Sashe 63
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
bacci ba ga baccin dake idonta bana wasa bane ga gajiyar da MD ya Tara mata shiko yana kwance kan bed a gaggauce ta shirya Bayan ta had'a ruwan liptop bako madara haka Tasha saboda sauri take tana komawa d'akin hijab d'inta ta sanya Harzata fita ta tsinkayi muryarsa da cewa"karfe nawa zaki dawo "A tunaninta ma bacci yake saita taja gunguni a ranta kafin ta ce " 4 Kuma 2 suke da lectures ta fad'a masa hakane Dan ta sarara"Okay "kawai ya fad'a " tana fita driver har yazo Dan tuni yasan lokuta da take Da lectures koda Zarah ta gama lecture hostel ta wuce kallo d'aya zakayi mata kasan ba daidai take ba saboda ba k'aramun bacci bane a idonta tana shiga ta samu su Asmy na lunch kasancewar 2 lokacin suma basu jima da dawowa daga lectures ba kai tsaye bed ta haye tare da sauke ajiyar zuciya kwanciya tayi Chuchu ce ta ce 'Lafiya dai momcy"lafiya qlau bacci ne kawai nakeji wlh "ta fad'a tana juya musu baya tare da kwanciya ta cire hijab din jikinta Da kallo Asmy ta bita kafin ta ce "Ki sauko kiyi lunch tunda nasan daga lecture kike bakici komai ba " idan na tashi naci ta bata amsa bacci ne mai nauyi ya d'auki Zarah ita ce bata tashi ba sai 4:30 Dan koda Asmy ta ce Zata data ita chuchu tace ta rabu da ita tana tashi salla kawai tayi sai sannan taci abincin da su Asmy suka rage mata a cooler tana gamaci time.ta duba taga har biyar saura tunani tayi tasan drivern yazo kila harya tafi tsaki taja a ranta ta ce "Yau ba Inda zani wlh mugu kawai" har dare ganin Zarah bata da niyyar tafiya ya sanya Chuchu cewa "wai yau nan zaki kwana amma" Eh nan zan kwana"Alhmdllh daman ina son ki jiye mun harda Dan so nake na sauke kafin mu gama sch d'innan wlh"Murmushi Zarah tayi ta ce "Insha Allahu zama ki sauke kafin lokacin tunda Kinga yanzu hizif shida ya rage maki" Da daddare Zarah ta amshi haddar Chuchu Inda ta kuma Kara mata wani shafin driver ko tunda yazo yayi ta jira yaga bata nan ya koma ya fad'a ma ogansa bai ganta ba "Okay kawai md yace " Kd ya wuce Ranar Dan yanason ganin Ammynsa "washegari ya koma Zaria Bayan yayiwa Ammynsa bankwana " Zarah ko ranar ma so tayi ta k'ara kwana dandai kawai tana fitowa lectures ta had'u da driver da ba abunda zai maida ita tana zuwa ta samu MD ya hakimce a kan kujera a takaice ta gaisheta tare da wucewa ciki....after 3 weeks Rabin rayuwar md yanzu kam ta dawo Zaria saboda koda yaushe yana nanike da Zarah yana kwasar romo ko sch yanzu dak'yal yake barinta ta tafi Zarah ko tana nan tana lissafin sauran wata guda ra rage yarjejeniyarsu ta kare inda karatunsu ya rage wata biyu su gama tun daga lokacin da ta zubar da maganin nan bata Kara waiwayar sha ba kwata_kwata tunaninta ma baikawo mata komai a ranta ba harkar gabanta kawai take "Yauma dak'yal MD ya rabu da ita Dan a safenma yanzu ba d'aga mata yake ba cikin Sauri ta gama shirinta Zata wuce sch tana shirin fita Ya ce " kijira na saukeki hanyar nayi"to"ta fad'a a hankali tare da zaunawa gefen gadon tana nan harya gama shirinsa ya fito Cikin shigarsa ta alfarma da gayu sai baza k'amshi yake kallo d'aya Zarah tayi masa tayi kasa da kanta saboda gabanta dake tsananin fad'uwa a tare suka fita Inda ya shiga driver sit ta zaga ta shiga gaba sun fara tafiya kenan ta Hango wata yarinyar mai tallar ta aya a faranti cikin Sauri ta d'ago tare da cewa "Dan Allah ka tsaya zan saya abunchan" Kallonta yayi tare da Kallon abunda take nuna