← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 129

Sashe 88

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Kiran Jabir da Chuchu suke masa ba Sosai zahra ta chaza masa kai ganin tana Kokarin fusgewa daga ruk'on da yayi mata ya sanyashi kallon driver ya ce " Kayiwa ko ina na motar lock sannan Ka wuce Abuja damu"Angama ranka ya dad'e drivern ya fad'a yana cigaba da tukunshi"Sai sannan MD ya tuna da maganganun da zahra tayi gaban driver kwata kwata Yama manta da wani a motar "Kuka zahra take sosai Kamar ranta zai fita ,Wanda MD jin kukan nata yake har cikin ransa Yana rike da ita tana kuka Dak'yal har suka zo Kaduna yana sassauta ruk'on da yayi mata ta fusge tare da Fara kokarin bud'e motar ta kasa buga glass din motar ta fara a haukace kamar mahaukaciya " Dafe kanshi MD yayi dake masa tsananin ciwo ya ce "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Allahumma ajirni fi masifatihi" Ganin tana shirin fasa glass din motar ya sanyasa Saurin ruk'ota Da k'arfin tare da matseta jikinta Ya ce "Ki nutsu Mamy Dan Allah kibari" Bazan nutsu ba din mugu macuci wlh ka maidani garinmu ko nayi addu'ar da motar nan zata kama da wuta Duka mu mut....bata k'arasa fad'a abunda take son fad'a MD ya Sanya bakinshi cikin nata Dan ya lura wannan hanyar ce kad'ai zata taimaka masa ta kasa magana"Zahra najin bakinshi cikin nata ta fara yunkurin ta kwace amma ta kasa samu tayi ta gantsarawa harshensa cizo iya karfinta..............✍🏿
Chapter 88 · 0% Book details