Sashe 60
Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lamiɗo na zaune ya hakimce ko iya ɗaga idanuwana baya yi saboda Sarauta da ƙasaita. Ubangiji ne in ya ce kum ya fakum ba wanda ya isa.
An yi hawan dawakai. Sarki ma ya hau farin dokinsa ya zagaya cikin gari ya dawo tare da tawagansa sannan Bilkisu Gimbiya ta sauke shi a saman doki. An yi ma Bilkisu naÉ—in Gimbiya bayan an saka mata alkeybba ita kuma Ummu Salma aka saka mata alkeybban a matsayin Sarauniyar Daurama.
Da yamma kuma Mami ta ce a kaita gidan Sarki Mai murabus ta duba shi, aka ba da mota aka kaita ita da su Islam da Hajiya Falmata tunda gobe baƙi za su yi halin su.
Yau ga Mai martaba tsohon Sarki Nasiru ga Fatima Batula sun haÉ—u a garin Daura ba a matsayin mata da miji ba, sai a matsayin Baba da Mama, iyayen Mai martaba Sarkin Daura Muhammad LamiÉ—o su Gimbiya Maimunatu sai kallo domin dai yanzu sun san kishin Fatima ma ba shi da amfani tana da mijinta.
Fulani ta yi mata karɓa na karramawa sosai domin ita tun bayan abin da ya faru komai ya wuce a matsayin y'a ta ɗauki Mami.
Da za su tafi Tsohon Sarki ya yi ma Faruk da Islam kyautar kuÉ—aÉ—e Fulani ma haka ta yi musu kyauta haka Hajiya Falmata ma ta samu farar takarda cike da sabbin kuÉ—aÉ—e.
Ranar litini baƙi suka fara watsewa. Mami ta riga kowa tafiya Daddy ma da ya zo a ranar asabar ya koma. Tawagan mutanen Adamawa duka jirgi Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo ya ɗau nauyin su har da su Shamsiya da kowa da kowa. Kowanne da abin arziki bayan abin rabo ga kuɗaɗen da Masarauta ta raka su da shi.
Ammah kuma tsohon Sarki ya sake biya mata kujeran Makka za ta sake komawa ta sauke farali.
Su Hamma Jibo duk sai da suka je suka kai gaisuwa kafin su tafi.
Received at 15:23
13 people reacted with â¤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Aka bar Ummu Salma da Banafsha da tarin dukiyar da suka tara. Tun da suka tafi Hadimai suke gyaran ko wani bangare. Ba su kaɗai ba har sauran dangin su na Daura suma sun koma da sha tara na arziƙi sai a lokacin suka ga Mami wasu ma ba su santa ba sai dai labarinta. Waɗanda suka santa ɗin iyayensu ne sun kuma rasu sai yara da jikoki an yi zumunci kuma sun ji daɗi kwarai.
Sun tafi sun bar Daura da Sarkin su Muhammad LamiÉ—o da matanshi tare ya'yan shi a cikin Masarautar Daura in da za su fuskanci Sabuwar rayuwa.
*Janafty*
Received at 15:23
12 people reacted with â¤

*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.
Alhamdulillah baƙin da suka zo Daura duk sun koma gidajensu cikin ƙoshin lafiya da aminci kowa na ta son barka tunda sun koma gidajensu da sha tara na arziƙi sai dai fatan Allah ya ta ya Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo riƙo Ubangiji ya ba shi sa'a ya kuma tsare shi.
A satin kaf duka platform na social media da manyan bloggers ɗin arewa hotunan Lamiɗo ne kawai ke yawo cikin shigar Sarauta ya yi kyau har ya gaji da kyau saboda shi ɗin mai kyau ne, yan comments section na ta faɗin albarkacin bakin su mafi yawancin su dai suna yabon kyau da zati ne irin na sabon Sarkin Daura wasu kuma suna masa laƙabi da matashin Sarki, suna ganin cancantarsa wasu kuma suna ganin kamar shekarunsa sun yi ƙanƙanta kowa dai na faɗin albarkacin bakinsa ba tunda ba wanda aka hana faɗin ra'ayinsa.
Ummu Salma ta kira duka danginta da suka zo ta yi musu bangajiya da godiya. Ita kaÉ—ai a bangarenta daga ita sai Harira sai Asabe da Banafsha Hanan na can bangaren Bilkisu ita da su Sultan da Beena amma kusan a bangaren Ummu Salma suke yini saboda Banafsha.
Daman ita Ummu Salma ba ta ce za ta karɓi Hanan ta dawo bangarenta ba. Ta san Lamiɗo ba ya son a raba ko makwamcin Beena da Hanan ne kuma tunda Bilkisun ba ta nuna komai ba ta cigaba da zama a can ba za ta taɓa mgana ba, a baya ma ta zauna tare da ita kuma ba abin da ya same ta ballanta ma yanzu da suke ƙarƙashin rufi ɗaya na gida ɗaya.
Tuni Mai martaba Lamiɗo ya miƙa a mulkinsa ya yi sabon naɗe naɗen hakimai ya sauya wasu sarakunan ƙauyaku sannan ya sauya masu sarautunsu.
Sannan an ƙaro hadimai da dogarai tare da dirobobin masarauta.