masa ya ce "me zakiyi da abunchan ya gama shan kura a titi jifa " Tana Shagwabe fuska ta ce "Nidai ina so" parking yayi tare da mik'a mata 1k ya ce Amshi ki saya zage glass din motar tayi cikin Sauri ya sadda kansa Dan karma wani ya gansa a ganesa Zarah ko mamakinsa tayi kamar wani marar Gaskiya Juyawa tayi ta kira mai ta ayar Inda ta saya ta 500 ta bar mata chanjin a leda aka sanya mata har lokacin kan MD sadde saida ta Zage glass din kafin ya d'ago ya tada motar sukayi gaba kasayin shiru Zarah tayi ta ce "Wai Dan Allah me yasa baka San ana ganinka yanzuma ka sadda kanka " Is not your business "ya fad'a yana cigaba da driving" Turo baki gaba tayi tare da Fara cin ta ayarta har wani lumshe ido take Dan sosai tayi mata dadi ita kanta mamaki take da bata tabajin sha'awar wannan Abun ba Amma yau sosai taji dadinta Ta wutsiyar ido MD yake kallonta yanda ta dage take gintsar Abu da shi baimasan menene ba "bismillah" ya tsinkayi muryarta"Alhmdllh kici kayanki""Ka dandana kaji da dadi "Girgiza kai yayi a takaice ya ce "Banajin irin abubuwan nan" tab'e baki tayi tare da cigaba da cin abunta har cikin makaranta ya kaita Daidai gab da hostel d'insu yayi parking sauran ta ayar ta sa a jaka tana shirin fita Ya ruko hannunta Tare da damk'a mata 5k a hannu ya ce "Ki dawo da wuri yau please da yazo ki biyosa kidaina tsaidasa" Kasa tayi da kanta Tare da cewa"Toh ngd"har lokacin bai saki hannunta ba Ganin irin yanda yake kallon hannun tare da murzasa tanason tayi magana amma kwarjini yau da yayi mata ya hanata Chan Bayan few minutes ya ce "Kidingayin lalle zaiyiwa hannunki kyau inason ganin lalle a hannun mace"gaban Zarah na fad'uwa ta d'ago ta Kallesa saikuma tayi saurin kasa da kanta samun kanta tayi da cewa " To kace Matarka ta dinga yi maka mana"Murmushin da bai shirya saki ba ya saki ya ce "Kenan sai matata zatayi mun" Eh"ta fad a hankali"wani murmushin ya k'ara saki ya ce "To Matar wata Tara nace ta dingayi yimun ba ta gidan ba" ba tare da ta Kallesa ba ta d'an turo baki gaba ta ce"Matar wata d'aya dai ai wata Tara baya ne yanzu saura wata d'aya ko ka manta"ina sane harkin k'agara lokacin yayi mu rabu ko"D'ago da dara daran idanunta tayi ta sauke a kansa saitayi saurin kasa da kanta ta ce "Ina makara karya hanani shiga" Okay "ya fad'a yana sakin hannunta bud'e motar tayi tare da fita Daidai idonta ya sauka akan Hafiz dake gaban motar Kad'an sosai taga ya kara kyau da kiba yasha shaddarsa ash mai shegen kyau Ya harde kafa d'aya kan d'aya a jikin sabuwar motarsa sosai gabanta ya tsananta fad'uwa da karfi dafe saitin zuciyarta tayi daidai sukayi ido hud'u da shidinma ita yake kallo bako k'iftawa sannan yana bin motar da ta sauka da Kallo a matuk'ar rude ta juya ta kalli MD dake cikin mota har lokacin yaki tafiya Shima Inda take kallon yake Kalla Juyawa tayi ta k'ara kallon Hafiz da Shima motar MD yake kallo dukda baya ganin Wanda ke ciki lokaci guda Zarah taga fuskarsa ta sauya Wanda Bata tab'a ganin hakan a tattare dashi ba kamar wacce kwai ya fashewa haka ta k'arasa Inda yake ta kalli bayanta ta kalli gabanta haka ta dingayi ga MD yaki tafiya cikin jarumta ta k'arasa Inda Hafiz yake da har lokacin kallonta yake ya kalli motar da ta sauka dak'yal ta iya tattaro jarumtar da bata San tana da ita ba ta ce " Ya Hafiz Kaine da gaske kuwa"Juyowa yayi ya kafeta Da idanu tare murtuke fuska tamau nuna motar da ta fito daga ita yayi cikin muryar b'acin rai ya ce...........✍🏿