Sashe 61
Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba faɗa masa ta yi ba ya fahimci ta ɗauka Ummu Salma na zuwa ne shi ya sa in ta kwana biyu sai ta ɗauke kafa sai bayan wani kwana biyun bai taɓa faɗa mata ai Ummu Salma ba ta zuwa ba, bai cika magana ba sannan ba ko wani ƙaramin abu ke saka shi magana ba.
Wayarsa ya É—auka ya kira Ummu Salma a jiya Bilkisu a wajensa ta kwana yana sane yau ba za ta zo ba. Ita kuma Ummu Salma a waya suka gaisa yau jiya ne kaÉ—ai suka haÉ—u da safe da ta zo gaishe shi ita da Banafsha.
Wayar har ta katse ba ta ɗauka ba, sai ya ƙyale ta a tunanin shi ta yi barci kamar ko ya sani ta yi barci domin da wuri suke kwanciya yanzu. Cikin barcin ta ji kiran wayar ta dake gefenta ko da ta farka wayar ta katse tana dubawa ta ga Hamma na sai ta watsake ta bi bayan kiran na shi.
Lokacin Bilkisu ya ke so ya kira ta kawo masa coffea mai zafi, yana so ya sha kafin ya kwanta. Wayar ta shiga ta É—auka ta fara gaishe shi kenan kiran Ummu Salma ya shigo a waiting call yana dubawa ya ga ita ce sai ya fasa faÉ—in abin da yaso ya faÉ—a.
"Kuna lafiya? How are my childreen?
Ta amsa masa da suna lafiya, É—azu ma suna tare da Sultan wani lokacin yana zama tare da shi a fada, ko kuma in zai je can wajen Mai martaba tare suke tafiya. Beena ce da Hanan jiya da Safe sun taho bangaren shi, su ne yake yini bai gan su ba.
Ya sauya maganarsa da cewa ya kira ya ji lafiyarta ne da ta yara ta ji daɗi. Daman tana zaune da waya ne amma tana tunanin shi yana can tare da Ummu Salma duk da abin ya fara mata sauƙi zafin kishin yana raguwa tunda Umman Kano ta ce ta dage da addu'a yanzu da za ta ga Ummu Salma ta ji zuciyarta ta fara zafi yanzu za ta fara kiran sunan Allah, sannan tana yawan addu'an Ubangiji ya rage mata zafin kishi tunda dai ta fahimci Ummu Salma ba za ta bar mata Lamiɗo ba gwara ta koyi yadda za ta rayu da ita a matsayin kishiyarta sai dai har abada ba za ta so ta ba.
Received at 19:42
6 people reacted with â¤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ya zura mata idanuwana yana kallonta.
Sai ta sadda kanta ƙasa.
"Hamma kar Anty Bilkisu ta zo ta ganni ba daɗi."
Ya yi mata wani kallon ƙasa ƙasa sannan ya ɗauke kansa kamar bai ji abin da ta ce ba.
"Ya aikin? Ka gaji ko?
Nan ma bai amsa mata ba.
"Na yi kewar ka Hamma "
Ta faɗa cikin shagwaɓa, kuma da gaske ya ji kewar shi a muryanta da ya kalleta sai ya ga idanuwanta har sun fara tara kwalla yana kallon fuskarta yana mai nacin kallonta kamar ya daɗe bai ganta ba yana jin zuciyarsa na warwarewa a kanta.
"Da gaske na yi kewar ka."
Ta sake faɗa tana lamgwaɓe masa kamar wata karamar yarinya.
"Yanzu bana ganin ka sosai, ka zama na mutane ba na Ummu Salma ita kaÉ—ai ba."
Ta gama fada tana masa fari, sai da ta kusa saka shi dariya ya yi maza ya kame Hattara dai Sarki ne fa.
Mug É—in hannun shi ya ajiye a saman teburin dake gaban shi na tangaran.