Ummu Salma an ba ta hadiman bangarenta sai ta naɗa Harira a matsayin shugabansu ita da Asabe. Bilkisu kuma daman Debora da Anitha sun taho bayan taron naɗi ta tabbata dai ba za ta barsu ba suma kuma ba za su barta ba, sun shigo har bangaren Ummu Salma sun gaisheta sun kuma ga Banafsha Debora ke faɗa ma Ummu Salma James da Baban Adila na can Lagos za su kula da gidaje da motocin dake can. Ummu Salma ta san daman ba za su tafi ba, yadda suke jin daɗin aiki a ƙarƙashin Hamma Lamiɗo ta san ko da suma sun amince zai ce ne su taho Masarauta su cigaba da aiki can ɗin ma da za su zauna ba duk wata suna da albashi sauran buƙatunsu ma ba zai taɓa gajiyawa ba. Kamar maigadinsu na Jimeta ne, shima aikin shi kawai ya kwana ya kula da gida amma tarin alherin da yake samu ta hannun Lamiɗo ko wani ma'aikacin gwammati sai haka.
Tuni Masarautar ta ragu, baƙi duk sun koma gidajensu har da na ƙasashen waje da suka taho. Yau sati ɗaya da yin taron naɗin nan, kimanin kwana talatin da takwas da haihuwan Ummu Salma saura kwana biyu su yi arba'in ta dage da kula da jikinta kamar yadda Mami ta faɗa mata in dai suka yi waya sannan ta dage da shan magungunar wajen Surayya Halin yau, domin ta kame ta yi tsam yadda Mai martaba zai manta cewa ta haifi Banafsha.
Ita tun da aka yi taron naɗin ba ta je bangaren Mai martaba ta kwana ba, ta kan je da safe kafin ya fita fada ta gaishe shi ta kai masa Banafsha wani lokacin kuma sai da daddare in ya shigo ta aiko jakadiya ta yi mata iso, in kuma ta je ba ta wani daɗewa take dawowa bangarenta duk da ta yi kewarsa amma tuna tana jego ya sa ba ta yi tunanin kwana a wajensa ba. Ta ɗauka Bilkisu na zuwa wajensa ganin bai taɓa mata magana ba, a tunanin ta ya san in mace ta na jego in tana da abokiyar zama ta kan ɗan ɗaga kafa da zuwa turaka amma ba addini ba ne al'ada ne kawai.
Shi kuma ya na ganin ba ta kwana a wajen sa in Bilkisu ta yi kwana biyu, ba ta sake zuwa sai bayan kwana biyu a tunaninta yana tare da Ummu Salma ne, shi kuma ba ta zuwa ko ma ta zo sai ya ga ta tafi ba ya son dogon magana ko tambayoyi shi ya sa bai tambaya ba. Sannan ga sha'anin mulkin da ya yi masa tsaye a rayuwarsa. Duk yadda ba ya son mulki sai da ya zo ya sarƙe shi a lokacin da bai yi tunani ba.
Received at 19:42

Duk yadda ya kai ga hasashen wahalan mulki ashe wasa yake yi sai da ya gan shi ya ciki ya tabbatar da wahalansa ya fi hasashensa yawa. Tunda Mai martaba tsohon Sarki ya yi murabus bai kwanta tun daga dare har wayewar gari yana barci ba, bai samu kebewa da iyalansa tun daga safe zuwa yamma ba. Bayan an yi taron naɗi kuma ba shi ma da lokacin kansa yana ta ganawa da sarakunan ƙauyaku da malamai da dattawan gari sannan jiya ya fita sun je wani ƙauye nan kusa da aka samu barkewan cutar amai da gudawa a dare ɗaya yara goma sha suka rasu, yau ɗin ma sai da yamma ya dawo fada ya biya wajen Mai martaba tsohon Sarki domin ba ya gudanar da komai sai da shawaransa kuma yana ganin amfanin haka.
Sai dare ya baro fada sun ci abincin dare tare da wakilan fada da Saleem da tare suke yini a fada, Mai martaba Lamiɗo ya yi masa masauƙi a cikin Masarauta wani lokacin ya kwana anan wani lokacin kuma ya koma gida, ya gama karatunsa yanzu aiki kawai ya ke jira, daman ya yi degree ɗin sa da farko ya dawo gida ya yi service sai ya koma domin ya haɗo masters ɗin shi yanzu kuma ya gama shi ya sa ya dawo gida.
Goma da wasu mintina ya iso bangaren shi.
Ya yi wanka ya saka sauƙaƙun kaya duk yadda ba ya shiri da zafi yanzu ya fara. Tunda yini yake cikin manya kaya da rawani.
Ya ƙoshi tunda sun ci abinci amma sai ya ji yana marmarin shan ruwan zafi a daran nan kafin ya kwanta kuma ma a ce Ummu Salma ce za ta dafa masa, ya samu saƙon ta, ta hannun jakadiya kuma itama ta yi masa test messages ta faɗa masa tana son a kawo mata kayan abinci a store ɗin bangarenta da cefane za ta dinga girki da kanta.
Ya ba da umarnin a yi mata yadda take so yana marmarin girkinta bakin shi na buƙatar ɗanɗanon abincinta da ya daɗe bai ci ba, sannan kuma ya yi kewarta, hirarta kawai yake so ya ji kafin ya kwanta ya rasa me yasa take gudun sa? Kwana biyu Bilkisu ke ɗebe masa kewar dare, to kuma kowa da abin da ya iya, ita ba ta iya hira ba shi kuma yana so a yi masa hira ya saurara ko da ba zai yi magana ba.