← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 129

Sashe 18

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar sai bacci barawo ne cikin dare ya kwashi Zarah koda su Asmy suka tashi suka tashi Sallar asuba kin tashinta sukayi saboda ta huta bata samu bacci ba sai wajen 8 ta tashi garas Sannu sukayi mata ta amsa da murmushi ta ce "kunjiku fa kamar wata mai ciwo sannan ta duba agogo ta ce " ya Allah shine kukaki tadani nayi sallah"Chuchu ce ta ce "Ai munga bakiyi bacci ba shiyasa" dukda haka din ai da kuntadani ta fad'a tana Mikewa Dan zuwa ta dauro alwala.
<KD>
Yau koda ya tashi duk rai ba dadi Bayan ya shirya kamar ko yaushe a palour ya hakimce tare da kwanciya kan sopa lumshe idonshi yayi ba abunda ke fad'o masa a rai sai muryarta lokacin da take karatu har wani lumshe ido ya ke shi kanshi ya rasa dalilin da yasa muryar ta kasa barin kwalwarsa saurin barin wannan tunanin yayi a ranshi tare da Jan tsaki wayarsa ce tayi ringing dubawa yayi ya ga Amera ce tsaki ya ja tare da Aje wayar ta karashi ringing d'inta harta gama.

Kira ta shiga yimai sosai har 5 missed call bai daga ba Jin shigowar message ya sanyashi Jan tsaki tare da d'aukar wayar ba tare da ya duba message d'inba ya Danna mata kira ringing d'aya yaji ta d'auka.

Sautin kukanta ya fara jiyowa ta cikin waya tare da cewa "Haba honey tun shekaranjiya nake kiranka kak'i dagawa Nifa ya kamata ace ma nayi fushi ka taho batare da kayimun bankwana ba Amma kai kake fushi me nayi maka baby ko ka daina so na ne"

"Cikin sigar lallashi ya ce " Kiyi shiru kinsan banason kukanki yanzu dai ya wuce ykk"

yanajin daga bangaren ta ta sauke ajiyar zuciya ita har mamaki take yanda MD bai iya bada hakuri ta ce "am okay dear please yaushe zaka dawo kewarka duk ta isheni"

"Lumshe ido yayi tare da budesu ya ce " ba rana sai nagama muhimmin aikin da ya kawoni"

.Kamar mai shirin yi kuka ta ce "Haba honey wani aiki ne da bazaka k'arasa yinshi ba a nan please kasan banason zamanka a Nigeria ina kishin yanda y'an iskan karuwan matan nan ke kallonka please my husband ka dawo"

"Cike da kosawa da magana ya ce" bana magana biyu Amera Kitaho kawai ki sameni idanma Kaduna ce bakya son zama saimu koma Abuja finally magana ta k'arshe"

"Cike da takaici Amira ta ce " Bazan dawo Nigeria ba Honey duk Randa ka dawo ina nan ina jiranka amma Bazan dawo k'asar da za a dameni a Takuramun ba"

"Tsaki MD ya ja Dan duk ta k'ara masa Haushi tsaki yaja tare da katse kiran yayi Wulli da wayar Dan itama duk ta gama chaza masa kai a ce ya na da mata amma bata biya masa buk'ata ai gaskiyar su ammy ne da suke cewa da shi da gauro ba banbanci.

Saboda Hajiya kaka ya dagawa gidansu Dan kullum ya je zance d'aya ne Fada kullum hakan yasa yayi zamansa a gidansa ya na hutawarsa Dan Yawaicin rayuwarsa hutunsa kadanne idan ba Kaduna ba yazo duk Inda yaje harkar kasuwanci bata barinsa sakat.

Kamar yanda jaber ya fad'a a one week din ya zo a lambun gidan suka zauna suna kurbar drink " Aje lemon dake hannunsa MD yayi ya ce "Ina sauraranka bloody wace shawarace ka ce kazo da ita".

Ya na fuskartansa jaber ya ce " Shawara ce Na yanke wacce nake tunanin ita ce mafita a gareka mafi sauki shine kayi *Auren wata Tara*

?da mamaki MD ya ce "What *Auren wata Tara* kuma Kamar ya ban fahimce ka ba ka kullemun kai ina gudun Karin Auren shine zakazomun da maganar da na guda"

"Murmushi Jabeer yayi tare da cewa of course wannan ita ce kad'ai damar da na hasaso maka zata zame maka mafita"

"Har yanzu ka sanyani a duhu fa kayi mun bayani me Kake nufi da inyi *Auren wata tara"*

Gyara zama jaber yayi tare da cewa yanzu zanyi maka bayani kuma nasan zaka fahimta "sannna ya d'ora da cewa.......✍🏿
*07026166536 domin magana da marubuciyar*

