← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 75

Sashe 49

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu ta miƙa ta ɗauki jinjirar ta rumgume kawai ta yi tsaye.
Ummu Salma ta ce"Mami BBC suka sanar ga sauran gidan jaridu nan ma na fitar sanarwan Mami ga shi su Hamma Kabiru a group ma suna mganar"

Take faÉ—a cikin ruÉ—ewa sannan ta fara karanta abin da BBC HAUSA suka fitar da hoton Mai martaba.

"SARKIN DAURA ALHAJI DR NASIRU MUHAMMAD SHITU, YA YI MURABUS DAGA KAN ƘARAGARSA A DARAN JIYA SANNAN YA ƊORA BABBAN ƊANSA MUHAMMAD NASIRU MUHAMMAD A MADADINSA."

Duk in da ka shiga labarin dake yawo kenan bisa laka'ari da cewa ba a cika samun Sarki ya yi murabus ya gadar ma wani ɗansa Sarauta ba an fi dai samun Sarki ya rasu a fafata a zaɓen majilisar fada har a samu wanda zai gaje shi sama da shekari hamsin a tarihin Masarautar Daura haka bai taɓa faruwa ba shi ya sa ya zama sabon abu.

Ummu Saalma sai hawayen farinciki daman shi ya sa aka ji Hamma Shuru shi kaÉ—ai ya san halin da yake ciki.

"Allah sarki Hamma ba ya son sha'anin mulki. Daman abin da muke so ba shi Allah ke bamu ba, sai wanda ba mu saka rai da samun sa ba."

Sai hawaye shar sannan ta cigaba da faÉ—in.

"Ko ya zai ji a yanzu?

Shi kawai take tunani ga shi ba ta kusa da shi da ace tana kusa ma ba za ta samu ganin shi ba. Yanzu ba Yarima ba ne Sarkin Daura ne.

"Allah ya ta shi riƙo. Allah ya tsare shi."

Mami ta faɗa duk koƙarinta na kar ta yi hawaye sai da ta yi ta tuna maganar Baffa in tana cewa ta tsani abin da ya shafi Sarauta

"Ki kika sani ko É—anki ya zama Sarki watarana Fatima? Ko ba na raye hakan ta faru ki yi masa fatan alheri Ubangiji ya kaddara haka ki daina jayayya da kaddara "

Ta fashe da kuka tana rumgume Jaririyar Hannunta.

"Allah ya gafarta maka Baffa."

"Kin zo duniyar a ranar da mahaifinki ya zama Sarki. Barka da zuwa SARAUNIYA DAURAMA."

"ALLAH ga bawan ka nan Muhammadu ya zama shugaban wasu al'umma a yau, Allah ka ta ya shi riƙo ka jiɓanci lamuran shi, ka kiyayesa ka taya shi kar ka barshi shi kaɗai Ubangiji ka taya sa riƙo."

Ummu Salma da Harira suna taya ta da amsawa da Amin a tare wayoyin su suka É—au kara Video call ne ita Ummu Salma BaÉ—É—o ce ke kiranta ita kuma Mami Hamma Saddam.

Jaririyar Mami ta miƙa ma Harira ita kuma ta ɗauki wayar sai ga Ammah da Hamma Saddam da Hamma Abdulrahim, har da su Hamma Abdulrraham daga gani daga salla asuba suka zarto gida kowanne da Jallabiya.

"Fatima LamiÉ—o ya zama Sarki."

Ammah ta faÉ—a cikin wani karaÉ—i a muryanta.
Mami ta ce haka ta gani Hamma Saddam ya yi jinjina.

'Sannu Fulanin Daura an gaishe ki."

Aka kwashe da dariya. Ammah na hawaye tana addua'n Allah ya ta ya LamiÉ—o riko.
Su Hamma Saddam na ta murna da ihu sannan ga murnan Auta ta sauka an haskota tana videa call da BaÉ—É—o wacce ke ta murna da tsalle.

"Ranki ya daÉ—e da gaske dai kin zama Sarauniyar Daurama."

"Kin iya haihuwa tarihi ba zai manta da wannan haihuwar taki ba Sis na."