Ta janyo jikinta zuwa wajen kafafunsa ta kama da duka hannuwanta ta rumgume a ƙirjinta
"Yaushe rabon da mu yi hira! Hammaaaaa"
Ta ja sautin sunan sai da ya ji a zuciyarsa jikinsa ya É—au É—umi ta saka kanta a tsakanin kafafunsa kamar wata yarinya.
"Har na fara rama saboda rashin ka."
Ta gama faÉ—a tana sake tusa kanta a tsakanin kafafunsa nenan ta birkita shi take yi, ya yi saurin matse kafafunsa ya saka hannu ya jawo kanta sai kawai ta É—ora kan a saman kafafunshi tana sauke masa ajiyar zuciya.
"Hamma."
Ya ƙi magana ta sake kiran shi.
"Hamma na."
Nan ma ya yi mata shuru kawai.
Ta ɗago tana kallon shi ya ɗauke kansa sama yana wani ginshiƙa.
"Hammaaaaaaaaaa."
Ta ja sautin sosai sai da ya kalleta bai shirya ba.
Sai kawai ta tashi ta haye saman cinyarsa ta yi É—are dare
"Hamma."
Ta sake kiran shi tana tallabo fuskar shi, suna kallon juna cikin idanuwansa.
"Hamma"
"Ummu Salama."
Ya kira sunanta cikin ƙosawa.
"Ni dai ka amsa."
"Me?
"Hamma na."
Sai da ya É—an juya bakin shi yana so ya yi dariya cikin zuciyarsa ya na jin salama.
"Na'am"
"Shike nan?
Ya faÉ—a yana kafe ta da idanuwana, sai ta yi masa mirmishi ta sumbaci bakin shi.
"Ba ka yi kewata ba ne?
"A'a."
Ya bata amsa kai tsaye ta kalle shi ta yi masa narai narai kamar za ta yi kuka.
"Ni ko?
"Ba komai to."
Ta gama faɗa tana ƙokarin sauka daga kafafunsa ya sanya hannu ya jawo ta, ta faɗo saman ƙirjinsa ya rumgumeta da tattausan hannayensa zuwa faffaɗan kirjinsa a tare suka sauke numfashi, kowa na jin zuciyarsa na ɗaukan ɗumi na rashin ɗan uwansa sun jima a haka suna jin bugun zuciyoyin junan su.
"Hamma."
"Uhm."
"Ina son ka."
Sai ya yi shuru kafin ya É—an gyara kafafunsa.
"Kin daina sona yanzu?
Da sauri ta kalle shi
"In ji waye?
"In ji ni."
Ya amsa mata kai tsaye.
"Tunda na zama Sarki. Kin fara guduna."
Ya faÉ—a yana kafeta da idanuwana ta zaro idanuwana tana kallon shi.
"Yes"
Ya faÉ—a yana kara haÉ—e rai, har yana wani É—auke kansa
"Yaushe ne na guje ka?
"Ba ga shi nan ba kin taɓa zuwa kin kwana a waje na tunda kika zo?
Ya tambayeta yana kafe ta da idanuwansa masu sanyata kasala da mutuwar jiki.
"Au wai daman shi ne kake magana."
Ta faÉ—a tana rufe baki, ya balla mata harara amma bai yi mgana ba ta kwashe masa da dariya sai ya yi fuska bai sake kallonta ba.
Ta rumgume shi tana faɗin" Hamma ma ina sonka abadan abadan har ƙarshen numfashina."
"Sweet mouth."
Ya faɗa yana ƙokarin cire ta daga jikinsa.
"Zo ki tafi,."
Ya faɗa a hankali ta maƙake masa yana so ya ɗago ta tana ƙara ƙamƙamesa.
Sai ya ƙyaleta sai don kanta ta sake shi tana shafa sajen shi.
"Ranka ya daÉ—e."
Ya ƙura mata idanuwana zaman ta a saman jikinsa har wani kasala ya sakar masa.
