Sashe 120
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Why jabir me nayi Mata da zata nunamun irin wannan tsanar wlh jabir Ina son matata bazan iya rabuwa da ita ba please me yasa ta Kasa fahimtata "Kayi hakuri bloody Dan Allah komai yayi farko Yana da karshe kamar Wanda aka zabura haka MD ya aje little yabar palourn ya fita daga gidan y'ar mama Habi tazo ta dauki yaran jabir ya fita ya bishi MD dafe kanshi yayi da yakejin kamar zai rabe biyu ranar hotel suka kwana Dan MD ya dauki alwashin bazai koma Kaduna ba harsai Zahra ta amince Masa Tundaga ranar MD.basu koma kd ba hotel suke kwana kullum saisunje gidan mama habi Saida Yaga yaran Amma Zahra taki bashi hadin Kai ta fitoma su gaisa kiyawa take mama habi ko Sosai ta dinga Mata fada akan wulakancin da take yiwa bawan Allahn Nan yayi yawa Yauma Bayan sun tafi Bata yarda ta fita ba kwance tayi Tana hawaye ita. Kanta yanzu karya take ta ce "Batason Musty Saidai Kuma batajin zata koma Masa ya wulakantata"MD Saida sukayi sati biyu a katsina suna zarya jabir harya Fara gajiya a lakacin ne Kuma MD ya Fara wani irin ciwo Zazzabi da azababban Ciwon kai yau tunda safe Jabir Yana lekawa dakin ya samesa durkushe Yana Numfashi sama.sama hankali tashe Jabir ya dinga kiransa Amma baya iya mayar Masa sai Numfashi yakeja Cikin kidimewa da taimakon ma'aikatan Wajen aka Kai MD asibiti Kai tsaye medical center aka wuce dashi da isarsuma emergency akayi dashi Ammy jabir ya Kira ya fada Mata suna katsina MD ba lafiya "Cikin tsananin tashin hankali Ammy ta ce "Katsina Kuma jabir Me ya kaiku katsina meya samesa"Hankali tashe ya labarta Mata akan Zahra ne satinsu biyu garin"Salati Ammy tayi ta salamce ta ce gamunan yanzu"Hankali tashe Ammy da chuchu suka Wuto katsina kasancewar ta fly suka hau yasa sukayi saurin zuwa Sosai hankalinsu yayi matukar tashi ganin halin da md ke ciki Cikin kuka chuchu ta ce "Ya Jabir Ina Take fadamun wani gida ne take "Ki Bari chuchu a Fara sanin halin da yake ciki tukwana ayi wata magana daga baya "Cikin kuka ta ce "Yaya jabir Dan Allah ka fadamun please ka kaini gidan da take Dan Allah "Ganin irin yanda chuchu ke kuka Ya Sanya jabir daukarta a mota ya dinga lallashinta har suka iso gidan da Zahra take Cikin kuka ta shige Gidan a palourn ta samu Zahra itama dukta rame Tana bawa Amar Madara Cikin tashin hankali da kuka chuchu ta ce "Shikenan momcy Kin kashe Yaya Kin sakashi Cikin wani Hali saboda soyayyarta da yake maki meye laifinshi Dan yace kawai Yana sonki Momcy Yaya Yana halin mutuwa ko rayuwa saboda ke.."ta karasa fada Cikin wani irin kuka Mai cin rai"Hankali tashe Zahra ta Mike kadan ya Hana Bata saki Amar ba cikin tsananin tashin tashin hankali ta Dora hannu aka saikuma ta fashe da kuka ta ce "Na shiga ukku chuchu Yana wani asibitin "Medical center ta fada cikin kuka ai Zahra Bata kuma sauraransu ba hijab dinta kawai dake kusa da ita ta sanya ba Shiri tayi waje a guje kamar wata mahaukaciya Tana fita ta tsaida napep ta fada Masa asibitin dazai kaita hankalinta matukar tashe suna Isa asibitin bama ta saurari Mai napep dinba Dan bama ta fito da kudi ba hango Ammy da tayi jikin wani ward ya