← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 129

Sashe 11

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"korata ake kenan"cikin murmushi ta bashi amsa da "Nina isa Banki mu shekara haka ba"

'ta fad'a ta na rufe fuska " murmushin jin dad'i yayi cike da kewarta Hafiz ya juya yabar makaranta Inda Zarah ta kama hanyar hostel d'insu.

ta na shiga ta samu Asmy Harta cire hijab din ta na shirya musu kaya "Kallon d'akin tayi ta ce.

" wai nufinki mu kadai ne kenan a dakin"

"Wlhko Nima haka nagani naga duk ba a fara zuwa ba Kinsan Monday ake fara lectures ba kowa zai zo kamar haka ba"

"Kice mu iyayen azarb'ab'i mune farko farko ta fad'a tana cire hijab din jikinta "

Dariya asmy tayi ta ce "Keko abunka ga farin shiga Dariya Itama Zarah tayi tare suka kimtsa komai kafin Zarah ta mik'awa Asmy wayar da ya Hafiz ya saya musu zo kuga murna wajen Asmy hada tsalle ta Rungume Zarah.

" itama Zarah cikin farincikin take bud'e wayar suka ga iPhone 6+ ce Duka iri daya dubawa sukayi kowacce Duka an sanya sim ganin ba chaji gashi ba wuta ya sanyasu ajewa sai Chan wajen 8 aka kawo wuta nan suka sanya wawowin chaji salla Zarah tayi tare tare da hayewa kan bed tace.

"nikam bacci zanyi wlh nagaji" Asmy ce ta ce "Chab aini nan inkinga na kwanta to wayar nan ta cika Na duddura abubuwa a ciki har what's app saina bud'e komin dare.

" Dariya Zarah tayi ta ce "aifa abun nema ya samu nikam bacci ma zanyi waya bata dameniba sosai Idan kin d'auko abubuwan nima ki daukoman amma what's app kadai zaki budemun sannan kiyimun down load din Qur'an na ji da na karantawa"

" To" Asmy ta fad'a ta ce "Mu sarakan zumudi Allah sama akwai data a sim din " Juyawa Zarah tayi tare da kwanciya ta ce .

"Allahsa ma babu muga ta tsiya kiyi ,zaman hofi"

"Insha Allahu ma akwai muguwa Asmy ta fad'a tana Mikewa itama tare da Fara Sallar bacci ne ya kwashe Zarah cike da gajiya.

Ranar Monday suka fara Lectures Sosai Dukansu suka maida hankalinsu ga karatunsu Zarah suna waya da Hafiz Sosai Kuma suna chat dukda ba Sosai take hawaba saboda ba wasu mutanen chat gareta ba.

danma Asmy tayiwa wata kawarsu da sukayi sec magana ta bada number su aka sanyasu grp din makaranta anan ne ma wasu ke binsu PC har suke chat amma dukda haka Zarah saita yini bata hau online ba.

Karatu suke sosai ba kama hannun yaro yanzu hostel din ya fara cika da mutane Dakinsu ma sunsamu Karin wata Mutum guda zaituna.

<Kaduna>

Cikin marairaicewa ta ce "Yaya Dan Allah ka bari na tafi A B U din wlh yaya banason karatu a America plx harfa sun bani admissions kuma ma har anfara lectures yaya Dan Allah"

"Chuchu bazan barki kiyi karatu anan k'asar ba fa Ga yanda na tsara tare zamu tafi america a gidana zakiyi karatunki amma ban lamunce na barki ki tafi Zaria karatu ba Nafison kiyi a gaba na na sanya miki ido saboda wannan rawar kan naki Dan kiyi abunda kikeso shiyasa ai kikak'i cike KASU kika zab'i ki tafi Zaria sannan banason kiyi karatu a kasar nan sanin kanki ne to bazaki ba A B U din ba na gama magana"

"kuka Chuchu ta sanya tare da Fara birgima ta sangarta sosai ta ke kuka da diddira kafa Ammy ce ta shigo ta ce .

" Subhanalla Me akayiwa Auta ta ke wannan kukan "MD dake zauna baice uffan ba sai maida hankalinshi ga kallon da yake yayi"

Chuchu ce cikin sangarta ta ce"Ammy yaya ne ya ce "Wai bazan tafi Zaria karatu ba dole sai dai mu tafi america tare Bayan ni banason nesa dake Ammy plx ki ce ya barni "

"Kallon MD Ammy ta yi ta ce " me yasa bazaka barta ba babana tunda harta samu kuma ta nuna Chan din take so ka barta ta tafi kawai nima banason tayi nesa dani saboda kaga gidan kadaici zaiyimun yawane ba Abbanku Zainab na gidan mijinta kaima ka tafi sai anganka please Babban yaya ka barmun ita "

Jan numfashi Yayi tare Dagowa ya harari Chuchu dake Kuka jikin Ammy ya ce.

"Allah Ammy kin sangarta Yarinyar nan jifa irin tabarar da takeyiwa mutane"

Dariya Ammy tayi ta ce "Ah muka sangarta ta dai duk gidan nan wa ya fi sangarta Maryam sama da kai "

"Ummmm to Taci arzikinki Ammy na yarda Tayi Chan d'in Allah kiyaye Amma Tana cigaba da irin wannan shigar Saidai taga na cireta Nayi mata Aure "

ya fad'a yana kallon matsatsun Riga da wandon dake jikinta Tsallen murna Chuchu ta buga tare da rugawa ta Rungumeshi ta ce.

