamar ya juya.
Shike nan ta samu zaman lafiya Hamma Saddam kuma sai wajen sha biyu da rabi ya kira ta haushi ya sa ba ta ɗaga wayarsa ba. Ba amfanin da zai yi mata kuma a yanzu ga ƙasarta a hannunta tana shinshina kamar wata mage.
Sallar azahar ya sa ta bar falo ta koma ciki ta yi salla. Ta kwanta tana ta barci saboda likita ya ce ta dinga samun barci sosai wajen uku na rana yunwa ya tashe ta, ta je kitchen ta nemo sauran tuwonta tun na shekaranjiya da Harira ta yi mata da miyar kuka ta ciro a firiza ta kunna gas ta ɗumama miyar ba manja ba maggi dunƙule sai gishiri shima kaɗan sai farin maggi, ba ta son ko wani ƙamshi.
Kodayaushe ta zo kunna gas sai ta tuna da wani abu ya faru farkon dawowarsu kawai ta shigo kitchen ta rasa abin da za ta yi, kawai sai ta kunna gas ta ɗora tukunya ta manta kawai ta koma ɗaki ta kwanta, Allah ya taimaka Harira ta zo kitchen ɗin ta ji ƙauri, da sauri ta kashe gas ɗin ta sauke tukunyar har ta fara ƙonewa da Harira ke faɗa mata shuru kawai ta yi ba ta san ta yi ba
Received at 07:54Reactions: ⤠15, 👠1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
abubuwa suna yi mata wani irin tun bayan abin da ya same ta na rasa jarirnta, sannan tana zaune kawai sai ta dinga jin wani ƙara a cikin kanta, ƙaran mai yawa yana barazanar fasa kunnuwanta, chanje-chanje da dama take fuskata da ta koma asibiti ta yi musu bayanin likitan ya ba ta tabbacin alamomin cutar Eclampsia da ta yi fama da shi ne lokacin da ta haihu, amma ta gode ma Allah ta fita daga haɗari suma canje canje a hankali za ta daina fuskartarsu. Kullum ta yi salla sai ta yi ma Allah godiya da ya tsare ta da wannan cutar, domin tana da haɗari itama za ta iya ba da labarin haɗarin ta.
A kitchen ɗin ta ci tuwon nan ta wanke hannunta sannan ta koma ɗaki Harira na cikin ɗakinta wataƙila ta kwanta ne. Da ta koma ɗaki ba ta kwanta ba sai ta fara gyara kayanta wajen kwana huɗu kenan mai wanki ya kawo su da sauran ƙananun da Harira ta wanke mata ita kuma ta ce ta bar mata za ta gyara su amma ta kasa.
Sai da ta gama tas ta jera a wardrope sannan ta shiga tiolet ta yi wanka ta ɗauro alwala ta fito ba shafa mai take yi ba doguwar rigarta kawai ta material ta saka akwai tattara ta ƙasa sai aka sake ta. Akwai zanen baƙi a cikin material ɗin sai ta saka hula baka ta rufe kitsonta da ya tsufa.
Falo ta fito ta zauna a saman kujera tana canza tasha zuwa Saira movies ta ga suna maimaicin shirin gidan Sarauta.
Ba daÉ—ewa sai ga Harira ta fito, tana tambayan abin da za a dafa.
"Harira ni fa ba cin abincin nan zan yi ba kullum sai kin tambaya ne?
Harira ta sunkuyar da kai ba ta yi magana ba.
"Ki je ki dafa duk abin da kike so Harira nan fa gidanmu ne."
"To ranki ya dade"
Har ta wuce sai ta dawo.
"Ba za a yi miki wani abu ba?
"Tuwo ne kuma ina É—an da sauran shi, bari da safe sai ki yi mini wani"
Harira ta wuce kitchen tana faÉ—in Allah ya kaimu.
Ta bar Ummu Salma na kallo. Ta mayar da hankalinta kan kallo amma ba ta jin nishaÉ—in da take ji a da in tana kallo gata nan dai zaune kawai.
Adaidai lokacin da agogon bangon dake falo ya harba 4:30pm na yamma daidai ta ji ana buga ƙofa an yi knooking na farko ba ta tashi ba, ta ɗauka ma Saddam ne har tana tura baki.
To tun É—azu ta so zuwansa bai zo ba sai yanzu.
Ta ji daɗin zaman kamar kar ta tashi sannan ga Harira na kitchen akwai ba da wahala ta ce ta baro kitchen ta zo ta buɗe ƙofa.
Sai biyu aka yi knooking sannan ta iya miƙewa ta isa ga ƙofar ta buɗe
Tana buɗe ƙofar ta juya ko kallon wanda ke tsaye ma ba ta yi ba.
