Sashe 57
Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mamaki ya kama su, Ummu Salma na ganin kayan jikin dogarin Daura ta faɗo mata arai sai ta kalli Baɗɗo tana faɗa mata baƙi ne daga Masarauta
Suka rankwafa suna gaishe da Ummu Salma ta amsa sannan suka shiga cikin gida.
Takalmin maza suka gani a ƙofar ɗakin Ammah takalmin mai kyau ne irin na masu Sarauta Ummu Salma ta kalli takalmi sannan ta juya tana kallon Baɗɗo.
"Hamma ne"
Ta faɗa da sauri kafin ta yi saurin faɗawa falon Mami har mayafin ta na yin ƙasa,
Zuciyanta na bugawa, wanda take tunanin ganin shi ne ta gani, yana zaune a saman kujera cikin alkeybba da rawani ga wata sanda a hannun shi irin ta masu mulki, rawanin shi fari ne har bakinsa da hancinsa ba a gani idanuwansa ne kawai a waje. Ammah na gefen shi itama a saman kujera ta sadda kai ƙasa kwarjininsa da ƙamshin turaren sun cika falon gabaɗaya.
Cak ta tsaya ta kasa gaba ballatana baya. Ba ta taɓa tunanin za ta ganshi a wannan lokacin ba.
Baɗɗo da Harira suka shigo ai ganin shi ya sa Harira ta yi ƙasa tana gaisuwa.
BaÉ—É—o ma ta rankwafa Sarki ne fa ba abun wasa ba ne. Allah ya sa Banafsha na bayan Harira a goye
"Kika tsaya ma mutane a kai kuma."
Ammah ta faÉ—a tana hararan Ummu Salma ganin ta tsaya kawai ta kafe LamiÉ—o da idanuwana shima kallonta yake yi ta cikin rawaninsa yana jin zuciyarsa na yin É—umi.
Daman ya ce ba zai faÉ—a mata ba, bai yi tunanin zuwan na shi zai tabbata ba ne. Sai ga shi kuma ya tabbata irin yadda kewar Ummu Salma ya yi masa rugu rugu in zai furta ma ba za a amince ba.
"Ki ƙariso ki gaishe shi, sun fi awa da zuwa kina can kun fita tun safe ba ku dawo ba."
Ammah ta sake faÉ—a tana sake hararan Ummu Salama.
Da ta kasa ma tafiya kafafunta na rawa itama ƙwarjini Hamma ya yi mata sosai sai ta ke jin sa kamar baƙo a gare ta.
Da ƙyar ta samu ƙarisawa gaban shi, sai kawai ta ji ƙafafunta sun rinjayeta ta zube a gaban shi.
"Hamma"
Sai kuma da ta faÉ—a ta tuna da sauri ta rufe bakinta tana kallon Ammah dake hararanta.
"Ranka ya daÉ—e."
"Sannu da zuwa."
Ta faɗa a rarrabe sai kuma ta sadda kanta ƙasa tana wasa da gefen mayafinta.
Yana kallonta yana jin wani iri a jikinsa Ummu Salma ta canza ya ji daÉ—in ganinta ta yi kiba.
"Mun same ku lafiya?
Ya faɗa a ginshiƙe muryansa a kausashe kamaar yadda ya saba amma wannan karon a ƙasaice.
Ta amsa da lafiya lau tana satar kallon shi.
Ammah ta mike ta isa ga Harira ta karɓo Banafsha.
Ta kai ma Lamiɗo har in da yake zaune ya karɓeta yana yi ma Ammah sannu tana ba shi ta bar bangaren daman Baɗɗo da Harira sun fice, suna bangaren Baɗɗo ita kuma Ammah sai ta shiga kitchen ɗin tsakar gida kamar za ta yi wani abu nan ko ba abin da za ta yi, ta ba su damar ganawa ne.
Bayan fitan Ammah Lamiɗo ya ajiye sandar hannunsa a gefe ya riƙe Banafsha dakyau a cikin jikinsa yana kallonta barci take yi amma kamar ta sani sai da ta farka tana ta cilla kafafu irin na jarirai ya saka ɗan yatsan shi na hannun dama a cikin na ta yatsan na hannun dama yana kallonta da wani irin soyayya ta ɗa da mahaifi.