sanyata rugawa a guje ba Abunda take in Banda kuka Tana zuwa ta fashe da kuka ta fada jikin Ammy Tana kuka ta ce Dan Allah Ammy karya mutu Ammy wlh Ina son mijina dan Allah Ammy ki taimakamun"ta fada Tana fashewa da wani irin kuka saikuma ta zabura ta ce "Ina ne inda yake Ammy Dan Allah"Ammy na hawaye ta nuna Mata dakin"Ai Bata saurara kowa ba ta Ruga a guje Tana hangoshi doctors biyu akanshi batasan sanda ta Ruga ta fad'a jikinshi ba Tare da fashewa da wani irin sabon kuka ta garkamesa ta ce "Dan Allah ya musty ka tashi karka tafi ka barni wlh Ina sonka please ka tashi Dan Allah"sosai ta rumgumesa doctors din duk kallonta suka tsayayi MD kamar cikin bacci yakejin kamar Zahra daukarsa mafarkine Saida ya bude idanunsa da sukayi Masa nauyi ya sauke a kanta data Haye kirjinsa Tana kuka"numfashin da taking yayi ne ya sanyata sauri tashi tare da saurin Kama hannunshi ta cikin Ido suke kallon juna yunkurawa MD yay ya tashi zaune kamar ba shine aka kawoshi Rai hannun Allah baisan Wanda wasu irin hawaye masu d'umi suka zubo Masa ba tare da gark'ame hannunta yayi sosai Yana hawaye ya ce"Dan Allah Mamy kiyi hakuri karki rabu Dani wlh Ina sonki har cikin zuciyata banajin Zan it's rabuwa dake Kuma na rayu please ki tausayamun"ya karasa fada Yana kuka kamar ba namiji ba "Komawa kirjinshi Zahra tayi Tana shashskar kuka ta ce"Kayi hakuri duk Abunda nayi maka Dan Allah Abban triple na shirya rayuwa dakai na har abada Ina sonki Nima Kuma zankoma maka please ka warke banason ganinka cikin wannan halin "a matukar zabure MD ya rukota ya juyota Yana kallon fuskarta ya ce"Ke kike fad'ar maganar Nan da bakinki Mamy da gaske kike kina Sona ko ko kunnuwanane suka jiyemun ba daidai ba "Zahra na hawaye ta gyada Masa Kai "Ai MD baisan lokacin days sake rungumota jikinshi ba cike da farinciki da tun haihuwar triple bai Taba shiga irinshi ba ya ce "Thanks you thanks you so much my all above ngd Mamy da amincemun da kikayi Zaki koma gareni nagode "Lafewa jikinshi Zahra tayi Tana Murmushi Tana Jin wata nutsuwa na Kara ratsa ta tanajin Kamar ta sauke want gagarumin nauyi a kanta it's kanta sai yau ta fahimci irin son.da take Masa batare da ta sani ba mamaki take har yaushe ta Fara sonshi haka Bata sani ba "Gyaran muryar da Ammy tayi ne ya dawo da su daga duniyar shaukin kaunar junan da suka lumtiya a hankali Zahra ta zame jikinshi daga nashi Tana dagowa ganin Ammy da Baba(kakanta) da tayi ne yasanyata Jin wata irin kunya tamkar ta nutse a Wajen Ammy ko da baba hamdala kawai suke Kallonta days zakayi musu kasan suna cikin tsananin farinciki haka chuchu da it's da jabir da suke bayansu da gudu chuchu ta ruga ta rungume Zahra cikin farinciki ta ce "Thnks you so much momcy kin ceci rayuwar Dan uwana ngd "Murmushi kawai Zahra tayi Tana kasa da kanta karasowa dakin sukayi inda MD yake baba ya zauna ya ce "Ashe jikinshi da sauki jikana hankali na duk a tashe da jabir ya fadamun zuwana kenan Masha Allah "Murmushi MD.yayi Wanda Ammy harsun mance yaushe rabon da yayi irinsa ya ce"Alhmdllh"Jaber ne Yana harararsa ya ce"Yana ganka ka Mike Haka kamar ba Kaine muka kawo Rai hannun Allah ba"Yana Murmushi ya