Sashe 25
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan komai ya lafa Sai sannan MD ya lura da aika_aikar da ya aikata bai tab'a tunanin Zai samu yarinyar a budurwa ba shiyasa har yayi mata mugunta a lokacin ana kiran asuba kunna glove din d'akin yayi Haske ya kauraye saida ya wara idanu ganin irin jinin da ya gani a zanin Gado Sosai ya rikice ganinta sume jijjigata ya fara Amma ba motsi rasa yanda zaiyi da ita yayi tagumi yayi ya sawa sarauta Allah ido,Firgit ya Mike tunowa da yanda yayiwa Amera a first night d'insu cikin Sauri ya jona ruwa a kettle kasancewar akwai nefa ruwan d'umi ya zuba a roba tare da d'iga ruwan Dettol da baya rabuwa dashi a toilet dinsa Cikin Sauri ya sungumeta tare da sanyata cikin ruwan ya fara gasata sosai yayi mamakin yanda ko motsi batayi ba Sosai yayi ta had'a ruwan zafi ya na gasata ko zai samu ta tashi amma ko motsi batayi ba cikin tashin hankali ya samu ya mata wanka Wanda bai yarda ya k'ara kallon surar jikin ta ba Dan gudun kara shiga wani hali Bayan ya gama mata ya fito da ita daman ya sauya bedsheet din kwantar da ita yayi tare da dauko mata rigar Amera dake gidan da suka taba zuwa sau daya ta kwana wani biki dan Sau daya ma ta taba zuwa gisan kasamcewar saita shekara nawa bata taka garin zaria ba ya sanya mata saida yayi wankan tsarki kafin yayi wani wankan ya fito Cikin Sauri ya shirya Zaune yayi bakin gadon ko zaiga farkawarta amma shiru Ganin Safiya ta fara ya sanyashi kabbara Salla a d'akin Dan ba damarma yaje masallaci. Har karfe Bakwai Zarah bata farka ba wanda hakan ya k'ara rud'ar da MD karfa na kashe y'ar mutane"ya fad'a cikin ransa"Saurin mikewa yayi tare da karasawa Inda take kwance numfashi ne kad'ai zai tabbatar maka da ta na raye "wani tunani ne ya fad'o masa yayi saurin daukarta tare da fitowa da ita harabar gidan a mota ya sanyata tare da shiga driver sit da gudu ya dannawa mai gadi horn ya zo ya bud'e masa bai zarce ko ina ba sai asibitin Dr Aliyu Emergency aka wuce da ita MD duk ya rud'e A office d'in Dr Aliyu ya zauna ya na dafe da kansa Bayan shigowar Dr kallonsa yayi ya ce " ina y'ar uwar tata ta ke? "Bansani ba Dr wani hali take ciki yanzu" ya fad'a damuwa k'arara a fuskarsa "Alhmdllh ba wani Abu bane rud'u ne da firgici ya sanyata tayi doguwar suma anjima zuwa 4 insha Allahu Zata tashi sannan za a rubuta mata magunguna Wanda zata dinga sha yanzu mun sanya mata drip " Boyayyar Ajiyar zuciya MD ya sauke Bayan fitar MD office d'in Dr yayi sauri ya kira jaber Bayan ya d'auka ya ce "kana ina Abokina yanzu Abokin ka ya kawo Zarah Asibitinmu ?Cikin tashin hankali jaber ya ce " what Asibiti Dr gamu nan zuwa yanzu"Minti goma ba ayi ba saiga Asmy da jaber sun shigo asibitin Asmy banda kuka ba abunda take Dan tun jiya ko bacci bata samu tayi ba saboda darurar halin da aminiyartata take ciki Dan ita kanta in banda tsoron kar wata guda ya cika hakan bata faru ba da ba abunda zaisa ta aikatama aminiyarta tata haka ta na kuka ta ce "Dr ina y'ar uwata?me ya sameta?. " Kwantar mata