← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 75

Sashe 12

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

An barsu sun shiga amma mutum biyu biyu, sun duba ta da jiki, likita dai ya ce ba yanzu za su sallameta ba sai an kwance É—inki sannan sai jininta ya daidaita.
Ammah ce kawai ba ta zo duba ta ba, amma dai sun gaisa ta waya.
Kowa dauriyan Ummu Salma yake gani ba ta yi kuka ba da aka ce jaririnta ya zo ba rai nan ko ba su san raÉ—aÉ—in dake cin ta a zuciya ba.

Satin ta ɗaya a asibiti aka kwance ɗinki. Har a lokacin ba a wanka sun ce jikinta na da kyau ba ta da ƙwan jiki babu wata matsala sun kara mata kwana uku sai ta yi kwana goma sannan za ta fara wanka. Amma tana shiga ruwan ɗumi saboda tsarki da jini.
Mami da BaÉ—É—o ne tsaye a kanta shi ya sa suke da wani matsayi mai girma a zuciyarta.
Yayyenta ma suna zuwa duba ta tunda duk suna nan ba su koma ba.

Tana asibitin ne amma hankalinta duk yana gida.
Ita na ta zaman makokin a gadon asibiti ta yi shi.

Sannan ta zama wata shuru shuru magana ma ba ta yi ban da ta amsa ya jiki shike nan. Ba wanda ya damu tunda tana cikin jinya ne ga rashi har sau biyu, ita ko ba su san abin da take hange ba gani take yi tunda ta rasa Baffa ba za ta sake rayuwa mai daɗi ba sannan ta zo ta rasa jaririnta tun daga lokacin ta ji duniyar ma ta fita kanta har cewa ta yi me ya sa ba ta mutu a wajen haihuwar ba! Da ta huta da wannan  raɗadin da duniyar ma gabaɗaya. Yanayinta ne kwata-kwata ba ta gane ba, tana jin ta kamar wata sabuwar hallita.

Kwananta goma sha biyu a gadon asibiti suka sallameta jininta ya sauka ya koma 130 sannan sun yi dukkan gwaje gwaje babu wata matsala an kwancen É—inki har ta fara wanka. Sun koma gida Baffa na da sati biyu da rasuwa kenan.

Washegarin ranar da ta dawo gida Fulani da Gimbiya Shahida tare da Saleem da Hajiya Kilishi suka dawo gaisuwa suka kuma sake duba ta da jiki.
Mai Martaba dai bai dawo ba amma ya sake turo wakilai ranar da aka yi bakwai.
A ɗakinta dake cikin falon Ammah aka sauke ta, Baɗɗo har lolacin ba ta koma gida ba tana tare da Ummu Salma sai da ta dawo ne ta ga Harira baiwar Allah ita ce ke kula da yaran dake gidan Hanan ma ta zo wajenta tana surutun Mahma ban gan ki ba Papa ya ce kin yi tafiya sai ta amsa mata tana shafa kanta idanuwanta suka kawo ƙwalla Hanan kaɗai ta rage mata a yanzu a duniya.

Ummu Balki da Umma A'i suna nan ba su koma ba. Amma Umma A'i za ta koma ita Umma Balki ce sai an yi arba'in za ta koma Mami na nan ba ta ma saka ranar tafiya ba Daddy ma ya dawo shi ya tafi da Barira za ta je can zamfara ta ga iyayenta kafin Mami ta dawo.
Su Hamma Jibo duk suna nan tare da matayensu suma ba wanda ya saka ranar tafiya.

Baffa ya rasu ranar talata 21 ga wata December, shi kuma jaririn Ummu Salma ranar 22 ya zo duniya ya kuma koma a ranar 24 ga watan december. Ga shi har an shiga sabuwar shekara.

Makota da wasu da ba su samu zuwa gaisuwa ba suna É—an shigowa yin gaisuwa. Ummu Salma ta koma ba ta uhm ba uhm, duk abin da aka ce za ta ce to kawai jinin haihuwanta kwana sha uku ya yi ya É—auke amma tana shiga ruwan zafi sannan Mami na yi mata wankan jego na towel tana gasa mata jiki cikin dubara duk da mikin wajen da aka yi mata aiki yana ta warkewa yana haÉ—ewa. Sannan sun rubuta magunguna an siya tana sha, dokar likita ce ta dinga cin abubuwan da za su gina mata jiki sannan ta dinga motsa jikinta sannan wannan haihuwar ta É—an ajiye tumbi ba kamar na Hanan ba.

Ita ba ta wannan take ba, jikinta ko wani gayun duniya ba ya gabanta yanzu
Received at 10:01Reactions: ❤ 6, 👍 3
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
In ta tuna yau Baffa a duniyar nan sai ta ji ta rasa meke yi mata daÉ—i, sai da ta dawo gida aka ba ta wayarta.
A status ta ga Hamma Saddam ya saka hoton jaririnta ta yi saving a ɓoye ta ɗauka tana kallo tana kuka haka ma hoton Baffa gani take yi kamar zai dawo gani take yi kamar a mafarki.
Kwata kwata ba ta cikin natsuwarta amma dai tana bin shawaran likita tana kokarin yaki da abin da ke damunta amma dafin da radaɗin rashin Baffa wani abu ne da har ta koma ga Allah ba zai taɓa gushewa ba.

Baffa mutum ne na gari ba domin yana matsayin uba gare ta, ta tuna ranar da ya rasu Hamma Jibo na tambayan ko ana bin shi bashi, tunda ana so kafin akai mamaci makawancinsa a biya masa bashi ko ya yi kwanciyar kabari cikin salama nan take Hamma Abdullahi ya ce Baffa ba ya cin bashi, tunda tare suke kasuwanci ya ce sai dai shi Baffan ne ke bin mutane bashi.

