Sashe 102
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"karka Cemun komai baka da bakin da zaka fad'amun wata magana "Sannan ta kalli driver tace jamu" Bayan Inda Zahra take Ammy ta zaga ta shiga "Motarsu ta tashi sosai zahra tayi mamakin Ganin Ammyn Chuchu me ya kawota gidan meye alakarta da Musty" Ganin ba amsa ya sanyata hade kai da gwuiwa tana hawaye "A sanyaye Ammy ta ce " Kidaina kukan nan kar kanki yayi ciwo"Duk yanda zahra taso shiru kasawa tayi Ammy na ganin haka ta janyota jikinta tare da Fara Lallashinta ta ce "Kiyi hakuri insha Allahu komai yazo karshe " Shiru zahra tayi tunani chunkushe a kwalwarta kafin bacci ya kwasheta a jikin Ammy tayi baccinta kallonta kawai Ammy take tana jin tausayinta na ratsa ta yarinyar abar tausaya wa ce Kamar yanda Chuchu ta bata labari ga maraici ga kuma halin da MD ya jefata Har mahaifinta ya shiga wani hali banda zargin mutane Har suka isa gida zahra batasani ba saida Ammy ta tasheta ta ce "Tashi Daughter munzo" a sanyaye zahra ta fito daga motar sosai tayi mamakin Ganin saukarsu gidan su Chuchu dan bazata mance gidan ba kama hannunta Ammy tayi a hankali take binta saboda cikinta da taga yayi girma har suka isa Babban palourn ita dai zahra na biye da ita Suna shiga palourn zahra tayi ido hud'u da chuhu Da gudu chuhcu ta Ruga tare da Rungumeta Da karfi saikuma ta sanya kuka Ammy ce ta ce "Ki bita a hankali Maryam bakiga yanda take " tsagaita kukan sukayi suka zauna Kan sopa Chuchu na dubar zahra dake hawaye Goge mata hawayen tayi ta ce "Kina.Lafiya sis?Gyada mata kai tayi har lokacin hawaye zahra take " Ajiyar zuciya Chuchu ta sauke ta ce "Kiyi hakuri momcy insha Allah komai yazo karshe Mikewa Chuchu sukayi tare da zahra Kallon Ammy da har lokacin ranta b'ace yake tayi ta ce " Ammy zamuje ciki"Okay tafada maki abunda take so a girka mata sannan ta huta sosai "To Ammy " Chuchu ta fad'a tana kama hannun zahra "Ki bita a hankali fa wajen hawa stairs " To Ammy Chuchu ta fada "koda suka isa d'akin Chuchu kasayin shiru zahra tayi Dan tun d'azu zuciyarta cike take da Tambayoyi Kallon Chuchu tayi ta ce " Sis Dan Allah na.tambayeki"Murmushi Chuchu tayi mata ta ce *bama saikin tambaya ba zanyi maki bayanin komai yanzu dai kiyi salla ki fad'a abunda kike so kici "numfashi zahra taja ta ce " Banason cin komai "wara idanu Chuchu tayi ta ce " taya zakice bakisoncin komai inke bakya so Unborn d'inmu yana so"Hararar wasa zahra tayi mata ita kunyar cikin nan ma take ta kauda kai Chuchu ta Kalleta ta sake cewa "please me kike son ci Dan Allah kinsan Na fad'awa Ammy Bazakici abinci ba fad'a zata maki " nafa koshi "ta bata amsa " okay bari naje na fad'awa ammy"Chuchu ta fad'a tana Mikewa saurin Rikota Zahra tayi ta ce "Ki bari mana karkije ki fada mata naji zanci koma meye " a a a ki fad'a a girka maki"girgiza mata kai tayi ta ce "Duk abunda kukayi zanci" Shikenan Chuchu ta fad'a ta ce "Bari naje na had'o maki ruwan wanka" gyada mata kai zahra tayi har lokacin mamaki take "Bayan Chuchu ta fito daga bathroom d'in Kallon zahra tayi ta ce " na hada kishiga kiyi bari naje na dawo"Okay "ta fad'a tana Mikewa a hankali