Sashe 16
Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta yi shuru tana mai kauda kai. Wani abu na taso mata sun fama mata gyambonta.
Hawaye suka kece mata amma ta kasa magana.
"Ki yi hakuri don Allah ki yafe mini. Na yi nadamar duk abubuwan da na yi miki."
Nan ma shuru sai hawaye, ji ta keyi kamar ba za ta iya yafe musu ba.
Gwaggo ta saka ba ki tana faÉ—in.
"An san an ɓata miki, amma don Allah ki yi hakuri ki yafe masa."
Hajiya Sahura ma ta saka baki haka ma Alhaji Sherif amma ya ce ba za a tursasa mata ba. An yi mata ba daidai ba ta yafe wannan imani ne in ma ba ta yafe ba, ba wanda zai ga laifinta.
Mami ta juya tana kallon Ummu Salma yadda take kuka ta kasa magana.
LamiÉ—o kuma ya kasa gane yanayinsa, me ya sa taki magana kawai ta ce ta yafe su bar gidan ba ya son ganin Habib kwata kwata.
Received at 11:37Reactions: ⤠9, 😠1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Shamsiya ce ta tashi daga in da take zaune ta ƙarisa gaban Ummu Salma ta durƙusa a gabanta.
"Bestie."
Ta faÉ—a muryanta na rawa BaÉ—É—o ta yi mata wani mugun kallo.
"Sunan ta Ummu Salma, wannan sunan kin daÉ—e da cire shi a tsakanin ku."
BaÉ—É—o ta amsa ma Shamsiya a fusace.
"Ki yi haƙuri Aisha."
"Ba komai Shamsiya. Ki yi hakuri kema amma ko tausayinku ban ji ba. Na ji ɗaɗi ma wataƙila kuma kun ɗanɗana irin zafin da muka ɗanɗana a zukatan mu a baya."
Shamsiya ta kasa magana sai kuka. Ta janyo hannuun Ummu Salma tana riƙewa a cikin nata hannun da sauri ta janye hannunta
Sai Shamsiya ta kece da kuka tana ba ta hakuri lokaci É—aya ta tsinke da ba ta labarin duk abin da ya faru.
"Ni na ba ma Habib shawaran ya zubar da cikin jikin ki, sai ga shi ni da nake son na haihu da shi Ubangiji ya hana ni sau uku ina samun ciki yana zubewa, likitoci sun ce ina da raunin mahaifa, zai yi wahala mahaifana ya iya rike ciki, wannan ba alhakin ki ba ne? Habib ɗin dana ke so na raba ki da shi ni na aure shi, daga baya nima ya guje ni, ya sake ni lokacin da na ke bukatarsa na koma gida cikin halin baƙin ciki na rasa karatuna a lokacin na kuma rasa mahafina. Ummu Salma na shiga jarabawa mai tsanani amma da wuri na gane kurakuraina na gyara, na daɗe ina tunanin hanyar da zan same ki, domin na nemi gafaranki ban samu ba, kunya kuma ta sa na kasa neman gidan nan. Ubangiji ya jarabeceni da Soyayyar Habib da duk abin da ya yi mini na kasa cire shi a raina shi na yi ta jira yana dawowa da nadamarsa na ƙarbe shi, ni da shi mu muka faro komai dole tare za mu karkare shi, fatanmu mu haɗu dake mu ba ki hakuri Habib ya samu labarin kin yi aure kina auran ɗan uwanki ɗan Sarkin Daura daga nan muka san kin yi mana nisa, wani matashi ne a anguwan nan Habib ya sa ya saka masa ido duk ranar da ya ganki ya faɗa masa domin mu samu damar neman gafaran ki, sai kawai ya kira sa yana faɗa masa Baffa ya rasu da shi aka yi jana'izar Baffa sannan aka raka shi har gidan sa na gaskiya. Mun bari ne sai zukata sun sanyaya sannan muka zo, ki yi hakuri ki yafe mana wallahi Habib ya yi nadama kuma duk abin da ya yi miki da shawarata in akwai wanda za ki fi ganin laifin sa ne ni ce Ummu Salma ni ce silan komai."
Ta ƙarishe faɗa cikin kuka, kowa a falon jikinsa ya yi sanyi. Shamsiya kuka take yi kamar ranta zai fita amma Umma Salma ta kasa magana itama hawayen take yi.
Ammah ce ta juya tana kallon Umma Salma.
"Ki yi hakuri ki yafe musu, a daran da Baffa zai rasu ya yi mana wannan tunasarwa ya ce muma muna laifi amma Ubangiji ya yafe mana sannan ya ce mu zama masu afuwa da yafiya domin Allah na tare da masu hakuri."
Umna Balki ta jinjina kai tana faÉ—in gaskiya ne ita da Ummin ikki.
Ummu Salma ta runtse ido ta buÉ—e, tun da aka ce Allah sannan aka kira sunan Baffa an gama magana
Za ta yafe musu amma ba ta son wata alaka ta sake haÉ—a su har abada.
Murya a shaƙe ta ce komai ya wuce ta yafe.
"Mun gode Ummu Salma Allah ya saka da alheri."
Ta amsa da Amin tana kallon Shamsiya. Shamsiya ce ta koma haka? Lalle rayuwa kenan ta tuna a baya ba ta da ƙawar da ta fita sai Baɗɗo amma yau an wayi gari Shamsiya ta ba da gudummuwa wajen jefa rayuwarta cikin baƙinciki.
Shamsiya ta riƙe hannuwan Ummu Salma da karfi domin kar ta ƙwace.