da hankali Dr yayi Ganin ta rude ya sanyashi kaita dakin da Zarah take kwance ta sameta Drip mak'ale ga tsintsiyar hannunta Batasan lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba Ta ce "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un na shiga ukku ni Asmy Zarah ki yafe mun Na chucheki banyi hakan da wata manufa ba saidan soyayyar da nake maki sosai Asmy ta Rungume Zarah ta na wani irin kuka. Nan jaber Shima ya shigo idan ranshi yayi dubu ya b'aci ga dukkan alamu ta karfi MD yabi yarinyar nan lokaci guda yaji wani tausayinta ya mamayeshi sai yanzu yake Dana sanin abunda suka aikata shida Asmy baitab'a tunanin MD zaiyi wannan Rashin imaninba Cikin damuwa ya juya tare da Danna masa kira ringing biyu ya dauka. Cikin b'acin rai jaber ya ce " yanzu MD abunda kayiwa yarinyar Nan ka kyauta harta kai ga ka kwantar da ita gadon asibiti wannan wani irin Rashin imani ne"tsaki MD ya ja tare da katse kiran ya wullar da wayar Kujerar mai zaman banza D'ora kanshi yayi ga sitiyarin mota kwata kwata ya kasa samun nutsuwa tunda abunnan ya faru Haushin kanshi kawai yakeji da ya afkawa yarinya k'arama Why na aikata wannan me ya kaini " kwata kwata ji yayi kasarma ta fice masa a rai a take a lokacin ba tare da ya waiwayi gidanshi na Zaria ba ya wuce Kaduna password d'inshi kawai ya d'auka ya wuce Airport ba tare da bata lokaci ba jirginsu ya d'aga America. ******* Asmy banda kuka ba abunda ta ke jaber yayi Lallashin Amma a banza wajen k'arfe Ukku Da Rabi taga zarah ta fara motsi cikin Sauri Asmy ta mik'e tare da isa Inda take ta ce "Sis ki tashi Dan Allah" A hankali Zarah ta fara bud'e idanuwanta da sukayi mata mugun nauyi Harta k'arasa budesu karewa dakin kallo tayi ta tabbatar da gadon asibiti ne take kai rumtse idonta tayi abubuwan da suka faru ne suka dinga dawo mata "innalillahi wa inna ilaihiraji'un" ta shiga nanatawa "Tunaninta abunda ya faru duk mafarki ne Dan bata tab'a tunanin ko a mafarki ba Asmy zatayi mata haka Da kallo tabi Asmy dake tsaye a kanta tana kuka ta ma kasa magana " a fili ta ce "Kardai kice mun Gaskiya ne Asmy ba mafarki bane nake ,Aminiyata Dana d'auketa y'ar uwa tamkar wacce muka fito ciki d'aya za a had'a baki da ita aci Amanata a rabani da budurci na " girgiza mata kai Asmy ta fara cikin hawaye ta ce "Ki tsaya ki saurareni Zarah banyi hakan....tsawar da Zarah ta daka mata ce ta sanyata Had'iye maganar da tayi shirin fitowa daga bakinta cikin tsananin b'acin rai Zarah ta ce " Get out Ki fita bana son ganinki bana k'aunar ganinki Asmy kin cuceni kinci Amanata Allah ya isa tsakani na daku Ki fita kafin nayi maki abunda baki tunani bana k'aunar ganinki a kusa dani "ta k'arasa fad'a ta na Fashewa da kuka mai cin rai"Sosai hankalin Asmy ya tashi ta na kuka ita ma ta ce " Dan Allah ki saurareni Zarah kece shaida bazan tab'a chutar dake ba na aikata hakan ne a saboda ceton rayuwarki da kuma soyayyar da nake maki ki saurareni Dan girman Allah Zarah"wata tsawar Zarah ta kuma mata wacce ya sanya Asmy saurin barin