Ta shiga toilet din sosai taji dad'in Wankan saboda ruwan dumin da Chuchu ta had'a mata Bayan ta gama ta d'aura towel a bakin gadon taga kaya marassa nauyi da Chuchu ta Aje mata d'auka tayi ta sanya tare da sanya Hijab tayi magrib da isha'i tana lazumi Chuchu ta shigo da plate din Farfesun naman rago d'ayan kuma lafiyayyan shinkafa da miya ce Samanta anyi yanke yanken kayan lambu da itama Tasha naman kaji a sama y'ar aikinsu da suka shigo Tare tazo gabanta ta Aje jug din dake d'auke da kunun Gyada da yasha madara cikin girmamawa ta ce " Ina yini Hajiya"Ina yini Zahra ta mayar mata Bayan barin mai aikin d'akin nan Chuchu ta tisata gaba saida ta kusa cinye naman shinkafarce ma ta kasa ci saboda kunun gyadar da ya cika mata cikin Dan sosai taji dad'inshi wajen 10 harsun kwanta ganin Chuchu bata da shirin mata wani bayani ya sanyata cewa "Baki fad'amun komai ba Chuchu" Shiru Chuchu tayi tanajin nauyin ta fad'awa zahra Yayanta ne yayi mata haka dak'yal ta iya tattaro jarumta ta ce "Tun ranar da yatafi dake Asmy tafadamun komai na *Auren wata taran* da kukayi wlh sis bantaba sanin yayana bane yayi miki haka sai dazu" mamaki cike da Cikin zahra ta ce "Kamarya Yayanki" Shiru Chuchu tayi kafin ta labartawa zahra komai d'aya faru har suka gane Yayanta shine ya aureta shiyasa har Ammy taje ta d'auketa sannan Chuchu ta Goge hawayen da suka zubo mata tana kama hannun zahra ta ce "Dan Allah sis kar dalilin wannan yayi sanadiyar shafar zumuncin mu nasan a halin yanzu ba Wanda Kika tsana sama da yaya na Dan Allah kiyi hakuri kar abunnan ya tab'a zumuncinmu" Sosai zahra tayi mamakin jin cewa Yayan Chuchu da take yawan musu zancenshi shine Mustaphan wannan shiru tayi mamaki duk ya gama cikata kenan d'an Ammy ne "Kinyi shiru sis bakice komai ba " Chuchu ta fad'a"Sai sannan zahra ta d'ago ta kalli Chuchu ta ce "Nayi mamaki ne sis Inajin bacci mu kwanta " Shiru Chuchu tayi duk tayi sanyi ganin yanda zahra tayi ta ce "Dan Allah sis kiyi hakuri ki daukeni tamkar y'ar uwa kar laifin yayana ya shafeni" Kirkirar murmushi Zahra tayi ta ce "Kibar maganar nan Chuchu babu abunda kikayimun mubar maganar kawai" Chuchu najin haka ga sauke ajiyar zuciya kwanciya zahra tayi kan makeken bed din Chuchu ta lumshe ido bacci take so ya d'auketa amma tunani ya hana....bangaren MD tashin hankalin daya shiga bana wasa bane cikin Sauri ya kira Jabir a waya bai samesa ba Innalillahi wa inna ilaihiraji'un kawai yake maimaitawa kafin yayi Sauri ya fito ya kwalawa driver dinsa kira kai tsaye Airport ya nufa ya wuce Kaduna koda isarsa gidansa dake nan din g r a ya nufa Yana son zuwa gidan Ammy amma baisan me zata masa ba saboda yasan tsananin fushi Ammy take dashi sosai yayi mamakin ya akayi Ammy tasan da maganar nan d'ayar number Jabir ya kira nan yaci sa. a ya d'auka baima jira komai ba ya ce "Kana ina Jabir ka maza kazo gidana dake gra ina kd akwai matsala babba" Daga bangaren jabir yasan daman da haka Koda Jabir yazo gidan Cikin tashin hankali MD ya ce "ya akayi Ammy tasan da maganar nan Jabir Bayan kasan dagani saikai sai Dr Aliyu sai ALLAH daga bangarena suka san da maganar nan taya