Ummu Salma na zaune tana satar kallon shi tana mirmishi farinciki ya cika ta.
Received at 15:21Reactions: ⤠12, 👠2
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Hamma ka daÉ—e da zuwa ne?
"Shi ne ba ka faÉ—a mini ba?
Ta gama fada har tana zumbura masa baki ya kalleta sau ɗaya ya kawar dakai in tana masa wannan shagwaɓar da za ta saka ya kasa riƙe kansa.
"Tafiyar ce sai yau ta tabbata."
"Na fara sauka a fadar sarkin Adamawa ne, ba daÉ—ewa zan yi ba yanzu za mu tafi amma zamu biya gidan Gwamna kafin mu tafi."
Ya gama faÉ—a yana sake wasa da hannun Banafsha dake hannunsa.
"Na zo ganin ku ne."
"Ke da takwaran Mami."
Ya furta cikin wani irin amo, amon da ya shiga jinin jikinta ya sakar mata wani kasala.
"Na gan ku."
"Na ji daÉ—i."
Ya gama faÉ—a ya É—an kallon Ummu Salama.
Itama shi take kallo cikin wani yanayi.
"Come here."
Ya furta yana cigaba da kallonta, sannan lokaci ɗaya yana nuna mata gefen shi, kamar daman tana jiran ya furta ta tashi da sauri ta ƙarisa gare shi ta zauna a gefen shi, tana zama ta rinjayi jikinta zuwa gefen kafaɗan shi lokaci ɗaya tana kwantar da kanta a kafaɗar na shi a saman alkeybban jikinsa da rawaninsa.
"Na yi kewar ka."
Ta gama faɗa tana turo hannunta ta sagalen hannayen shi ta riƙe shi, ga shi gidan ba kowa su Hamma Saddam duk suna wajen aiki.
Kallonta ya yi ta cikin rawaninsa.
"I miss you too.'
A kalaman shi, ta ji gaskiyan abin da ya faÉ—a.
Ta yi masa mirmishi, ta kalli Banafsha, dake hannunsa itama sai ta miƙa yatsunta suka sarke yatsun yarinyar a tare sau uku.
"Ka ga takawaran Mami ko?
Ta furta tana kallon shi, ya ɗan gyara zaman shi kaɗan. Ya saka hannu ya kama hannun Ummu Salma, sannan suka kama hannun Banafsha a tare suka jimƙe.
"Na ganta. Kin iya haihuwa. Allah ya raya mana ita. Ubangiji ya yi mata albarka ita da sauran yan'uwanta gabaÉ—aya."
Ta amsa da Amin Amin. Ummu Salma ta ga hannuwansu ya yi kyau sai ta kalle shi.
"Hamma ina wayarka?
Kafin ma ya yi magana ta ji tudun waya a jikin rigar saƙin dake jikinsa nan ta zura hannu a cikin akeybban ta zura can ta ciki ta ɗauko wayar.
Ta ga akwai password kafin ta tambaya ya faÉ—a mata shekaran haihuwansa ne.
Ta buÉ—e wayar ta É—auki hannayensu hotuna, sannan ta yi musu selfie.
Ta haÉ—e kanta tare da na LamiÉ—o shi yana cikin rawani ta É—auke su a tare.
Sannan ta tashi tsaye ta ɗauke shi yana rike da Banafsha sai da ya gaji ya ce mata ta zo ta zauna sun kusa tafiya sannan ta haƙura da hotunan ta dawo ta zauna
"Me kika za a dinga kiran ta?
"Banafsha."
Ya kalleta amma bai yi magana ba ta fara masa bayanin sunan mai kyau ne duk da ta faɗa masa ta chart wataƙila ma hankalin shi bai kai can ba. Tunda yanzu abubuwa sun ƙaru.
"Banafsha."
Ya maimaita sunan sai da gefe da gefen bakin shi ya motsa.
"Nice name."
"Sunan ya yi daɗi Baɗɗo ce ta zaɓa mata."