dakin ta na kuka kai tsaye office d'in dr ta nufa ta na kuka ta ce "Ya zanyi dr Duka munyi hakan ne saboda ceton rayuwarta da kuma tsaron lafiyarta me yasa bazata fahimceni nayi mata bayani ba Dr y'ar uwata a halin yanzu babu wacce ta tsana sama dani ta ce Na tafi bata son gani na" ta k'arasa fad'a ta na durkushewa tare dayin kuka mai cin rai"Cikin lallashi dr Aliyu ya ce "Karki damu Zata huce a halin yanzu ta na cikin fushi ne kuma dole tayi fushi dake Asma'u bai kamata Kuyi mata haka ba Da kunbi ta shawara ta da zamu samu mu.lallab'ata ne har ta amince kafin komai ya wakana" ta na kuka ta ce "Dr kaifa kace one months yayi akwai matsala gudun wannan ne yasa Muka aikata hakan ya zanyi da rayuwata ne waini Zarah takeyiwa Allah ya isa" Lallashinta jaber yayi tare da cewa "tashi muje Na maidake school insha Allah za a kula da ita a halin yanzu ta na fushi dake ne Idan ta huce saiki dawo" girgiza masa kai Asmy tayi ta ce "ba Inda zanje nabar Zarah cikin halin nan jaber " Lallashinta yayi ya ce "Akwai nurse din da zasu kula da ita ganin naki ne zai k'ara fama mata ciwon rad'ad'in da take ji tunda nace maki ki taho muje karkimun musu ko so kike mutanen asibitin nan su fahimci halin da ake ciki irin kukan nan da kike" Ba dan Asmy ta so ba tabi jaber ya maida ita hostel tunda taje take kuka Chuchu duk ta damu ta isheta da tambayar ina Zarah Hakan ya sanyata yi mata karya ta ce "Tun jiya ta tafi funtua Matar babanta ce ba lfy ita kuma kukan da take batajin dadine"... Bayan fitar Asmy d'akin wani irin kuka Zarah take Tanaji daman mutuwa tayi ta huta budurcinta da take ta tsarewa tsawon shekaru take tsananin alfahari dashi tayiwa mijinta na Aure na sunna tanadi shine a halin yanzu ta rasa shi a banza wani wanda baisan darajar d'an adam ba ya amsheshi kuma Had'in kai da Aminiyarta da ta yi matuk'ar yarda da ita " A haka nurse guda biyu da Dr Aliyu ya turo suka shigo Dak'yal suka samu suka lallasheta tabar kukan Dr Sakina ta ce "sister d'an mike muga kin iya tashi?Yunkurawa Zarah tayi zata Mike Azabar zafin da taji daga k'asar ta ne ya sanyata saurin rumtse ido tare da saurin komawa ta na hawaye ta ce " bazan iya ba Dr"Girgiza kai Dr Halima dake gefe tayi ta ce "Wlh mijin yarinyar nan bashi da imani Karkiga yanda aka kawota Na zaci ma sai anyi mata dinki Allah ya taimaka Bata k'aru ba" Dr Sakina ta girgiza kai ta ce "Ai mazan ne na yanzu jira suke Allah dai ya kyauta " Zarah ta na jinsu suna hirarsu ita dae batace uffan ba a ranta ta ce "Ai da mijin nau ne ma yayimun haka da da sauki amma wani Chan katon banza tsinanne a ranta ta ce " Allah ya isa tsakanina da kai mugu azzalumi macuci Fuskarsa da a halin yanzu babu mutumin da tafi tsana sama dashi ta shiga dawo mata Drip aka k'ara sanya mata kafin Su bata magunguna ta sha bayan sun taimaka mata sun mikar da ita dukda tana rurrumtse ido toilet suka shiga saida suka kara gasata cikin ruwan dumi da dettol da gishiri sosai dukda ta na ta musu raki bayan sun gama gasata ta danji dadi kadan wanda yanzu