"Mun gode sosai Ubangiji ya cigaba da dauwamar da rayuwarki cikin farinciki, kin ga yadda rayuwa ta yi danmu ko? Na kasa haihuwa Umma Salma itama Habiba ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba tunda Habib ya aure ta."
Ta gama fada tana juyawa sannan ta nuna Habiba.
"ÆŠiyar Baba Usman ce ita ya aura bayan mun rabu."
Ummu Salma ta bi ta da kallo, sai da Shamsiya ta yi magana sannan ta gane ta.
Ta san ta tabbas ɗiyar Baba Usman ce suka kalli juna Ummu Salma ta kauda kanta kawai, rai suka wulaƙanta kuma wannan haƙƙin sai ya tambaye su amma ko Habib zai mutu bai haihu ba ne, ba za ta ba shi Hanan ba
Kowa ya É—auka za su yi maganar Hanan amma ba su yi ba sai godiya da suke yi suna shirin tafiya.
Ammah ta ce su dakata sannan ta kalli Ummu Salma wacce tunda ta ce su dakata gabanta ke zikiri.
"Ina É—iyar su?
Received at 11:37Reactions: ⤠8, 🔥 1

Ba Ummu Salma ba hatta su Hamma Jibo sun sha mamaki, sun É—auka daga neman gafara shike nan cikin nan cewa ya yi baya so, suma kunya ce ai ta hana su tambayan labarin cikin LamiÉ—o ya ji maganar Ammah a zuciyarsa amma ko a fuska bai nuna wani alamu ba.
"Ammah ba fa É—iyarsu ba domin cewa ya yi baya so ya bar ma Auta wannan cikin halak malak."
Hamma Abdullahi ya sake maimaitawa.
Sai Alhaji Sherif ya kalli Baba Usman, shima ya kalle shi cikin mamaki domin ba su gane kan maganar ba. Habib kuma jin sa yake yi wani iri yana ganin a kamar mafarki daman kunya ce da nauyi ya sa bai tambayi cikin jikin Umma Salma ba amma abin na ran shi cewa ya yi ba zai taɓa tambaya ba.
"Alhaji cikin da Umma Salma ta fita da shi ta haife shi, mace ce sunan ta Hannatu kamar Habibu ne yana ƙarami "
Gwaggo ta faÉ—a ma Alhaji Sherif tana dariya lokaci É—aya da hawaye.
Shamsiya kusa da Habib ta koma tana faÉ—a masa Umma Salma ta haifa masa yarinya mai kama da shi
Ya kasa magana bakin shi da jikinsa ma rawa suke yi.
"Na sani, amma Baffa ya ce ko bayan ran shi mu haÉ—a Hannnatu da mahafinta tare da ahalinsa."
"Why Baffa?
"Me ya sa?
Su Hamma Abdulrahaman ke tambayan kan su.
Su Hamma Jibo kuma sun yi shuru domin ta wani fannin sun hango manufar Baffa
Ammah ta kalli BaÉ—É—o sannan ta ce ta É—auko Hannan ta kawo musu itama duk jikinta ya yi sanyi.
"Barci fa take yi Ammah."
Mami ta faÉ—a domin itama a É—auko musu Hanan din bai yi mata daÉ—i ba
"Ku taso ta."
Ammah ta faɗa kai tsaye. Sai kowa ya kasa motsi barin ma Ummu Salma da ta ji kamar numfashinta zai ɗauke me Ammah take nufi? A ɗauko Hanan a bawa Habib ina ba zai saɓu ba yau ko duniya za ta haɗe ba za ta bari Habib ya ga Hanan ba, ballatana har ya taɓa jikinta.
Baɗɗo ta miƙe ta wuce ɗaki ta ɗauko Hanan dake barci, tana ɗauko ta kuma kamar ta sani ta farka tana mutsike idanuwana.
Ummu Salma ta ji kamar an zare mata lakka, lokacin da Ammah ta ce wai Baɗɗo ta miƙa Hanan ga su Habib.
Ba ta san ina ta samu wannan karfin ba, ganin ta kawai ta yi a gaban Baɗɗo ta warce Hannan ta ƙanƙameta a jikinta.
"Ba zai taɓa mini ƴa ba, shi ya ce ba ya so ya bar mini. Saboda haka har abada ta haramta a matsayin jininsa."
Take faɗa tana kuka, Mami ta miƙe tana yi mata magana ta matsa baya ta fashe da kuka.
"Mami har da ke! Raba ni da ƴa ta za su yi wallahi ƙwace ta za su yi"
Tana wani irin gunjin kuka.
Nan fa su Alhaji Sherif suma suka mimmiƙe cikin tashin hankali.
"Ba wanda zai kwace miki Æ´a' ai tunda ya ce ba ya so ya bar miki ta ki ce har abada.'
Alhaji Sherif ke faÉ—a cikin sigan lallashi amma Ummu Salma ta kamkame Hanan ta hana su, su ganta
Hamma Jibo ya yi magana ta sake fashe masa da kuka har tana ya taimake ta.
Ko zafin jikinta ba ta ji yadda take jijjiga ga kuka.
"Ki saki yarinyar nan Ummu Salma, ba ki ji me na ce ba ne?.
Ammah ta sake magana amma Ummu Salma ba ta amince ba da gudu ta nufi Hamma LamiÉ—o ta duka a gaban shi.
"Hamma ka saka baki, ka faÉ—a ma Ammah kai ne Baban Hanan, ka hana ta ba su ita."
Take faÉ—a tana wani irin kuka mai ban tausayi
Baya son kukanta shima hukuncin Ammah bai yi masa ba amma tunda umarninta ne ba zai ja da ita ba.
"Is okay amma dai yanzu ki yi abin da ta ce, miƙa ma Aisha Hanan ɗin."