Ya jita amma bai yi magana ba
"Ba yau su Anty Bilkisu za su je Daura ba?
"Su na can ma"
Ta kalle shi cikin mamaki. Ta san dai a yau É—in za su isa amma ta yi mamakin ashe sun isa da wuri.
"Jirgin safe suka biyo."
Ya sake amsa mata tambayarta tun kafin ma ta yi tambayar.
"Allah sarki muma gobe muna tafe."
Ya tambayeta tsarin tafiyar ta fara masa bayani.
"Akwai jirgin da za ku bi da ƙarfe goma na safe, mutane ashirin kawai sauran akwai mota."
Ta amsa mishi da cewa su Hamma Abdullahi sun ce a mota za su isa Daura ranar Jumma'a.
"Me ya sa?
"Sun ce suna son ganin gari."
Ya É—an jinjina kai.
"Ba wata matsala?
"Babu komai Hamma."
"Are you sure?
Ya sake tambayata sai ta amsa masa da cewa komai suna da shi sun siya.
"Allah ya saka da alheri."
Ya amsa da Amin a saman labɓan sa.
"Ammah fa ta ce ba za ta je ba "
"Na yi magana da ita. Za ku taho tare in sha Allahu "
"Ta amince?
Ta tambaya tana É—an ware idanuwana.
Ya lumshe idanuwana ya buÉ—e.
"Uwata ce fa, za ta je ta sanya mini albarka."
"Haka ne É—an Ammah"
Ta faÉ—a tana dariya hakoranta sun bayyana a waje ya shagala da kallonta.
Itama shi take kallo zukatansu na fizgansu akan junan su.
Ummu Salma ta bi shawaran zuciyarta ta barta ta rinjayi gangar jikinta sai ga shi ta na sumbatar gefen fuskar LamiÉ—o, ya juyo ya kalleta ta sumbaci bakinsa ta cikin rawani.
Ya kanƙance idanuwana yana kallonta.
"Kar ki taƙale ni."
"Ba anan ba."
Received at 15:21Reactions: ⤠12, 😠2

Ya furta a rarrabe, ba ta ƙyale shi ba sai ji kawai ya yi ta tallabo kan shi ta zare rawanin ta yi kasa da shi, yana mata gargaɗi da idanuwansa ta yi kamar ba ta gani ba ta fara sumbatar bakin shi, shima kamar yana jira ya tarbi harshenta ya kuma saka hannu ya riƙe kugunta da hannu ɗaya, dayan hannun kuma ya riƙe Banafsha kar ta faɗi.
Sai ga Mai Daura da Sarauniyar Daurama suna masu sumbatr juna cikin shauƙi da soyayya a falon Ammah, na sama da mintina biyar sannan Ummu Salma ta saurara ta lafe a ƙirjinsa tana mayar da numfashi. shima numfashin yake mayarwa a jere amma shi a saukaƙe yana so ya daidaita yanayinsa.
"Kin cire ma Sarki rawani ko?
Ya faÉ—a yana jin zuciyarsa na matsewa waje É—aya.
Yar dariya ta yi amma ba ta yi magana ba.
"A gaban É—iyata kike sumbata na Ummu Salama?
"Muke sumbatar juna dai?
"Kuma a falon Ammah na."
"Ni ba ruwana, har da kai."
"Sai da na ce kar ki yi. I warned you kafin ki fara."
"Da na fara ai ba ka ture ni ba."
"Kenan kana so?
Ta faÉ—a tana kallon fuskar shi.
"Ina so."
"Sosaii.. ."
Ya ja sosai ɗin yana jin wani iri, yana buƙatarta amma kuma ba lokacin hakan ba ne yanzu.
"Ai Anty Bilkisu na nan yau."
Ta faɗa tana ƙoƙarin danne yanayinta.
Sai ya yi kamar bai ji ba ya kawar da maganar da cewa ta gyara masa rawaninsa ta saka hannu ta ja sama ta rufe bakin da hancin.
"Ya yi? Kar Sarki ya ji kunya fa."
"Ba wani kunya ya yi kyau, har ya fi ma wanda ka zo da shi."