akayi ta fita" Nan Jabir ya bawa MD labarin yanda sukayi da Ammy Shima yayi mamakin yanda sukasan maganar"Sosai MD ya shiga tsananin damuwa Daren ranar da idonsa bacci gagararsa yayi....washegari Around 9:am Ammy ta sanya Chuchu ta kira mata zahra tare suka isa palourn da Ammy take Wanda zahra kasa yarda ta had'a ido da Ammy tayi saboda wani irin nauyinta da take ji "A sanyaye kanta a k'asa ta ce " Ina kwana Ammy"Lafiya qalu takwara ya bakunta"Ammy tafada fuskarta d'auke da murmushi"alhmdllh "Zarah ta fad'a a hankali" shiru Ammy tayi kafin ta ce "D'ago ki kalleni zahra zamuyi magana" Sai sannan zahra ta iya d'agowa amma bata yarda sun had'a ido da Ammy ba tana wasa da yatsun hannunta ta ce "Tohm Ammy"saida Ammy taja numfashi kafin ta fara magana da cewa" Nasan Chuchu tayi maki bayanin komai Ba saina Kara maimaitawa ba ina mai baki hakuri akan dukkan abunda Babana yayi miki Dan banga laifinki ko Kad'an ba Kiyi Hakuri ki d'auki hakan a matsayi jarabawa ce kuma insha Allahu kinkusa cinyeta abunda nake so dake ki kwantar da hankalinki waje Daya ki nutsu kiyi hakuri Nasan anyi miki ba daidai ba ki daukeni tamkar mahaifiyar da ta haifeki karkiyi d'ari_d'ari dani ina son ki zauna a wajena ne Har ki haihu kafin muga yanda Allah zaiyi na bincika na samu labarin mahaifinki yanzu yaji sauk'i yana garin danginsa kiyi hakuri ki zauna damu har zuwa lokacin da zaki haihu saimuje tare ayiwa iyayenki bayani sannan a basu hakuri Sannan Abu na gaba da nakeson fad'a maki Ko babana yazo gidannan kar wani Abu ya k'ara hadaki dashi ko ganinsa kikayi kibar wajen kada wata alaka kota magana ta kara hadaki dashi karki sake ki sake masa fuska koda wasa kinji na fad'a maki " gyadawa Ammy kai tayi Alamun taji"Ajiyar zuciya Ammy ta sauke ta ce "Yawwa to Allah yayi miki albarka ya Rabaki da abunda ke cikinki lafiya " Shiru tayi Chuchu ta amsa da ameeen "ga Dr nan zaizo ya duba ki yanzu ki tabbatar kin karacin abinci sannan ta kalli Chuchu ta ce " ki kulamun da ita sosai Kuje Kuyi break fast an shirya muku a dining dake sama "Daman zahra so take Ammy tace Su tashi saboda jinta take kamar a k'aya tare sukayi break fast da Chuchu kafin Su fara hira sosai Chuchu ta dinga Jan zahra da Hira Wanda har saida ta samu da wartsake wayarta Chuchu ta jawo ta ce " Bari na kira Asmy nayi mata albishir"Lokacin da Chuchu ta kira Asmy tana kwance zazzabi ya rufeta daga bangaren Asmy ta ce "Tun jiya nake jiranki bakya d'auka nakagara Naji yanda kukayi dashi" murmushi Chuchu tayi ta ce"AI Albishir na kira na miki gama momcyn nan a kusa dani"Asmy batasan sanda ta mik'e ba ta ce "Da gaske ko wasa" Dariya Chuchu tayi ta ce "Ga kat ki gani" ta fad'a tana bawa zahra wayar murmushi tayi ta k'ara wayar a kunne a hankali ta ce "Hello sis" Ai Asmy batasan sanda ta buga ihu ba ta ce "wayyo Allah Alhmdll Alhmdllh Zahra kece kuwa" Murmushi zahra tayi ta ce "Karki batamun dodon kunne da Allah Malama " Dariya Asmy tayi ta ce "ba dole nayi murna ba karkiga yanda nayi kewarki Kina ina" chuchu ta mik'awa wayar Chuchu ta ce "tana gidannanmu" Gidanku kuma ina kika sameta "Dariya Chuchu tayi ta ce " akwai labari