Ga murnan haihuwa ga ta Sarauta. Ummu Salma ta yi magana da su Ammah kowa sai da ya kira su video call har Hamma Kabiru ya ce bai samu Hamma LamiÉ—o a waya ba.
Received at 18:55
Bilkisu reacted with ❤
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Mu ma nan ba mu same shi ba tun tafiyan shi. Yanzu É—in ma ba lalle a same shi a yanzu ba mu jira ya neme mu."

Haka Mami ta faÉ—a, dole kam a jira jin ta bakinsa.
Yayyenta duk sun mata barka suna faÉ—in ta iya haihuwa.

Kafin ka ce me gabaÉ—aya social media da dukkan wani platform sun saka labarin abin da ya faru a Daura. Sannan hotunan LamiÉ—o sun fara yawo tare da cikakken tarihinsa wasu hotunan da naÉ—i a jikinsa irin wanda ake yi masa da salla ne sai wasu hotunan kuma yana cikin Uniform É—insa na tukin jirgin ruwa.

"MUHAMMAD NASIRU MUHAMMAD LAMIƊO, SHI NE ƊA NA FARI GA MAI MARTABA SARKIN DAURA MAHAIFIYAR SA HAJIYA FATIMA BABA, BA YAR MASARAUTA BA CE SUN RABU TUN KAFIN TSOHON SARKI MAI MURABUS YA HAU KAN KARAGA. MUHAMMAD LAMIƊO MATASHI NE ƊAN KIMANIN SHEKARU ARBA'IN A DUNIYA YA YI KARATUNSA NA TUKIN JIRGIN RUWA A ƘASAR MALAYSIA YANZU HAKA MA'AIKACI NE A KAMFAMIN CHEVRON NIGERIA LIMITED A MATSAYIN ƊAYA DAGA CIKIN MARINE, MA'ANA CAPTAIN ƊIN SU MASU JIGILAN JIRAGENSU ZUWA ƘASASHEN WAJE YANA DA MATAR AURE GUDA BIYU DA YARA BIYU, MATARSA TA FARKO HAJIYA BILKISU USMAN BAYERO ƊIYAR SARKI KANO USMAN BAYERO."

Rubutun dake ta yawo kenan tare da hotunan Lamiɗo nan da nan yan'uwa suka fara status na ta ya murna ga Lamiɗo da kuma na samun ƙaruwa.
Gimbiya Shahida ta kira Ummu Salma a waya sun yi magana ta ce Fada ta cika saboda murabus É—in mai Mai martaba a maganar da take yi ma tuni LamiÉ—o na fada a matsayin Sarkin Daura.
Ta ce su kan su ba su san hukunci da Mai martaba ya yanke ba kenan.

Ana ta yawo da maganar ko wata Sarautar zai canza ma Yarima ashe Murabus zai yi suma tun jiya ba su gan shi ba murabus É—in cikin dare aka yi shi a daran kuma aka naÉ—a LamiÉ—o sai dai Kawai aka wayi gari da sanarwaan amma zuwa yamma Mai martaba zau gana da yan jaridu da gidajen talabijin zai yi bayani ga al'ummar Daura da sauran mutane.

Ta kwantar ma da Umma Salma hankali da cewa ta kwantar da hankalinta ta samu lafiya ta kula da kanta da jaririyarta. Har zuwa nan da kura ta lafa yanzu dai LamiÉ—o ba zai samu kan shi ba gaskiya. Kuma gaskiya ta faÉ—a tabbas sai nan da lokaci kaÉ—an maganar haihuwa ma bai sani ba domin ba a faÉ—a masa ba waya ce kuma ba ta tare da shi.

Kamar yadda Ummu Salma ta ga abin daga sama haka Bilkisu ta ji, ita tana barci daga cikin ahalin gidansu aka samu wani yayanta ya kira ta ya faɗa mata tana hawa social media ta samu tabbaci jiki na rawa ta kira Gimbiya Hadiza ta ƙara samu tabbaci. Ta tabbatar mata da cewa da suma haka suka wayi gari amma kamar Fulani da duka yan'uwan Mai martaba mai murabus sun san da faruwar komai.