*

Ranar da Baffa yake da kwana da ashirin da biyu da rasuwa Umma A'i da Baffa Umaru suka koma Mubi, aka bar Umma Balki tare da Ammah sai Mami da matan su Hamma Jibo.
Suna nan ba su koma ba, kowa ba ya son tafiya duk da duk sun koma bakin aiki amma suna tunanin acikin satin nan duk za su koma suna ma ta shiri ne.

LamiÉ—o ne kawai bai koma aiki ba yana ma shirin tafiya Daura ne. Mai martaba zai koma London ganin likita cikin satin nan.
Mami ma tana nan ba ta ma saka rana ba, itama ba ta son tafiya duk dare haka suke taruwa suna tunawa da Baffa suna kuka, wato mutuwar Baffa rami ne a zukatansu da ba zai taɓa cikewa ba.
Ga Ummin ikki da itama koda yaushe a gidan take yini. BaÉ—É—o kuma nan wajen Umma Salma ta tare saboda ta É—ebe mata kewa
Duk ba wani hira suke yi ba.
Amma mutum rahama ne.

Ammah ko har yau ba wanda ya ga kukanta kuma ta na nan tsaye kan kafafunta.
Daman Umma Balki ta sha cewa Ammah jaruma ce sai da rasuwar Baffa kowa ya ga tabbaci ko kuka ake yi yanzu za ta fara faɗa da cewa su daina yi ma Baffa kuka addu'a kawai take roƙo su yi masa kodayaushe tana cikin hijabi da casbaha tana cikin ibada da nema ma Baffa gafaran Ubangijinsa kowa jinjina ma dauriyarta yake yi ta yi jarumta matuƙa.

Washegari kuma aka ce za a je maƙabarta ayi ma Baffa addu'a. Baffa Kabiru da Baffa Mustpaha gobe za su koma gidajen su.
Hamma LamiÉ—o ma a goben zai bi jirgi zuwa Katsina.
Mami kuma ta ce sai sati na sama Daddy zai zo sai su koma. Hamma Jibo kuma ya ce sai karshen sati za su koma Abuja.

Za a tafi gabaÉ—aya ne har da Mami da Ummu Salma duka gidan ma gabaÉ—aya.
Bayan la'asar suka tafi Ummu Salma ma motar Hamma Jibo ta shiga Hamma Lamido kuma motar Amininsa.
Sauran kuma suka shisshiga ta su Hamma Abdullahi.
Harira kawai aka bari a gida sai Islam da yara. Har da su Adda Nauwara aka je maƙabartan.

Maƙabatar ba nisa shi yasa suka isa da wuri.
Sun yi magana da maigadin wajen tunda ana ziyara addini ya hallata amma ba wai mutum ya samu wajen zuwa a kodayaushe ba.
Sunna ta yarje ma iyalan wanda ya rasu su ziyarce su domin su yi musu addu'a amma ba wai a mayar da abin kamar ibada ba.

Alaman da suka sanya yana nan amma zuwa lokacin nan Baffa sun yi nisa a makabarta. Kafin shigarsu Hamma Jibo ya ce kowa ya yi addu'an da muka sani a cikin azkar na shiga makabarta.
Kowa ya yi sannan daman suka shiga, a gaban kabarin Baffa Ammah ta dafa kasar tana yi ma Baffa addua'a.
Sai a lokacin ta yi kuka hawayenta na É—iga a saman hannunta da kasar kabarin Baffa.

"Allah ya jiƙan ka Baffa. Haƙurin da ka ba ni kafin rasuwarka na yi, ban yi kuka ba. Na gode Baffa Ubangiji ya sanya kabarinka cikin salama Allah ya yalwata maka hasken shi. Mun yi kewarka Allah ya sada ka da rahamarsa."

Sai a lokacin ta fashe da kuka Ummin ikki ta rumgumeta gefe tana lallashinta. Amma da Ummu Salma da su Mami suka fara kuka sai ta fara musu faÉ—an ba ta so. Hamma Abdullahi kuka Saddam kuka haka ma Abdulrahim
Ummu Salma kam sai da LamiÉ—o ya rumgumeta yana ta lallashi kuka har yana sauti.
Received at 10:01Reactions: ❤ 11, 👍 2
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sai da kowa ya yi masa addu'a sannan suka bar wajen kamar kar su tafi kamar su ga Baffa ya fito daga kabarin sun tafi gida tare da shi. In da aka binne jaririn Ummu Salma ne ya ɓace ba su gane wajen ba.
Shi ya sa ba su daÉ—e ba suka bar makabarta.
Suka duba hagu da dama, gabas da yamma maƙabarta babba ce amma ta yi rabi da mutane.

Jama'a mu dinga ziyartan maƙabararta za mu kara imani da tsoron Allah, za ka ga fa cewa kai ma wata rana nan ɗin ne gidan ka na gaskiya. Duk tarin arzikinka nan ne karshen ka, Sarki ma anan za a san ya shi haka ma Gwamna haka ma attajiri , haka ma talaka nan ɗin ne dai shine ƙarshe, za mu ƙara imani za mu ƙara jin cewa mu shirya ma muttuwa ko yau ko gobe ko anjuma tana tare damu.

Ubangiji ya sa mu yi kyakyawan ƙarshe. Allah ya sa mu mutu cikin imani.
Amin.

Sun koma gida kuma sai mutuwa ta dawo sabuwa
Suka haÉ—u suna ta kuka.
Ammah tana ta faÉ—an ita ba ta son kukan nan.

"Abdulrahim har da kai? Kai da za ka zama namiji mai lallashi "
Chapter 12 · 0% Book details