← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 75

Sashe 17

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya faɗa yana kallonta lokaci ɗaya da ƙokarin riƙe ta, wani kallo take yi masa na kaima har da kai za a raba ni da farincikina kawai sai ta tashi ta manta akwai mikin ɗinki a jikinta bai gama warkewa ba ta juya ta saka Hanan a baya wacce ta yi zuru zuru har ta fara kuka ganin abin da ke faruwa.

Habib na tsaye amma kafafunsa rawa suke yi.
Shamsiya ta duka a gaban Ummu Salma.

"Ba ƙwace ta za mu yi ba Ummu Salma ganin ta kawai za mu yi."

"Ba za ku ganta ba. Ba ke kika ce a zubar da cikin ba shi kuma ya bi abin da kike so ba, ya so Hanan ba ta rayu ba Ubangiji ne ya fisa wallahi ba za ku taɓa ƴata ba ku je na yafe muku amma har abada kar ku sake tunkaran in da nake "

Nufinta ta gudu ɗaki ta rufe Ammah ta miƙe tana sake daka matsa tsawa.

"Kar ki matsa daga in da kike."
Received at 11:37Reactions: ❤ 8, 👍 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Maganar Ammah ya hana ta motsi amma ba ta daina gunjin kuka ba
Mami tausayi ya kamata sai hawaye haka ma BaÉ—do da Ummin ikki.

"Jamila bi ta a hankali."

In ji Umma Balki cikin tausayawa.

"Ai a hankali na bi ta da farko na ga za ta yi mana hauka "

Ammah ta faɗa,sannan ta ƙarisa kusa da Umma Salma.

"Ba ki da hankali ne daga cewa za su ga yarinya sai ki fara ma mutane hauka? Ba ni ita."

Ammah ta gama faÉ—a tana mija mata hannu.
Amma ina Umma Salma ta kasa.

"Ba za ki sauke ta ba?

"Ammah."

"Na ce ki sauke ta kar in mare ki anan wajen"

Ammah ta fusata ranta ya ɓaci, kan ta farau haihuwa ji wani haukar da take yi.

"Kan ki farau haihuwa ko nan duk ba mu haihu ba ne sai ke? Daga cewa a kawo yarinya su ganta sai ki fara mana hauka in aka barki da ita za ki iya ba ta sunan Uba ne? Koma me ya faru shi ne mahaifinta mun sani kin sani suma sun sa ni."

"Ammah Hamma LamiÉ—o ne mahaifinta."

Ummu Salma ta faÉ—a cikin gunjin kuka kuma ba ta sauke Hanan É—in daga bayanta ba.

"Na ji shima mahaifinta ne amma kowa ya san ba shi ya haife ta ba. Cewa fa kawai na yi za su ganta ba tafiya da ita na ce za su yi ba amma tunda na ga abin da kika yi na ma fasa."

Ammah ta juya tana kallon BaÉ—É—o.

"Aisha shiga ciki ki haÉ—a kayan Hannatu ki ba ma mahaifinta su tafi da ita ta kwanan musu biyu."

"Ammah."

Ummu Salma ta kira sunanta da karfi tana kuka.

"Ammah don Allah ki yi haƙuri."

"Wallahi sai sun tafi da ita, in ta ga dama ta mutu saboda haka, shanshanci kawai kika rasa ma uba kika dangana balle wata Æ´a?

Yadda Ammah ke faÉ—a kowa yasan ranta ya baci shi ya sa ko su Hamma Jibo ba su yi gaddama ba.
Gwaggo ne da Alhaji Sherif ke ba da hakuri.

Baɗɗo ko ta shiga cikin ɗaki a wata ƙaramar jaka ta haɗa ma Hanan kaya kala biyar da komai da komai ta zage ta fito, tun kafin ta miƙa ma Shamsiya ta yi saurin karɓan kayan Hanan kuma Ammah ta sauke ta daga bayan Ummu Salma, tana kuka Hanan na kuka ta tura ta Shamsiya ta ɗauketa itama tana kuka tana dariya.

"Mun gode Ammah, za mu dawo da ita in sha Allahu."

Habib kuma yana kallon Hanan yana kuka, daga karshe ma fita ya yi daga falon daga gidan gabaÉ—aya ya fita waje ya je can yana kuka shi kaÉ—ai. Nadama ta kara kama shi yanzu cikin da ya so ya salwantar da karfin tsiya ita ce Hanan da ya ke gani mai kama da shi.

A cikin falon Ammah kuwa Gwaggo na faÉ—in ba sai an yi haka ba.
A bar Hanan kawai in an kwana biyu sai ta je kowa ya ganta amma yanzu tunda uwar babu daÉ—i ta zauna tare da mahaifiyarta shima Alhaji Sherif haka ya ce.

"A'a ku je da ita, itama ba daÉ—ewa za su yi ba za ta bi mijinta su koma Lagos. Wannan kukan da take yi na jaririn da ta haifa ba rai ne kwana biyu da rasuwan Baffa."

Ammah ta faÉ—a musu, domin ita a ganin ta shi ya sanya Ummu Salma shiga wannan halin nan Gwaggo ta dinga addu'an Allah ya kawo mai tsayawa
Shamsiya kuma tuni ta yi waje ɗauke da Hanan da take ta kuka har tana faɗin ta daina kuka nima maman ki ce, Baɗɗo ta dinga hararanta kamar idanuwanta za su faɗo ƙasa.

Habiba ta bi bayanta, ita tausayin Umma Salma ta ji bai kamata a ji tausayin Habib ba.
Fitar Shamsiya da Hanan tana kuka ya fito da su Adda Safina da Islam da Harira.
Suka ga wata ta fita da Hanan suka shigo falon Ammah nan suka ga Umma Salma ta faÉ—i a tsakiyar falon Ammah tana gunjin kuka.

