Sashe 56
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
dai ita ba ma'aikaciya ba,ba y'ar kasuwa ba,ba wani aikin gida take ba macen da ko shara bazata ce ta tabayi ba ,Amma duk dare saita gama chat d'inta da kawaye tace ta gaji"Da wannan tunanin dak'yal ya samu bacci ya kwashesa washegari da misalin 4pm yana zaune a kujerar palourn su suna Hira da Ammy Chuchu ta shigo gidan "da fara'arta ta ce " Lah yaya Kaine two days bana ganinka karkaga yanda nayi missing dinka "murmushi ya sakar mata ya ce " Daga ina Haka Auta na ganki da jaka"gefenshi ta zauna ta ce "Daga gidan Aunty Zey nake kwana na biyu a Chan " Kice ziyara aka kai mata "Murmushi tayi ta ce" Eh Yaya "Ammy ce ta ce " Tofa keda kikace zakiyi sati me ya maidoki"Dariya tayi ta ce "kewarki ta dawo dani ammy Gani nayi bazan iya ba ina gari bana ganinki sainayi ta tunanin kewa zatayi miki yawa gasu y'an rainin wayan yaran nan na Aunty Zey nayi da su taho mu taho suyi maki kwana biyu sukaki wai Saidai in gidan Uncle zankaisu shiyasa na tahowata watau ni sun rainani"ta fad'a tana turo baki" murmushi Ammy tayi ta ce "Ai yaran nan sarkafar iyaye garesu shiyasa nama hakura da a kawomun su Dan ba zama ba zasuyi sun fiso su jisu kusa da iyayensu sai suje Chan su karata Tunda ga Auta ai nasan ke kin bani Yaranki ko" Dariya Chuchu tayi tare da rufe fuska ta ce "Kai Ammy Saidai yaran Yaya dai" Ohhh bazakiban ba kenan kun nunamun Yayan shine kawai nawa ko to shikenan Shima Allah ya kawo nasan kuga yanda nima zan gwada muku banbanci Dan Ko halawa na sayawa yaranshi bazan bawa naku Ba "Dariya Chuchu tayi ta ce " Kai Ammy Bafa haka nace ba "MD najin hirarsu bai tanka ba saida Ammy takawo zancen yaransa Yaji zuciyarsa wani iri a ranshi ya ce " Allah yasa nima ina da rabon ganin nawa yaran"ganin hirar zata sanya MD tunani ya sanya su sakin hirar suka kama wata MD ne ya kalli Chuchu ya ce "Tunda kika dawo Hutu bakije gida na ba why" Sorry yaya Aunty Amera na gidan shiyasa bana son zuwa "Bata fuska yayi ya ce " Ita ga dodonki ko?girgiza kai tayi ta ce "Yi hakuri Yaya ba haka bane" Saura kwana nawa hutun naku ya k'are "3weeks" Okay shirya mu tafi ki k'arasa hutun a gida na "Kamar zatayi kuka ta ce " Yaya Za abar Ammy ita kadai fa "Sanin Halin Chuchu sarai ba jituwa Suke da Amera ba ya sanya ta cewa" Kayi hakuri Babban yaya tayi maka kwana biyu nima banajin dad'in gidan ni kad'ai sai masu aiki "To shikenan Ammy" ya fad'a Ajiyar zuciya Chuchu ta sauke Kala biyu Chuchu ta d'auko suka tafi gidan MD dukda ranta bayaso a palour suka tarar da Amira ta harde kafa daya kan d'aya tana latsa waya y'ar aiki durkushe gabanta tana mata tausa a kafa "Tsaki Chuchu taja a ranta ta ce " kamar wata yar shugaban kasa mtwsss fuska murtuke ta zauna palour Bayan MD ya zauna Dagowa tayi tare da Fara Murmushi ta ce "Honey yaushe ka dawo" Yanzu "ya bata amsa yana lumshe ido " Tsawa ta dakawa me aikin ta ce "Bazaki tashi ki tafi ba kina ganin mijina ya dawo Dan kutumar ubanki zaki zauna a nan ban muku dokar cewar ko a bisa sabani idonku ya had'u da na mijina a bakin aikinka ba to kema yau aikinki ya k'are Dan haka kije na koreki daga yau na kuma ganinki a hanyar layin nan ma sai nasa an kama Duka ilahirin danginki " Cikin kid'imewa y'ar aikin ta fara kuka tana magiya ta ce "Dan girman Allah Hajiya kiyi hakuri