Bilkisu ta daka tsalle ta dira saman gado ta fita falo daga ita sai rigar barci ta dinga kiran Sabuwa sai ga su a rikice sun É—auka wani abu ne ya faru sai ga shi tana faÉ—a musu Yarima ya zama Sarki bayan ta rumgume Sabuwa.

Su Debora da Anitha suka rumgume juna suna yi ma Bilkisu congratulations yara ma ihun murnanta ya tashe su ai sai ta shiga É—aga su É—ayan bayan É—aya tana juyi da su. Har da Hanan tana faÉ—a musu Papa is now a king of Daura duk da ba su wani gane ba suna ta murna. Bilkisu kai ya yi girma ta zama matar Sarki ta manta da batun wasu kishiya murna kawai take yi haka ta kira Umman kano tana murna ta ce suma sun samu labari.

Ta ce sai ta yi ta ma Allah godiya tare da addu'an Allah ya taya mijinta riƙo.
Sai bayan sun gama wayar ne ta lura da status É—in Adda Safina da hoton jaririya ta fara cin karo.

"Welcome to the world Princess. Kin iya zuwa duniya. Ranar da muke murna Babanki ya zama Sarkin Daura."

Ko ba a fada ba wannan jaririyar É—iyar Umma Salma ce ta haihu kenan? Ta san da LamiÉ—o na cikin sukuni zai faÉ—a mata yanzu ko a duniya ta ji ta ce Allah y raya ba ta damu ba. Ita yanzu ba kishi ba ne a gabanta she is now Gimbiya Bilkisu Gimbiya Bilkisu matar Sarkin Daura.

Ta zauna ta saka hoton Lamiɗo ta yi dogon rubutu na murna ta yi status dangi da abokan arzuƙa ana ta taya ta murna da barka da arziki.
Received at 18:55
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ranar har busa ta yi connecting ta wayarta daga speaker ta fara juyi tana kaÉ—a kai ranar farinciki ce wayoyin ko da ta amsa na mutane ba ta san adadi ba har da su Sofia duk sun yi waya suna ta ya ta murna ko da hukuncin bai yi ma wasu daÉ—i ba hukuncin ya riga ya zartu ba yadda aka iya.

Da yamma misalin shidda na yammaci aka fitar da maganar da Mai martaba mai Murabus ya yi da manema labarai aka watsa a duniya.

"Ni Alhaji Dr Nasiru Muhammad Shitu, a jiya 8 ga watan November wanda ya yi daidai da shekara ta dubu biyu da ashirin da biyar. Na yi murabus daga kan ƙaragar mulkin garin Daura na gadar ma babban ɗana Muhammad Lamiɗo ɗan Nasiru jikan Shitu, a kuma jiyan ya fara zama wakilin ku sarkin ku. Dalilina shi ne ina cikin jinya ina buƙatar hutawa domin inganta lafiyata. Bayan zama da masu ruwa da tsaki na fada majalisar zaɓe tare da malamai, Hakimai masu Sarauta alƙalai tare da limaman mu, sai kuma dattawan da hikaman mu a karshe suka aminta da tsarina bayan duba da cancantar wanda na kawo a matsayin wanda zai gaje ni. Alhamdululillah Allah na gode maka ina bayar da haƙuri duka al'ummata na Garin Daura da kewayenta. Da wanda ya ji daɗi da wanda bai ji daɗi ba, ku sani nima na ji daɗin tsawon shekarun da na kwashe ina mulki tare da ku, da wannan damar nake neman afuwarku na san a shugabancina ba zai yuyu na faranta ma kowa ba, ku yi mini afuwa in da na kuskure ina fatan Ubangiji ya tsare Masarautar Daura. Allah ya kare Jihar Katsina da Al'ummarta gabaɗaya. Ina mai yi muku albishir ɗin cewa za ku ji daɗin mulki Sarkin ku na Yanzu Muhammad Lamiɗo fiye da mulkina. Ubangiji ya taimake mu ya taimaki kasarmu Nigeria gabaɗaya ya ɗaga darajar Masarautun gargarjiya da addinin musulunci gabaɗaya.."
Chapter 49 · 0% Book details