"Thnks Babban Yaya Uba Allah ya k'ara girma bazan sake ba sannan tayi Dariya ta ce hhh yaya Ai ko kayimun Auren bazan zaunaba y'ar k'arama dani kuna kaini kafin ku dawo ma na rigaku gudowa "

Duk miskilancin MD saida ya d'an dara tare da Kai mata "Dukan wasa a baya ya ce.

" Kin rainani ko chuchun yaya shiyasa kika fad'amun haka"

"Ammey ma tayi Dariya tare da girgiza kai ta ce "Allah shiryaki Auta"

Dariya Chuchu tayi tare da mik'ewa ta Ruga cikin tana tsallan murna nan ta kira Aunty Zey ta mata albishir yaya Ya amince..

A nan take MD ya kira Wani Abokinshi dayake lecturar makarantar ta Cikin waya yayi mishi bayanin komai take ya ce Ai ba matsala tunda ta samu registration Banki kawai za Aje ayi"

PA d'inshi Ya kira Tare da sanyashi yaje yayiwa Chuchu registration saida yaga ya gama yi mata komai tukwana Ammy ce ta Kalleshi da damuwa a fuskarta ta ce.

"Baba na wai ya maganar bincike game da kisan mahaifinku naga Har yanzu bakayi wani Abu ba yaci ace angano kowaye yayi mana Wannan d'anyen Aikin"

"numfashi Ya fesar tare da cewa " Insha Allahu Mamy Gaskiya zatayi halinta inaji a jikina nan kusa akwai abun al'ajabin da zaizo bada jimawa ba akwai shirin da nake akan Lamarin "

Goge hawayen da ya zubo mata Ammy tayi tare da cewa"Allah dai ya Toni.Asirin ko suwaye sukayi mana wannan d'anyen aikin insha Allahu bazasu gama da duniya lafiya ba Sannan asirinsu saiya tono"

"Ameeeen MD ya fad'a tare da mik'ewa zai shiga Bedroom d'inshi dake gidan " da mamaki ammy ta Kalleshi ta ce "Ina kuma zaka Bayan Matarka na gari"......✍🏿

*Domin magana da marubuciyar 07026166536*

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

💑 *AUREN WATA TARA* 👨‍❤️‍👨

MALLAKAR

*Hajara L Sadeq*

*_TEAM GAWURTATTU BIYAR_*

🅿️.........*15 & 16*

Ta na gidansu Ammy"tsaki Ammy taja tare da cewa "Allah ya kyauta " D'an murmushin gefen baki yayi tare da girgiza kai ya wuce ciki.

<Zaria >

"Kwance take saman bed din Dakinsu ta na chat da Hafiz d'inta ya na bata labarin abun Dariya labarai masu sanya nishad'i sosai takejin dad'in chat d'in " Asmy ce da ke Dafa musu indomie a k'aramun gas d'insu ta ce "

"Uhm Manya chat yayi dad'i sai Murmushi ake "

"Kede bari wani labari ne ya Hafiz yake bani na ban Dariya" ta na sauke indomie d'in Asmy ta ce.

"Ai naga alama kam Sauko muci kafin ta huce "

kashe datar tayi tare da Saukowa nan suka faracin indomie d'in kasancewar dare ne.

"suna cikin ci y'ar d'akin su zaituna ta dawo K'arewa shigarta kallo Zarah tayi taci uban attachment ta sanya matsatsun kaya girgiza kai tayi tare da Cigaba da abunda take Dan ta lura yarinyar ba tarbiya gareta ba hakan yasa ko maganar kirki bata had'asu inba Sannu ba .

Sannu tayi musu Zarah ta amsa da yawwa " Asmy ce ma dayake suna Dan mutunci suka Dan tab'a Hira yayinda Zarah tayi kwanciyar ta dan gobe tun 8 suke da lectures .

Washegari tunda safe ta shirya 7:40 tayi mata a class saboda 8 suke da lectures Bayan lecturer d'insu ya fita Mikewa tayi tare da fitowa jikin wani block ta zauna tare da fiddo hand out d'inta ta fara Duba abubuwan da akayi musu sosai.

Sallama taji anyi mata batare da ta d'agoba ta amsa "zan iya zama Malama Zarah " Dagowa tayi tare da Kallonshi class mate d'insu ne amma tayi mamakin yanda yasan sunanta "

"Matsa masa tayi tare da cewa zaka iya zama mana" Bayan ya zauna Har lokacin karatunta take "cike da burgewa ya ce

" Gaskiya Malama Zarah kin burgeni wlh Tunda kika shigo makarantar nan na lura da kwazo da nutsuwarki Da yawan dalibai ba karatu ke.kawosu ba makaranta amma ke yanda kike dagewa yasanya nayi sha'awar Ko zakiyi abota dani Dan nima na k'aru saboda course d'inmu d'aya kuma math tana bani wahala sosai "

Murmushi Zarah tayi masa tare da kallonta ta lura yana da nutsuwa daga ganinsa kasan d'an Babban gidane ta ce "Badamuwa Allah sa mu karu da juna Saidai bansan sunan malamin nawa ba "

Cikin barkwanci ya ce "Ah dalibinki dai ai kece malamar sunana Yusuf muna zaune a garin Abuja tare da iyaye na karatu ya kawoni Zaria bansan kowaba"

"Ah kace Babana ne Saidai na kiraka da Baba " Dariya Yusuf yayi ya ce "Wow kice da y'ata nake tare Gaskiya nayi sa'ar haihuwar wannan santaleliyar d'iya Kinga dole ayimun biyayya Sannan Abban na zaki dinga Cemun ba Baba ba "

Duk yanda Zarah taso ta fusge saida ya sanyata Dariya ta ce "Eh Gaskiya ne Abba na Amma naga Abban nawa akwai iyayi da surutu fa "
Chapter 11 · 0% Book details