wannan Aikin shine madogarata idan na rasashi bansan ya zanyi ba kiyi hakuri ki yafemun ina tsoron tashi ne karkice kuma nayi laifi shiyasa kimun rai Hajiya" D'auketa da wani irin Mari Amera tayi Wanda Marin saida ya tsoratar da Chuchu ta ce "Ni zan fad'a magana ki musa mun Dan Ubanki y'ar matsiyata dake zanyi musayar baki tana shirin Kara d'auketa da wani marin Chuchu tayi Sauri ta shige gabanta " Wani banzan kallo ta watsawa Chuchu ta ce "Ke kuma ina ruwanki matsa kiban waje" bazan matsa ba idan ke bakisan darajar d'an Adam ba ni na sani me yarinya tayi miki Dan zalinci zakiyi mata irin wannan Marin Dan kina tutiya da arziki kifa sani arzikin nan da kike tak'ama dashi Allah ne yake rabawa ga duk Wanda yaso suma talakkawan basu sukayi kansu ba Allah ne yayosu haka haka masu arzikinma Duka yin Allah ne akanme zaki dinga wulakantar da na kasa dake dandai kawai suna karkashinki"wani banzan kallo Amera ta watsa mata kafin ta ce "Allahu Akhbar ke kuma yaushe kika fara wa azi bamu da masaniya" banza Chuchu tayi mata tare da kama hannun yar aikin sukayi waje kudinta 20k dake hand bag d'inta ta bata tare da bata hakuri "kafin ta dawo Inda ta samu MD haka ta barsa kamar komai bai faru ba a ranta ta ce Wlh hada laifin yaya da ya bari Matar nan take iskanci yanda taso" Bata kuma waiwayar Amera ba tayi wucewarta D'akin da take sauka tana Jan tsakin Haushi da tsanar halin Amera "MD ko sai Bayan barin Chuchu wajen ya rufe Amera da fad'a akan Abunda take bata kyautawa " Nanfa ta tubure tace wlh kome zaice Saidai yace Amma indai akan wannan ne yanzu ta fara ganin bata bakinshine ma zaiyi rabuwa yayi da ita kwanan Chuchu biyu a gidan Wanda kamar a k'aya tayishi ta koma gida Koda ta koma ta bawa Ammy labarin abunda ya faru girgiza kai tayi ta ce "Rabu da ita duniya ce " MD ko yananan yana lissafin kwanakin da ya ragewa su Chuchu su koma makaranta. Kowa idan zai koma makaranta bak'inciki yake na rabuwa da gida banda Zarah dake d'okin komawarta sch Dan wannan Karin ba k'aramar takura Tasha ba wajen Mama Rabi ba Bugu amma akwai zagi da bakaken maganganu ga aiyuka dukda wannan baya damunta saboda ta saba yaune komawarsu sch Wanda tunda safe ta shirya Bayan Baba ya sallameta da abunda ke aljihunshi dukda dak'yal ta Amsa nan yayi mata nasihohi kamar yanda ya saba yi mata Bayan fitarshi ba jimawa itama ta shirya sosai taji dad'in Rashin ganin Mama Rabi a gidan Dan yanzu ta tarki yawo gidan su Asmy suka wuce Inda daga Chan suka wuce Tasha suka hau motar Zaria minti hamsin me kyau ya kaisu har hostel Bayan sun huta wayarta Zarah ta janyo tare da dannawa Chuchu kira ta ce "Ya dai daughter munfa shigo bamu ganki ba " Daga bangaren Chuchu ta ce "Haba daman nafison saikunzo nazo nima gani nan tahowa gobe daman nagama parking d'in komai na " Okay to muna Kallon Hanya ki gaishe da Ammy"zataji Zan fad'a mata insha Allah "washegari Chuchu ta shirya ta taho makaranta Wanda driver ne ya Kaita MD Bayan ya shigo gidansu ganin baiga Chuchu ba ya sanyashi tambayar Ammy ya ce " Ina Chuchu wai Ammy"Ai ta koma makaranta tun d'azu kenan batayi maka bankwana ba auta kenan Wani abun sai ita nafa zata tayi maka bankwana"Girgiza kai yayi ya ce "may be ta kira waya ta tana kulle" Koda ya koma gida tun a hanya yake jinshi cikin farincikin da ya rasa dalilinshi.........✍🏿