ce "To bakaso kaganni haka ba na warke kaga silar ciwon Daman Kuma tayi magani"ya fada yanayiwa Zahra want shuumin kallo"Ammy na Murmushi ta ce"Babana baka ma karar muna Wajen ko"Sosa keya yayi Yana y'ar dariya"Bayan dr ya shigo ya ce To ya patient Kuma har ana dariya jiki yayi sauki kenan"Mikewa Md yayi tsaye kamar ba shine marar lafiyar ba ya ce "Ku taho mu wuce na warke"Dr ne Yana driya ya ce "To ranka ya Dade baka jira a sallameka ba"Na sallami kaina "ya fada Yana Sanya takalmi"duk dariya sukayi gaba daya gidan mama Habi suka koma Tunda suka shiga suka Fara jiyo kukan triple da gudu Zahra taje ta amshesu shataf ita Tama Manta da zasuyi kuka Dakyal ita da chuchu suka lallashesu har sukayi shiru tukwana tayi feeding dinsu chuchu sai tsiya take Mata Tana ciccijewa"Sosai mama habi taji dad'i da su Zahra suka sasinta kansu Nan aka Fara maganar yaushe zata koma number wayar Baba ta Kira Bayan sun gaisa take mashi bayanin komai cewa "yayi ba matsala habiba duk yanda kukayi daidai ne Ki barmusu ita su tafi kawai Allah ya bada zaman lfy"bayan tayi musu bayanin Abunda ya faru sosai kowa yaji dadin hukuncin na baba a ranar Suka juya kd Tare da Zahra da yaranta MD jinshi yake cikin wani irin farinciki Koda suka koma ya zaci Ammy bashi ita kawai zatayi su koma gidansu saiyaga sabanin haka ta wuce da ita bangarenta Nanfa MD.ya b'ata fuska Ganin Yana Shirin yin wata rashin kunyar gaban baba tsoho ya Sanya Ammy harararsa hakan yasa yaja bakinshi yayi shiru Koda Ammy ta Kira Hajiya Kaka ta fada Mata a waya An daidaita komai sosai tayi farinciki sannan ta Kara sanyawa aurensu albarka Dan ta koma maiduguri tun last week tundaga Zahra ta dawo Ammy ta shiga gyarata ciki da bai kamar wata sabuwar amarya har dilka da tsumin kamshi ake Mata gashi Ammy ta kasa ta tsare Akan md ta ce sai Y'arta ta Kara nutsuwa ta gyarata tukwana zata bashi Ita yaranta ko sosai suke wayau gasu Basu da kiyiwa Gata da soyayya suke Sha a gurin family din nasu ta musamman kayan wasa kuwa saisun ture idan yaran ka gansu saikace sunyi 7 months Nan ko watansu hudu daka kallesu kasan suna da tsananin lafiya irin zubin turawan Nan garesu"bangaren MD Shima Shirin yake sosai Dan Sabon gida ma ya bada kwangilar Gina Masa na gani na fada dan yace a Sabon gida Amaryar tasa zata zauna Banda lefe da suke shiryawa shida zey Dan makudan kudade na ban mamaki ya Bata Akan ta fita waje ta hadowa y'ar gold din nasa lefen da ba a taba yiwa wata y'a mace irinsu ba,yau Ammy ta Shirya bawa MD matarsa Bayan ta Sanya anzo an yarfa Mata Lalle dayayi mugun amsar fatarta kitso ta Sanya akayi mata shima Mai shegen kyau Tsadadden lace da yasha dinki Ta Sanya da yayi mugun yi Mata bala'in kyau simple make_Up asmy da tazo tayi Mata sai zolayarta suke ita da chuchu suna ce Mata amarya saidai ta hararesu ko ta musu Tsaki"Sosai ta fito tayi kyau kamar wata wacce zata zaben sarauniyar kyau ni kaina Saida na ce"Tubarakallah Masha Allah "saboda wankan ta wanku kallo daya zakayi Mata kasan eh ba karya ta cika Mrs MD a palour Ammy ta zaunar da su ta dinga yi musu nasiha sosai gami da nusarwa cikin hikima Ta dinga Musu nasihohi bayan nan ta