"Wayyo Allah na an cuce ni."

Haka take faÉ—a kamar ta zare, a lokacin kukan rashin Baffa take yi, da kukan rashin jaririnta yanzu a ce kuma an raba ta da Hanan

"Ba ma wanda ke sona sai Baffa wayyo Baffa, Allah ya jiƙan ka da kana nan da ba ka bari an cuce ni ba."

Take faÉ—a tana birgima tana kuka Mami na yi mata maganar ta tashi, ta manta akwai miki a jikinta amma ba ta ji ba. Har Hamma Jibo ya yi mata magana Hamma Kabiru har tsawa ya yi mata amma ba ta ji ba.
Ran Ammah ya kai kololuwa wajen ɓaci, har Umma Balki sai da ta yi magana Umma Salma ta duƙa tana kokarin tayar da ita amma ba ta ji ba sai ma fizge jikinta da ta yi tana cigaba da kuka.

Ammah ta kalleta wasu hawaye suka ziraro mata.

"Yau da ko wata Baffa bai yi da rasuwa ba har za ki fara tona mini asiri Ummu Salama? Ni ce na cucen ki kenan?
Received at 11:37Reactions: ❤ 8, 😱 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Ammah kin cuce ni, Hanan kaÉ—ai gare ni kika raba ni da ita."

"Are you Mad?

"Will you keep quiet."

A tare ya yi magana cikin tsawa lokaci ɗaya yana miƙewa. Sai da ta yi ɗif da kukanta domin tsawan Hamma Lamiɗo mai razanarwa ce.
Tun É—azu yake ganin abin da take yi ya É—auke kan shi, duk da shima hukuncin Ammah ya yi masa tsauri amma ba zai iya gaddama da ita ba.

Kowa ya yi mata magana amma ba ta ji ba, har tana cewa wai Ammah ce ta cuce ta. Me take so a yi mata? Ko can gidan take son komawa saboda an tafi Hanan.

"Yauwa gwara ka yi mata  magana tunda mu ta ƙi jin namu."

In ji Ummin ikki itama ranta ya ɓaci. Haba Ummu Salma kuma ta fara fita daga hayyacinta.

"Sakarci ne kawai ku yi mata dai a hankali."

Umma Balki take faÉ—a domin tausayi Ummu Salman ke ba ta. Ammah kuma kuka ta fashe da shi ta koma ta zauna

"Allah ya jiƙan ka Baffa, ka tafi ka bar ni yau ga shi Auta na cewa na cuce ta."

Kukan da Ammah take yi ya É—aga musu hankali.
Ummu Balki na faÉ—in ta daina kuka wannan ba wani abu ba ne, ita Umma Salma duk cikin rashin da aka yi mata ne ta faÉ—i haka amma ba cikin hayyacinta take ba Mami kuma ta duka tana ba ma Umma baki da hakurin kan ta tashi.

Hamma Kabiru ya ce su ƙyaleta gwara ma da Ammah ta yi haka ko gabaɗaya ma za su karɓi Hanan ɗin sai ta mutu don ubanta.

"Ummu Salma me ke damun ki? Wannan ai sakarci ne"

In ji Hamma Jibo yana mata faɗa. Lamiɗo kuma yana tsaye kawai yana huci ga cewar da ta yi Ammah ta cuce ta sannan ga abin da take yi sai kawai zuciyarsa ta haska masa Habib ɗin take so, da za a ba ta zaɓi shi za ta zaɓa saboda Hanan.

Ganin Mami da Baɗɗo suna ta lallashinta amma ta ki yin shuru ya sa Lamiɗo ya ce duk su ƙyaleta.

Cewa ya yi ta miƙe ta zauna. Ta ƙi tashi ya sake daka mata tsawa da sauri ta miƙe tana rufe idanuwanta hawaye na sake kece mata.

"Ka yi mata a hankali mana."
Mami ta faɗa ganin ya harzuƙa Ummu Salma kuma tana cikin wani halin da za a tausaya mata.

"Mami Ammah ce fa ta yi magana, ta yi mata gaddama a gaban mutane ta kyauta abin da ta yi?

Ya faÉ—a yana nuna ta da yatsa hannunshi na hagu.

"Ko ba ta so hukuncin ba tunda Ammah ta yi mata umarni me ya sa ta yi gaddama is she is ok? Bayan kuma ta kunyata ta a gaban mutane yanzu kuma look at her.? Kina ji fa ta ce wai Ammah ta cuce ta! Ammah ce za ta cuce ta?

Yanayin yadda yake magana ya sa kowa ya san a fusace yake.

"Ba ta kyauta ba. Amma a yi haƙuri."

In ji Umma Balki, Mami kuma cewa ta yi ya yi shuru kawai tunda dai ya faru kuma ba cikin hayyacinta ta yi ba.

"Ga zafin rasuwar Baffa ga na rasa jaririnta rana tsaka kuma ga Hanan dole za ta rikice."

"To ta tashi ta bi su can, tunda Ammah ta cuce ta. Ta bi su can if she want to stay with her Daughter sai na sake ta ta je ta aure shi sai ta samu daman zama tare da Hanan sosai."

Cak kukan Umma Salma ya tsaya. Ta ɗago da jajayen idanuwanta tana kallon Lamiɗo cikin ido, yau ba kallon soyayya yake yi mata ba wani irin kallo ne da ya kusa sanyata bugun zuciya ta ɗauka shi zai fi kowa fahimtarta ta ɗauka zai fi kowa sanin yanayinta baƙincikinta ɗaya yadda ya kasa gane halin da take ciki
Chapter 17 · 0% Book details