*hmm yanzu fa salon wasan zai fara fans Kudai muje zuwa*

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

*_Miss Hajo ce_*🤙🏿

👨‍❤️‍👨 *AUREN WATA TARA* 👨‍❤️‍👨

```MALLAKAR```

*Hajara L Sadeq*

🅿️............*25 & 26*

"Aure zakayi a sirri batare da sanin Iyayenka ko wani naka ba ka Aje Matar a sirrance har kayi mata ciki Kaikuma saikayi musu albishir da Amera ta samu ciki tunda ka ga ta na chan America ita kuma Matar zakuyi yarjeniya da ita ne akan Zaka aure ta na Wata Tara zata Haifa maka d'a ko y'a saika saketa sannan zaka biyata mak'udan kudi amma fa dole Saidai a samu y'ar talakawa nakasassu wacce basu da cin yau basu na gobe a rudata da kudi"

"Wani irin kallo MD ya dinga binsa dashi na baka da hankali kafin ya ce "

"amma bantaba sanin jaber baka da hankali ba sai yau wannan ai ba mafita bace maganar shirmece kazomun da ita Sannan ni kakeyiwa ikirarin da Auren y'ar talakawa neman haihuwa hauka ne wannan shawarar batayi ba nema ma kake duk ka b'atamun rai"

"Dage kafada jaber yayi ya ce " tunda hakan baiyi maka ba Ai shikenan amma kayi tunani wannan ce kawai mafita mafi sauki"

ya na gama fad'ar haka ya Mike ya ce "na Wuce Abuja akwai meeting din da zamuyi da wasu y'an kasuwa zan wakilceka Dan kwana biyun nan ka zama wani gashinan dai"

"MD ko tsaki ya ja ya na jin haushin wannan banzar shawarar da jaber ya kawo abun ma ya zama hauka ya fad'a ya na Jan tsaki"

Mikewa yayi kamar wani zaki tare da fitowa excort dinsa na ganinsa sukayi saurin bin bayansa tare da bude masa mota kai tsaye gidansu ya nufa.

A palour ya tarar da Hajiya ta mik'e kafa ruky na gefenta ta na chat ta na ganinsa ta tashi tare da cewa "Ina yini Yaya MD "

ba tare da ya Kalleta ba ya ce "Lafiya" fuskarsa a hade ya gaishe da Hajiya ta amsa da fara'a "Ammy ce ta shigo itama gaisheta yayi Bayan ta amsa ta zauna ta na Duba news a jarida.

Yayi minti Talatin ba tare da ya ce uffan ba Hajiya ce ta lura da akwai magana a bakinsa cewa ta yi " Yadai Naga kamar akwai magana a bakinka ka fad'a ta cikinka mana Malam "

"Cikin hade rai ya ce " daman akan maganar nan ce da mukayi Hajiya please ki janye shekara guda yayi yawa sannan fa haihuwa ta Allah ce Insha Allahu muna addua kuma kuka tayamu da addua za a dace"

"Wani banzan kallo Hajiya ta bisa dashi kafin ta ce.

" ka gama na ce Ka gama sanin Allah ne zaka gwadamun to tun kafin a haifi uwarka da ubanka nasan wannan nasan haihuwa ta Allah ce kajini da kyau da kunnan basira bari kaji dai nayi maka ta Mahaukacin kare "

"wallahi tallahi billahillazilla'ila ha illa huwa Matarka ta shekara bata haihu ba ko bata samu ciki ba Ko a kauye ne saina samo mata na aura maka ,"

"Ka ganni nan ni ba tsohuwar banza bace bana magana biyu kuma ka zuba ido ka gani badai ka na tsorantaba ta salamceka ba bazaka iya mata kishiya ba To ni nan da kaina zan Aura maka duk wacce tamun kuma dole ka zauna da ita ko ubanka da ya ke raye na sanya yayi Abu dole yayi bare kai k'aramun kwari ni wuce kaban wuri kayan takaici kawai shine hada wani daure fuska to a ganinka tsoranka zanji kome ko nima fatimar ce da kake zare mata ido ta kasa maka magana,"

" to ni ba ita bace wani had'e ranka na banza Sololon hofi ,gadara da iko da isa sai a waje a gida kuwa Tsigaggiyar matar da a tsaye kamar iccen kabari ta na Juyaka ita bama macen kirki ba ba wani kyau na azo a gani ba ba diri ba ba komai ba Abu k'ashi duk a waje Ko ina ma jin dad'i a wannan abar Har Kake like mata malam ga mata Duma Duma a gari sai ka zaba ka darje amma ka tsaya kana shashanci to wlh ka fita ido na in rufe Dan idan bakayi wasa ba idan bansa ka saketa ba kace ban haihu cikin Uwata da uba na da ruwan zamzam aka haifeni bada jini ba"

Tunda Hajiya ta fara maganar MD ya cika yayi famm ga haushinshi na kushe masa mata da take Hade rai yayi sosai tare da kauda kai "

Ammy ko shiru tayi sai d'an murmushi da tayi Dan gwara da Allah ya kawo Hajiya ko zata gyarawa MD zama "

Mikewa yayi ba tare da ya k'ara kallon ko d'aya daga cikinsu ba ya fita Ya na Jan tsaki.

"Da harara Hajiya ta bisa ta na tab'a hannu ta ce

" ohh ni Rukayya kujibi dai don Allah a haka a ido kamar zai tab'uka abun kirki nanko ba asan Solon Soson wanka bane dani kake zancen aini ba tsohuwar banza ba ce da zan zuba ido ina ganin tabaranci shekara Tara ana Abu d'aya to Abu yazo karshe na gaji kuma munsanya k'afar wando d'aya daku.
Chapter 18 · 0% Book details