← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 129

Sashe 49

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kinsan na Fad'a maki akwai kanwar mamanmu anan to shine takoma gidanta da zama ta na d'an rage Mata ayyuka saboda mijinta baya nan" ayya kice yanzu munzama mu biyu Gaskiya zamuyi missing nata sosai wlh"cewar chuchu"wlhko ai bama kadanba danma ai ba koda yaushe take Chan ba zata dinga dawowa nan" dukda haka dai Chuchu ta fad'a...washegari Bayan dawowarta daga lectures around 5pm tana kwance Kan sopa ta na Karatun exams din dake tunkaro musu shikuma yana operating a system "Kallonta yayi yaga ta maida hankalinta ga karatun da take Bayan ya gama aikin da yake a laptop ya linke ya Aje tunani ne yake karfa yayi gudun gara ya fad'a gidan zago taya za ayi Ace wata biyar yanzu da Auren amma bata samu ciki ba gashi har saura wata hudu yarjejeniyar su ta kare a ranshi ya ce " kodai matsalar daga gareni take?Amma ai Duk asibitocin da naje sun gwadani lafiya ta qalau to me hakan yake nufi "wani tunani yazo masa ya ce " Karfa aikin banza nake Yarinyar nan da abunda takesha tunda wayayyace zaiyi wahala ta yarda ta dauki ciki "wata dabara ce ga fado masa yace bari nayi mata low nagani idan hakane " Mamy"ya kira sunanta a hankali "Aje littafin dake hannunta tayi ta ce " Na'am"Karatun nan tund'azu kike yaci ki bari inba so kike ki hardace littafin ba "murmushi tayi ta ce " Ai da zan samu dama ma na hardace book din da zanji dadi sosai "Uhm kaji dictionary" y'ar Dariya tayi Kad'an ta ce "Uhm"Na tambayeki zaki bani amsa"? Gyada mashi kai tayi ta ce " idan har na sani zan baka ,insha Allah"kina son yara kuwa?Murmushi tayi ta ce "Ina so mana sosaima kuwa " kice mijinki yaji dadi zaki Haifa mai yara da yawa"Gabanta ne ya bada daram tunowa da Hafiz "murmushin da ya lotsar da dimple dinta ta ce " insha Allah"tana rufe fuska "murmushi yayi ya ce " Kenan ni bazaki Haifa mun ba "Wara idanu tayi saikuma ta turo baki ta ce " Matarka kaima ta Haifa maka mana nima mijina zan haifawa "yana jinjina Yarinta irin ta Zarah ya ce " Ayya ni ai matata bata haihuwa shekararmu Tara da Aure amma ko b'atan wata bata tabayi ba "cikin muryar tausayawa ta marairaice ta ce " Ayya wlh harkun bani tausayi Allah ya baku mai amfani Amma kuma kai kana son yara ne"ina sonsu sosaima kuwa tun kafin nayi Aure nake da burin Son yara ina sonsu sosai Wanda har nake tunanin sonsune da yayimun yawa yasa Allah ya jarabceni har yanzu bai bani ba"girgiza masa kai tayi ta ce "kadaina wannan tunanin kasa a ranka lokacin samun sune kawai baiyi Aure,Da Haihuwa Abu ne da Allah ya sanya musu lokaci dole sai lokacin Su yayi tukwana sukan zowa bawa ina maka fatan Allah ya baka masu amfani" Murmushin da baiyi niyya ba ya sakar mata ya ce "Hakane To Allah ya kawo lokacin" a ranshi ya ce "Ga dukkan alamu ba abunda take sha amma Indai hakane Tabbas ina cikin jarabawa ya zanyi da Hajiya kaka?Tabbas dole ne duk yanda za ayi Amera ta koma America kafin na samu mafita " Tunanin me kake ?ya tsinkayi Muryar Zarah "murmushi ya sakar mata ya ce " bakomai Please zaki iya girkamun