← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 75

Sashe 19

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"E, ai shi Sarkin Daura ya taɓa auren ƙanwar ita mahaifin Ummu Salma ta haihu da shi suka rabu tun kafin ya zama sarkin ma, ni lokacin na sani tunda Habibu ya faɗa mini , yanzu kuma an ce shi take aure ban dai sani ba ko yana cikin mazan da muka gani a gidan"

"Yana nan"

Habib ya amsa a sanyaye

"Yana nan wani fari dogo baya magana, domin har muka tafi ban ji ya yi magana ba."
Received at 11:37Reactions: ❤ 3, 🥰 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Gwaggo ta ce ba ta kula da shi ba, Hajiya Sahura ta ce ai duk kusan yaran farare ne suna kama da junan su.
Alhaji Sherif da Hajiya Sahura ba su jima ba suka tafi tunda mangariba ta yi Gwaggo na ta yi musu godiya.
Baba Usman ma gida ya tafi amma Habiba na nan so take yi ta ga abin da zai faru a gidan sai ta ce ma Gwaggo anan za ta kwana sai da safe za ta koma gidanta

Ai ko ta sha kallo, domin haka yan'uwa Habib ke tururuwan zuwa ganin Hanan washegari Hanan ta gaji ta daina kuka, Shamsiya ta yi mata wanka ta kuma dafa mata indomie da safe, amma har cikin dare ta tashi da rigima tana kiran sunan Mahma da Mami
Shamsiyar ta goyata a daran ta kwana jijjiga Habib kuma bai yi barci ba, farincikin da yake ciki ya hana shi barci kwana ya yi yana kallon Hanan yana hawaye, yana cewa yanzu wannan yarinyar É—iyarsa ce! Ya yi ma Allah godiya a fili da sarari bai san iyaka ba, bai É—auketa ba domin sai ya ji ya kasa amma saboda kallo har ya haddace kamaninta

Hanan ta sha É—auka, ta shiga hannun wannan ta fita ta koma hannun wannan
Kowa sha'awarta yake yi, kuma kowa in ya zo sai ya ba ta kuɗi ko wani abu, tun tana ƙiyuwa har ta dawo ta daina sai dai bin mutane da kallo, kowa mamaki yake yi ashe cikin da Ummu Salma ta fita da shi ta haife shi, ga Hanan sun gani a matsayin shaida.

Hanan ta fara sabawa da Shamsiya tunda ita ke wahala da ita, sannan in Gwaggo za ta ɗauketa ba ta ƙiyuwa yanzu Habib kuma sai dai ya tasa ta kawai yana kallo Habiba ta gaji da ganin takaici ta koma gida ranar a wajenta Habib ya kwana ko tarin ta bai ji ba, ta saba ta dinga masa habaici da tijara amma ranar tunda ta shige ciki sai da safe ya ganta da alamun dai jikinta ya yi sanyi, ko kuma ba haka ta so ya faru ba.

*
BAYAN KWANA HUÆŠU.

Ranar asabar misalin ƙarfe goma na safe Hamma Jibo ne da iyalansa ke ta haraman komawa Abuja.

GabaÉ—aya suna falon Ammah har su Hamma Abdullahi duk sun taho domin yin sallama dashi duk da jiya har wajen sha É—aya na dare da shi da Hamma Abdulrahaman duk suna gidan.

Ummu Salma na cikin É—akinta duk hayaniyar da ake yi ba ta fito ba. Tun bayan abin da ya faru ta daina ma kowa magana ta daina hira ta daina dariya ko falo ba ta fitowa tana cikin É—aki abinci sai dai Harira ko Mami su shigar mata da shi.

A gidan ma su kaɗai ne ke shigowa in da take, Ammah ko ɓarayin ɗakin ba ta sake kallo ba, ballatana Umma Balki da ta ce ba ta da kunya itama ta fita bayanta kan abin da ta yi Mami ce kawai ba ta taɓa juya mata baya ba sai Hamma Saddam da shi Abdulrahim suma ɗin ta ji haushin su domin suna bayan Lamiɗo kuma duka maganarsu ta kira Lamiɗo ta ba shi haƙuri ne ita an kasa gane yanayin ta shi ne mai gaskiya ita ce mai laifi.

Hamma Abdulrahaman kuma a gabanta jiya da Hamma Jibo ya kira ta da daddare yana yi mata faÉ—a ya ce ya so ne ma LamiÉ—o ya kikkifa mata mari saboda ta yi rashin kunya.
Duk a cikin abin da ya faru abu ɗaya ne ta yi nadamar shi maganganun da ta faɗa ma Ammah sune ta yi nadama kuma har haƙuri Hamma Jibo ya saka ta duƙa ta ba ma Ammah a jiyan
Daga yanayin yadda Ammah ta amsa mata itama haushin ta take ji.

"Ni ba ki yi mini komai ba Ummu Salama, kukana É—aya ko wata É—aya ba a yi da kasa ta shafe idanuwan Baffa ba amma har kin fara yi mini gaddama da nuna cewa ban isa dake da abin da kika haifa ba."

Kowa laifinta yake gani an kasa samun mutum É—aya da zai fahimci raunin ta? Sun manta itama mai rai ce tana da zuciya a kirjinta uba fa ta rasa a tsakani kwana biyu ta rasa jaririnta me ya sa ba za ta damu don za a raba ta da É—iyarta ba a matsayinta na uwa bai dace a ji ta bakin ta ba? Sai kawai a yanke ma rayuwarta hukunci don ta ce ba ta amince ba sai kowa ya koma yana ganin laifinta.

