← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 129

Sashe 96

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

d'aukar me kayimun marar galihu ko.kuma me mi.kake nufi da ajeni a gidan nan da kayi kamar wace y'ar iska ....saurin katse.kiran md yayi gabansa na fad'uwa tsoransa Allah kada Ammy taji abunda zahra ta fad'a kallonta yayi fuska ba wasa ya ce "Zaman Aure kike?Tana binsa da wani banzan kallo ta ce " lallai kai baka da kunya ma.wlh har kana da bakin da zaka iya furta wannan Kalmar Wacece zatayi zaman Aure da mugu azzalumi Wanda baisan damuwar wani ba damuwar kansa kawai ya sani mayaudar....bata k'arasa fad'a abunda takeson Fad'a ba MD yayi sama da ita bai direta ko ina ba sai kan Bed yana shirin danneta ta k'walla Kara ta ce "Wlh tallahi ka sake kayimun wani Abu zanyi maka abunda ba a tab'a yi maka shi a rayuwa ba " banza MD yayi mata ya rungumota jikinta sosai tare da Fara Aika mata K'ananan sakwanni ganin zai birkitawa kansa lissafi gashi yayi alk'awarin bazan k'ara wani Abu da ita ba saboda cikin dake jikinta daidai kunnanta ya rada mata a hankali "ki kwanta kiyi bacci yanzu indai bakyaso wani Abu ya faru" Zahra najin haka ta Had'iye kukanta Batasan lokacin da wahalallen bacci yayi awon gaba da ita ba saida yaji saukar numfashinta tukwana ya sauke ajiyar zuciya ya zame a hankali saida ya sha ruwan liptop da lemon tsami tukwana ya samu bacci ya daukesa washegari zahra ta tashi bayan asuba dan ta makara salla shiko md koda yayi salla ya fita daga dakin ya koma nasa Bayan tayi alwala ta gabatar da salla Sosai ta rokawa mahaifinta samun lafiya dukda MD ya fad'a mata ansallamesa yaji sauk'i amma bata yarda ba Tana gama salla yunwa ta ciyota tsaki taja Dan yanzu wata irin jin yunwa takeji da taci kamar bataci ba hakan yasa yanzu ta daina masa zuciya da abinci Dan ita ke illatuwa kofa ta nufa tana turawa taji a rufe tsaki taja Dan sosai takejin haushin kulleta din da yake ko yaushe kamar a gidan yari tsaki taja tare da komawa ta zauna tana lazumi tana addu'ar Allah zubar da cikin nan dake jikinta ba ayi 30 minutes ba MD ya shigo d'auke da plate din wainar kwai kusan guda biyar sai cup din tea da bread a hannunsa kai tsaye gabanta ya nufa dasu a hankali ya ce "Good morning mummyn baby" Tsaki taja tare da kauda kai Dan murmushi yayi Dan ya saba da abun nata ya Aje kafinma ya ce ta ci tuni ta fara ci Dan yunwar data ciwo ta saida abun yaso basa Dariya ganin yanda ta murtuke takeci kamar an mata dole cewa yayi "ki gama ki shirya muje Asibiti ayi miki scanning sannan ya kamata mu fara zuwa awo" wani banzan kallo tayi masa cike da takaici ta ce "Allah kiyaye Allah tsari gatari da saran shuka a tunaninka ni zanje Asibiti saboda lafiyar cikin nan Dana tsana Aiko Inma kana wannan tunanin tun wuri ka bari Dan wlh ba haihuwar....saurin kwabe mata baki yayi cikin bacin rai ya ce" Da Allah yiwa mutane shiru "Dogon tsaki Taja Wanda MD Inda sabo harya saba da tsakin nata wanda duk duniya bayan ammy babu wanda ya isa ya masa su wanje lafiya ta ce" Satoni dinma da kayi Allah saiya sakamun wlh Dan laifinka d'aya da y'an kidnapping"tsaki MD yaja tare da mik'ewa ya ce "Idan kina buk'atar wani Abu ina palour" Da harara ta bisa har yaban palourn wajen Azahar zahra ta karajin wata yunwar koda ta fita palour zaune ta samesa yana aiki a laptop Wuri ta samu ta zauna tana shashan magani so take tace masa yunwa takeji ta kasa ganin baiyi mata magana ba ya sanyata cewa "yunwa nakeji fa Malam" Kamar bazai tanka mata ba ya ce "Me kike son ci a kawo miki" Bana son Cin abincin restaurant Dan ban yarda da tsabtarsu ba bazan sake ci ba"Yana mata kallon mamaki ya ce "To shiga ki girka?Harara ta banka masa ta ce " Wlh kaji na rantse ko hanyar kitchen bazanyi ba"Aje laptop d'in MD yayi yana kallonta ya ce "To wa kike tunanin zai girka maki" Kai da kayi cikin da ke sakani jin yunwar kai zaka dinga girkamun harya zube.........🤙🏿
Chapter 96 · 0% Book details