tuwo irin na rannan"Shiru tayi kamar bazatayi magana ba saikuma ta ce "akwai kayan Had'in ne?Eh akwai komai a ciki" Okay Badamuwa ta fad'a tana Mikewa da Kallo ya bita harta shiga kitchen din kafin ya sauke ajiyar zuciya a ranshi yana mamakin yanda yake sauya wasu dabi'un game da halayyarshi idan yana tare da ita har yake tsayawa yayi doguwar Hira da ita ko Dariya da murmushi Wanda ko a gida bakowani lokaci ba yake yinsu a ranshi ya ce "Saboda Yarinyar simple ce bata da hayaniya?wata zuciyar kuma ta ce " saboda ka chutar da ita a farkon mu'amularka da ita Wanda idan bangyara mu'amula ta da ita ba ko Bayan rabuwarmu zata rikeni mugu a cikin ranta "da wannan tunanin har aka kira Sallar magriba sai Bayan isha'i Zarah ta gama Tuwon da miya ta juye a warmer a dining ta jera Kafin taje tayi Sallar isha'i Bayan tayi wanka ta sanya doguwar Hijab d'inta ta fito Zaune ta tarar dashi a palour yana cin tuwon cikin nutsuwa sosai MD yaji dadin Tuwon fiye da na rannan sai lumshe ido yake da hannu yayi mata nuni da good kafin ya furta " Thnks"a hankali"murmushi kawai Zarah tayi batace komai ba "Bazakici ba ?Sai anjima ta fad'a " a hankali"Zoki zauna muci tare"girgiza masa kai tayi ta ce "A a a " Sanin kanki ne banason musu ko?a sanyaye ta k'arasa ta samu guri gefen k'asar da yake ta zauna "ko kefa mumu girl" Wata irin harara ta banka masa kafin ta maida kanta kasa tana turo baki"murmushi kawai yayi "Cike da jin kunya Zarah takecin abinci bata wani ci da yawa ba ta ce ta k'oshi ba yanda baiyi da ita ba akan tadawo amma takiya ganin zata sanya masa kuka ya sanyasa cewa" Shikenan rigimammiya"tana turo baki ta koma Daki wayarta ta janyo ganin missed call ya Hafiz ya sanya tabi kiran saida ta katse kafin ya kira Hira suka fara Sosai cikin Sauk'i da k'aunar juna sosai suke waya Zarah na kwance saman bed tayi rubda ciki batasan har lokacin da MD ya shigo dakinba ba saida ta tsinkayi muryarsa da cewa "bani wayar " Cikin kid'imewa Zarah ta kashe wayar tana addu'ar Kar Hafiz yaji muryar MD "Dan Alla meye haka wai dan Allah idanfa yaji muryarka me kake tunanin zai faru" tsaki yaja ya ce "so what Dan yaji muryata baki da Gaskiya kenan" Shine fa Wanda zan aura"ta fad'a kamar mai shirin yin kuka"Ni kuma Wanda kike Aura a yanzu ba ?saiki bambance ni dashi wayafi matsayi "Tana turo baki ta ce " Kai ai mijin wucin gadi ne shikuma shine mijina na har abada "kwabe mata bakin yayi ya ce " Ki dinga sanin maganar da zakiyimun hope kin fahimta ko nayi maki kama da sa an wasanki sannan ya fusge wayarta dake ringing yabar dakin"takaici ya ishi Zarah rasa me zatayi tayi kawai sai ta fashe da kuka ta ce "Allah ya isa mugu azzalumi saikace shine ya sayamun wayar da zai amshe wlh nidai an cuceni da aka lakabamun wannan alkakaidin ya zamemun k'arfen kafa ke Asmy kina Chan kina rayuwarki hankali kwance ni kin barni da kunci tana wannan sabbatunta a haka har bacci ya kwasheta MD ko Shima kwanciya yayi yana buk'atar Ta amma wannan Karin bazai jeba Dan karyaja raini a wajen yarinya k'arama harta gane larurarshi ta kawo mashi raini Irin yanda Amera tayi masa Dukda Amera