Kuka kawai take yi in ta tuna da rashin da Baffa yau da yana raye da duk haka ba ta faru ba ko da zai yanke hukunci ba zai yi kai tsaye ba sai da amincewarta ba zai yi mata dole ko tursasa ta ba. Har yau da Baffa da ke da kwana ashirin da biyar da rasuwa ta kasa gasgata mutuwarsa gani take yi kamar mafarki ne kamar tafiya ya yi zai dawo nan ba da jimawa ba
Received at 11:37Reactions: ❤ 6, 👍 1, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Duk da yadda yan'uwanta suka gasa fahimtar ta ya yi mata zafi, amma duk bai kai kwatankwancin abin da Hamma LamiÉ—o ya yi mata. Ga kewar Hanan da ya yi mata rami a zuciya gani take yi kamar za ta rasa ta ne alhalin a lokacin ita kaÉ—ai gare ta.

Yadda suke da shi ta É—auka zai fi kowa fahimtar halin da ta ke ciki. Ta rasa mahaifinta ta rasa jaririnta duk a lokaci É—aya shin ba ta cancanci tausayawa ba ne? Abin da ya yi mata ya fi rashin Hanan zafi a zuciyanta. Shi ne fa ya buÉ—e baki a gaban mutane ya ce wai zai sake ta, ta koma wajen Habib in ta tuna ma da kalamansa sai ta ji kamar ta kurma ihu, komai zai faru tsakaninsu ba ta É—auka a tsakanin ita da shi ma zai iya kallonta ya faÉ—a mata zai iya sakinta ba, ballatana a bainar nasi gaban kowa da kowa.

Abin takaicin ma wai ta koma ma Habib, mutumin da ta tsana. Ai tunda ya gama da ita, itama ta gama da shi har gaban abada. Gwara ta mutu ba ta sake aure ba, in ta kama Hanan É—in ta koma wajensa ko son yarinyar zai kasheta ta gwammace ta yafe ta har abada. Abubuwa biyun nan suka sake raunana zuciyarta suka tafiyar da sauran fatan ta ga cigaba da rayuwar farinciki.

A daran ranar sai asuba barci ya kwasheta, kuka kawai take yi ga tunanin Hanan ta na can wani wajen za ta kwana ba ta san sau adadin nawa ta yi addu'an da Allah ya nesanta Hanan da Habib da zuru'an shi na har abada ba. Shi ya ce ba ya son cikin nan kuma akan shi ya yi mata wulaƙanci ya saketa sannan ya ce ta je da cikin baya so me ya sa Ammah za ta tusa masa abin da ya ce ba ya so ya bar mata? Don ya yi nadama ba ya nufin cewa ta sadaukar da Hanan ga nadamarsa in kuma wasiyya Baffa ce ta tabbata da shi ne ba haka zai yi ba duk abin da zai aikata ko zai yanke akan rayuwarta sai ya tuntuɓeta sai ya tabbatar da ta gamsu da niyyarsa amma daga Ammah har su Hamma Jibo ba wanda ya tsaya ya fahimceta kowa ita yake ganin laifinta.

Sannan ga baƙincikin kalaman Hamma Lamiɗo da suka zame mata dalma, saboda haka ya sa ko sunan shi ba ta son tunawa, mutumin da a baya ko sunan shi ta ji sai zuciyanta ta yi rawa amma ban da yanzu da tuna sunan shi ma kaɗai na kara sanyata jin haushin shi mai tsanani ya kama hanya ya yi tafiyarsa bai yi mata sallama ba, bai kuma sake nemanta ba ko a waya haushinta ɗaya wato shi ma a ganin shi bai yi laifi ba ita ce ta yi masa laifi don ya ce zai saketa ta ce sai me? Ita ce yake jira ta kira shi tana ba shi haƙuri ita kuma a yadda ta ke jin zuciyarta ko za su dauwama a haka ba za ta ce ya yi haƙuri ba domin shi ya fara rusa yarda da amincin dake tsakaninsu.

Gani ake yi kamar in ya rabu da ita wani abu ne, a yadda take jin kanta da yadda duniyar ta fita kanta ba za ta taba damuwa don Hamma Lamiɗo ya sake ta ba. Haushin shi da take ji yasa ta ji ba ta son shi yanzu, ko ya sake ta babu abin da za ta rasa domin ita an gama yi mata rashi a duniya. Har jiya da aka zauna zaman meeting din da Hamma Jibo ya haɗa a daran an kira Hamma Kabiru a waya aka saka a amsa kuwwa tana ji yana faɗin ya so Lamiɗo ya sake ta da gaske ya ga yadda za ta ƙare. Cikin izza yake faɗin ba za ta samu wanda yake ƙasa da shi ba kamar ma kuma ya yi mata nisa ta yi kuka sosai hawayenta har da majina kowa ita yake gani a matsayin mai laifi shi da ya fara furta kalaman shi bai yi laifi ba sai ita da ya mayar ma martani, ba zununci ba ko menene sai da ya lalace za ta nuna ma kowa Lamiɗo ba don shi aka haife ta ba, shima ba don ita ya zo duniya ba kowa ma zai iya rayuwa ba ɗan'uwansa kuma ya zauna lafiya.
Chapter 19 · 0% Book details