Ta kama hannuwansa ta damƙe a cikin na ta.
"Hamma."
"Saura kwana biyu na yi arba'in."
Bai tambaya ba amma yanayin kallon da yake yi mata na neman ƙarin bayani ne.
"Kasan in mace ta haihu a al'ada sai a ce sai ta yi arba'in sai ta koma ma miji, balle ni tunda ga Anty Balki shi ya sa ka ga ba na zuwa amma ba gudunka nake yi ba."
"To mene ne?
Ya tambaya yana kallonta.
"Ba ka gane ba?
Ta tambaye shi tana kallon shi.
"Ai ba umarnin Allah ba ne"
Ya ba ta amsa kai tsaye.
"Ke da al'ada kuke rayuwar aure ba addini ba?
Received at 19:42
12 people reacted with â¤

"Wa ya ce sai an yi kwana arba'in?
"Haka fa ake yi, ko su Ammah da Mami duk haka suka yi."
Ta ba shi amsa tana masa shagwaɓa.
"Ba dai Ammah na ba, da na zama É—an gata da ace zan samu rabin abin da Ammah take yi ma Baffa."
Kai tsaye ya yi maganarsa ta saki baki tana kallon shi.
"Ammah is a good wife. Ba ta taɓa barin kusa da Baffa ba. Da a ce Ammah ce ta riga Baffa rasuwa da har abada ba zai samu kamarta ba."
"Hamma."
Ta kira sunan shi.
"Ba wani Hamma, ba haka Ammah ke yi ba sai dai in Mamin ki."
Ya gama faɗa yana wani daƙuna fuska, dariya ta so kamata ganin ba wasa ya sa ta danne dariyanta.
"To na ga ina jinin haihuwa ne fa ga kuma ga Banafsha"
"To me zan miki? Ummu Salma kawai na ganki a kusa da ni a feel safe "
Yadda ya yi maganar daga ƙarƙashin zuciyarsa ne sai da jikinta ya yi sanyi.
"Sorry."
"Ka yi haƙuri."
"Kuma ba ki faÉ—a mini ba, kawai ba kya zuwa wajena."
"Kin kyauta?
"Ban kyauta ba."
Ta yi saurin amsa mishi tana wani lamgwabe kanta.
"Ban kyauta ba, ba zan ƙara ba."
Ya yi mata shuru, yana kokarin cewa ta É—aga shi, ta zo ta tafi dare ya yi.
"Anan zan kwana."
"A'a ni bana so."
Ya amsa mata ba wasa a maganarsa.
Ya miƙe tsaye tare da ita, ya juya ya ɗauko mata Banafsha, ya miƙa mata ta karɓa tana kallon shi.
"Hamma."
"Na ce fa ka yi haƙuri."
"Na haƙura"
"Ki bari sai kin yi arba'in."
Ya sake jadadda mata, kuma tunda ya furta ba zai sauya magana ba, sai kawai ta juya ta wuce ya bi bayanta har bakin bangaren shi sannan ya ba ma dogarawan dake gadin bangaren shi umarnin su yi mata rakiyar har sai ta shiga bangarenta suka amsa masa da girmamawa.
Sai da ta shiga bangarenta sannan suka koma, ta damu da fushin Hamman nata, da ta koma kafin ta kwanta sai da ta tura masa saƙon ban hakuri bai ba ta amsa ba a chart ma ta ga yana online ta yi masa saƙo bai buɗe ba sai ta ƙyale shi. Kuskurenta ɗaya da ba ta faɗa masa ba, ita ina ta san bai sani ba amma abin da ya ba ta mamaki Bilkisu ba ta zuwa ne? Ta so ta tambaye shi, sanin ba zai amsa mata ba shi yasa ba ta tambaya ba, sanin halin shi ba ya tattauna duk abin da ya shafi Bilkisu da ita, itama ba ta damu da ta sani ba, gwara haka kowa ya tsaya iya matsayinsa.