"Sai yanzu? Ai Sai É—an cikina ya bare da na tsaya jiran ka."
Ta faÉ—a tana komawa ta zauna a in da ta tashi.
Abin da ya ba ta mamaki jin shuru ba ta ji motsi ko surutun Hamma Saddam ba, shi da tun kafin ya shigo ake fara jin karaÉ—insa.
Sai ta juya a hankali wanda ta yi arba da shi ne ya sa gudun zuciyarta tsayawa na wani lokaci.
Kasala da wani irin sanyi ya lulluɓeta a lokaci ɗaya nauyin jikinta sai ya ƙaru.
Ya shigo falon sannan ya saka hannu rufe ƙofar falon
Lokacin da ya fara takowa a tsakiyar falon ƙirjinta ya fara bugawa fat! Fat!
Ta kafe shi da idanuwana ba kiftawa shima ita yake kallo da yanayin kallon nan na shi mai sanyata kasala.
*Janafty*
Received at 07:54Reactions: ⤠19, 🥰 1, 😠1

Duk takun zai yi domin matsowa zuwa gareta, tare yake da tsinkewar zuciyarta. Ita ta fara ɗauke idanuwanta a kan shi domin ba za ta iya juran kallon shi ba tana jin wani iri kaifaffun idanuwansa da kuma ƙwarjinsa sun cika falon ga ƙofofin hancinta na shaƙo mata sanyayyan ƙamshin shi wanda a baya yake sanyata cikin shauƙi da soyayya amma yau zuciyarta ne ta fara tsinkewa tana jin kamar za ta yi amai tunda ya shigo falon ƙamshin gabaɗaya ya gauraye falon.
Kanta na ƙasa tana wasa da zoben azurfan da Mai martaba ya yi mata kyautar shi tana jin a jikinta da zuciyanta Hamma Lamiɗo bai daina kallonta ba sannan yana ƙara kusantowa zuwa gare ta ne.
Jikinta har rawa ya fara saboda fargaba, duk da ta daɗe tana shirya maganganun da za ta kare kanta duk ranar da Hamma ya waiwayota amma kuma ganin shi a gabanta bagatatan ya wargaje duka shirinta, ta kasa ko iya kallon shi ta kasa miƙewa saboda yadda jikinta ya yi mata nauyi.
"Ummu Salama."
Ta ji ya kira sunanta a hankali da wannan muryan na shi cikin amo.
Sai idanuwanta suka cika da ƙwalla ta yi kewar kiran sunanta da yake yi shi kaɗai ne ke kiranta da Ummu Salama. Ta ɗago suka sake haɗa idanuwana wannan karon har ya ƙariso gabda yana tsaye hannunsa guda ɗaya a cikin aljihun bakin yadin dake jikinsa ɗinkin riga da wando har da babban riga. Amma babban rigan tana hannun shi na dama, kafafuna sanye da budaɗɗen takalmi na fata baƙi kansa kuma ya saka baƙar hula gashin sa ya fito ta gefe da gefen hulan sannan fuskarsa ta yi fayau tunda ya rage gashin gemu sa da sajensa gabaɗaya.
Kallon shi take yi tana ji kamar ba Hamma Lamiɗon da ta sani a shekara ɗaya da wani abu baya ba. Kamar Hamma Lamiɗo da ta sani dai a shekarun baya ne. Ta kasa iya motsi ballatana ta iya amsa kiran sunanta da ya yi ko ta yi masa sannu da zuwa ba komai ya ƙwace mata kanta ta mayar ƙasa tana jin tafin kafafunta na ɗaukan ɗumi sosai. Wattani biyu ta yi ba ta gan shi ba amma ji take yi kamar shekara ce.
Shi ko kallonta yake yi da dukkan zuciyarsa. Me ya same ta? Ya ga ta rame wuyanta sun faɗa idanuwanta sun ƙanƙance komai na ta ya sauya ba kamar yadda ya tafi ya barta ba.
Wani abu ne ya faru da ita ne?
"What wrong with you?
"Are you sick?
Tambayoyin duk a tare ya jera mata su, ita kuma lokacin zuciyarta ne ke cigaba da tsinkewa tana jin kamar za ta yi amai shi ya sa ta miƙe dakyar tana jin kamar jikinta ya yi ma kafafunta nauyi.
"Sannu da zuwa."
Ta faÉ—a cikin sanyin murya amma ta ki bari su sake haÉ—a ido.
Ya amsa da yauwa a iya fatar bakinsa.
"Na ce ba ki da lafiya ne?