← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 129

Sashe 60

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

gida Ba Inda yake zuwa daka Kallesa zakasan yana samun kulawa saboda har wani kib'a yayi fatar nan tasa ta k'ara fresh saboda yana samun abunda yakeson tako wani bangare ga wani time d'in idan ya sanya Zarah tayi masa girki tanayi saboda yanzu ya rage mata rainin wayau da yake da yanzu har sukan zauna su danyi Hira bangare guda kuma yanayin waya da Matar sa kullum dukda taga number nigeria bata fahimta ba saboda tasan wani lokacin idan yaje kasashe akwai abunda yake kashe kudi yayi number sa ta Nigeria tayi aiki Bayan two weeks Zarah ta tafi sch saboda saurin da take ta mance wayarta a d'akin MD na kwance yaji ringing d'in waya a jaka sai sannan ya lura da jakar wacece kyalewa yayi nan wayar tayi ta ringing ganin ringing d'in ya damesa ya sanyasa janyo jakar Dan ya d'auki wayar ya kashe gaba d'aya yana zage jakar yana fiddo wayar yaga an rubuta ya Hafiz a jiki tsaki yaja tare da kashe wayar gaba d'aya yazo zai maida kenan ya Hango magunguna a ciki kamar bazai d'auka ba saikuma ya d'auko guda ansha Rabi saura Rabi kenan duba maganin ya shigayi Inda ya shiga karantawa sosai yayi mamakin Ganin maganin hana d'aukar cikine d'auko sauran biyu yayi yaga duk irinsune "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" ya fad'a a ransa a fili ya ce "watau aikin banza muke yarinyar nan ta fimu wayau duk plane d'in da muke wata da watanni ashe da abunda take sha no wonder ace har wata Bakwai saura wata biyu karewar yarjejeniyarmu ace bata samu ciki ba ," sosai yashiga jujjuya magungunan yanajin ba dadi a ransa ya ce "Yanzu ya zanyi lokaci na kurewa" Wani shiri ne ya fad'o masa a rai Tabbas dole yayi mata plane d'in da zata daina shan maganin nan saboda ko ba Dan sabodashi ba nan gaba zai iya yi mata illa ya lalata mata mahaifa tunda ba tab'a haihuwa tayi ba "Bayan Zara ta dawo daga lectures lokacin md baya gidan ya d'an lek'a gidan gonarsa dake garin Kai tsaye Zarah wayarta data manta ta nufa tayi mamakin ganinta kashe Dan bazata manta ba bata kashe ta barta ba saikuma tayi tunanin kukan ta tafi ta kashe din tana dubawa taga missed call d'in ya hafiz kiransa tayi Bayan ya kira suka sha y'ar Hira kafin ya k'ara jaddada mata da dawowarsa saura wata guda dukda gaban Zarah Saida ya fad'i amma hakan bai hanata nuna masa tana farinciki da hakan ba " Bayan sun katse duba wani missed call d'in tayi taga na Aunty Halima ce "Itama kiranta tayi Bayan sun gaisa tace " Amarya k'in bace ba ajinki kin yada auntyn naki"Murmushi d'auke da fuskar Zarah ta ce "ba haka bane Aunty kinsan koda yaushe kina raina" Murmushi tayi ta ce "Haba dai ai ni da kike raina aina nemiki turomun address din gidanki gobe insha Aah zankawo maki ziyara tunda ke baki zumunci" Gaban zarah saida ya fad'i Hakanan ta fusge ta ce "Kai amma Aunty Dana ji dadi zanturo maki ta message yanzu" Bayan sunyi bankwana gaban Zarah ya shiga fad'uwa ta ce "Ya zanyi da Matar nan Innalillahi" gashi bama tasan address din gidan ba fita Tai Inda ta tambayi mai gadi ya fad'a mata address din da lambar gidan nan taturawa Dr Halima text d'in address din gidan gabanta ta na fad'uwa sai Bayan magriba MD ya dawo "Kallonta yayi yaga kamar akwai abunda ke damunta cewa yayi lafiya dai ko?a sanyaye tace " Lafiya qalau Sannu"ywwa ko duk gajiyar sch din ce "murmushi ta kirkira ta ce " Wlh ko sai a slow level 4 d'innan ba sauki"Yana zauniya ya ce "Hakane daman kinsan aski idan yazo gaban goshi yafi zafi Allah sa dai a gama lafiya" Ameeeen ya Allah ngd "Wani course kike" Mass com "Wow " ya fad'a tare da Jinjina mata hannu ya ce "na Sara maki" dan murmushi tayi ta ce "Ko" Eh,mana"Tunowa yayi ba course d'insu d'aya da Chuchu ba a ranshi ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Nasanma bata Santa ba Tunda ba course d'insu d'aya ba " Wayarsa da yasa alarm kafin ya shigo tayi ringing dubawa yayi ya katse k'aran tare da karawa a kunnansa kamar mai yin waya ya ce "Hello Ya mai jikin" shiru yayi kafin ya ce "Subhanallahi kenan abun hartayi worse haka Gaskiya Aisha bata da hankali haukan me take taje tayi da shan maganin hana d'aukar ciki ai yanxu gashinan ya juyar mata da mahaifa tayiwa Allah shishigi ya gwada mata ikonsa yanxu gashinan ta rasa haihuwar ma gabak'i d'aya garin shirme a Gaskiya banjiye maka dadi ba aboki Allah ya kiyaye gaba" shiru yayi na d'an dakiku Alamun kamar yana sauraran bayani daga wayar sai kuma ya ce "Ah to da gaskiyarka kam gwara kayi Aurenka tunda ita ta sayawa kanta Allah ya kyauta ita kuma ya bata lafiya" Tunda ya fara wayar hankalin Zarah ke kan abunda yake cewa kasancewar da karfi karfi yake maganar sosai gabanta ya fad'i fahimtar abunda suke cewa da tayi a ranta ta ce "Na shiga ukku karfa na illata kaina" tanajin saida ya gama wayar kamar bazatayi magana ba Dan Duk ta rude saikuma tayi k'arfin hali ta ce "Dan Allah na tambayeka" Inajinki"Wannan Wanda kuke waya dashi kamar na lura matarsa ce keshan maganin planning ne yayi mata illa ko"a ranshi ya ce "Alhamdulilla anzo wajen a fili kuma cewa yayi"eh ya akayi " shiru tayi saikuma ta ce "Bakomai amma ta jima tana sha har yayi mata illa haka?Girgiza kai yayi ya ce " a a a ko shekara ba ayi ba tana shan gashi sabon Aure ne sukayi Yanzu yayi mata illa har an cire mata mahaifa"Sosai ta firgita ta kasa control d'in kanta cikin firgici ta ce "Innalillahi yanzu kenan shikenan bazata sake haihuwa ba Amma ba kowanne maganin yake illa ba ko?...........✍🏿
Chapter 60 · 0% Book details