intayi masa babbace ita ko wannan karamar yarinyar da auren wuri ya haifi kamarta bazai yarda ta samu damar raina sa ba...washegari koda ya tashi a daddaure ya tashi ya koma MD dinshi na ainahi Zarah na ganin haka ta kasa masa Rashin kunyar da taso masa akan wayarta saboda muddin tana ganinshi a haka tofa bazata iya gaya masa maganaba ta rasa ya akayi mutumin yake mata kwarjini duk maganar da taso fad'a masa wani lokacin saita kasa a haka ta tafi lecture d'inta batare da ko magana ta had'asu ba inbanda gaisheshinda tayi ya amsa ciki_ciki a sch Asmy ta ce " wai ya akayi nayi ta Kiran numberki kashe sannan ina wayarki"tsaki Zarah taja Dan daman haushin asmy din takeji Dan duk ita taja mata wannan Abun ta ce "Bansaniba" Dariya Asmy tayi ta ce "Allah baki hakuri bani na kar zoman ba rataya aka bani" Tsaki Zarah taja tare da shiga motar driver da yazo daukarta batare da tayiwa ma asmy bankwana ba da dare around 10 tana karatu ya kira sunanta amsa masa tayi ba yabo ba fallasa "Zoki amshi wayarki''ya fad'a yana fito da wayar daga aljihunshi Dan yasan fushin nan da take Na wayar ne " Cikin Sauri ya Mike tare da zuwa "ta mik'a hannunta kenan zata amsa wayar ta subce mata ji kake tasssssss " Hannu aka Zarah ta d'ora ta ce wayyo Allah na ta fashe "Ya Allah MD ya fad:'a kafin ya yunkura ya d'auko wayar da tayi kwatsa_kwatsa kasancewar tilles duba wayar yayi yaga ai tagama amfani Zarah ko tuni harta fara hawaye ta ce Ta lalace ko"Baice mata uffan ba sai zaro sim din da yayi ya ce " ta gama nawa wayar take na biyaki"Dukda taji zafi a ranta amma hakan bazaisa ta ce zata sanyashi ramuwa ba Girgiza kai tayi ta ce " a a a ba saika biya ni ba tsautsayine ko a hannuna ai zata iya fashewa "yayi mamakin jin furucin ta dan A tunaninshi tuburewa zatayi ta ce saiya biyata baice uffan ba sai rike sim d'inta da yayi washegari Zarah harta hakura da waya Bayan ta dawo daga lectures Sannu yayi mata ta zauna tana maida numfashi " Amshi "ya fad'a " Kallon abunda yake nuna mata tayi taga kwalin waya ne "Ta wacece" ta fad'a a hankali"taki "ya bata amsa kai tsaye " wara idanu tayi tace Ni kuma ai bance ka rama munba baxan ansa ba "ba ramuwa bace kyauta ce Na baki" make kafada tayi ta ce "a a bazan amsa ba " saboda me?saboda dalilin ka yardamun yasa ka sayamun"Girgiza mata kai yayi ya ce "Daman nayi niyya ne ki amsa karki k'aramun musu kinsan abunda banaso kenan" A sanyaye ta k'arasa ta amsa tare da cewa "Nagode Allah ya saka da Alkhairi ya k'ara budi" murmushi yayi mata yanajin dad'in addu'ar tata so da yawa ya kanyiwa Amera kyauta ta millions amma godiyarta dashi kawai Thnks sai su I love you Amma ji yarinyar nan yayi mata y'ar k'aramar kyauta da bata kai ta kawoba tana masa irin wannan godiyar "Amen " ya amsa Chan cikin k'asar zuciyarsa "Bud'e kwalin wayar tayi taga An rubuta iPhone 12pro max a jiki " Dukda batasan kudin waya ba tasan mai tsada ce dubawa tayi taga harya mayar mata da sim dinta a jiki numbers ta shiga taga bako d'aya tunowa da batasanya icloud ba ya sanyata Dagowa ta Kalleshi ta ce "Ya Musty Dan Allah ka
Chapter 49 · 0% Book details