← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 129

Sashe 91

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dawo sabo kafin ta daure tayi alwala akan lallausan carpet din d'akin tayi salla jingina tayi da Gado tana rusa sabon kuka mai tab'a zuciya MD koda ya shiga ya ganta cikin wannan halin sosai ta daga masa hankali "Cikin tausassar murya Wanda kana jinta kasan Shima a tashin hankali yake ya ce " Dan girman Allah Mamy ina begging d'inki Dan Allah kiyi hakuri ki nutsu karki sanya kanki cikin wani hali ki sanya yaron dake cikinki "D'ago da idanunta da sukayi ja tayi tare da banka masa wata irin harara ta ce " kai har kana da bakin da zakayi mun magana akan Abunda ya shafi rayuwata wani hali kuma zanshiga Wanda yafi Wanda ka sanyani cikinsa Sannan cikin da kake magana kama daina sashi a lissafi Dan wlh kaji na rantse bazan haifesa ba bazan haihu da mutumin da ya ruguzamun farincikin rayuwataba bazan haihu da mutumin da yayi sanadiyar shigar mahaifina cikin wani hali ba ka cuce ni ka zalunceni......"kuka ne yaci karfinta ta kasa fad'ar abunda tayi niyyar fad'a rumtse idonsa MD yayi yanajin zuciyarsa na wani irin zafi da rad'ad'in maganganun nata a fahimtar sa kenan dalilin bayyanuwar cikin nan ya sanya mahaifinta shiga wani hali Tabbas dole ne yayi bincike sosai yakejin zafi idan tace zata zubar masa da ciki "Shiru yayi na d'an lokacin yana sauraran kukan nata da yake jinshi kamar ana d'iga masa darmar wuta kafarsa ya Kalla da tayi kumburi ga rad'ad'i da take na yankan glass din da ya shige masa danma kwalbar ta fita amma wannan bai dameshi ba hankalinshi yana kan yanda zai samu ta fahimcesa sosai MD ya shiga yi mata magiya da ban hakuri akan ta nutsu suyi magana amma takiya sai kuka da take tana ja masa Allah ya isa 'Ganin ta tsagaita kukan ne ya sanyashi cewa" Dan soyayyarki da fiyayyen halitta Annabi muhammad (s a w ) Wanda akayi duniya dominsa mukecin darajarsa kiyi hakuri ki nutsu muyi magana na had'aki da girman Allah da manzon sa Mamy badan ni ba girman da darajar Wanda na had'aki dasu zaki duba "Shi kanshi MD baisan ya iya magiya haka ba Dan baitabayi ba baitab'a rokon wani Abu ba a wajen wani tunda yake idan ba a gurin mahaliccinsa ba Amma yau shine yake magiya yana rokon yarinya k'arama tana batsewa gaba d'aya ta since masa notin kansa " Zahra batayi niyyar sauraransa ba Amma darajar Wanda ya had'ata dasu yasanyata tsagaita kukan ta d'ago kanta daga hade kai da gwuiwar da tayi tana Goge hawayen ta kauda kai Alamun tana sauraronsa "Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce " Me kikeso kike da Buk'ata da zakibar kukan nan Banason ganinki cikin halin nan ki fad'amun me.kikeso"cikin muryarta data fara dishshewa ta ce "Abunda nake so mai sauki ne na farko ka sakeni ka fita daga rayuwata har abada ko a hanya ka ganni.karka nuna ka tab'a sanin mai suna na ma ka rabu dani Na har abada na biyu Kuma ka kaini a zubar mun da Cikin nan...ta k'arasa fad'a cikin kuka" Tirk'ashi ai abunda ta lissafo MD baijin zai iya d'aya daga cikinsu musamman cikin d'aya kwallafa ransa a kanshi"fuskarsa ba walwala ya ce"ki daina maganar zubar da cikin nan Mamy ina son kaya na Ina kaunarsa Fiye da komai nawa da na mallaka ki taimakeni ki haifamun shi please Dan girman Allah "wani irin kallo na baka da hankali zahra ta bishi kafin ta ce " ohhhh wai a tunaninka ni zahra zan Haifa maka cikin nan to tun wuri Inma mafarki kake ka maza ka farka Dan wallahi tallahi kaji na rantse bazan haifi cikin nan ba ko ka kaini a zubar mun dashi ko kuma wlh na zubar dashi ta karfi da yaji"dafe kansa MD yayi dake matuk'ar sara masa yanajin wani irin daci idan yaji tace zata zubar masa da ciki "cikin dauriya da k'arfin hali Dan kansa wani irin ciwo yake masa ga tension ga kwanan zaune da yayi ya ce " Na shirya mallaka maki komai nawa dana mallaka kudi,kadara,componynnika na ,gidajena nako ina wallahi tallahi kinji na rantse na shirya sadaukarwa miki da komai nawa hatta gidajena bazan bar kaina da komai ba indai kin yarda zaki Haifa mun cikin nan wlh a shirye nake da baki Duka dukiya ta akan cikinnan yafiye mun komai Dana mallaka Abunda najima ina burin samune tsawon rayuwata shine yanzu na samu Mamy ki dubi girman Allah karki zubar mun da ciki a shirye nake da mallaka maki dukkan abubuwan nan Dana lissafa maki madamar zaki Haifa mun cikinnan saboda ina masa tsananin soyayyar da bantaba yiwa wani mahaluki irinta ba ,"wani banzan Kallon zahra take binsa dashi na tsana kafin ta ce"a tunaninka dukiya ita zata iya baka komai,a tunannika duk wannan abubuwan daka lissafo zanyi kwadayinsu ne yasa harnaji ina sha'awarsu na Haifa maka cikin nan to tun wuri ka sauya tunani k'aramar kwakwalwarka ta fad'a maka da daidai ba Ina son ka sani ba komai kudi ke iya saya ba ,baka da kud'in da zaka sayeni dasu ,Kai har kana da kud'in da zaka saye ni dasu to idan baka sani ba ka sani ni zahra bana sha'awar dukiyarka,bana kaunarta,kuma babu abunda zanyi da ita ,bakada kudin da zaka ribe ni da su wlh ,baka da wannan ikon koda kudinka Sunkai tundaga sama har k'asa "ta k'arasa fad'a tanajin wani irin dacin takaici a cikin zuciyarta " Sosai MD yayi mamakin yanda yarinyar ke fad'a masa magana son ranta kwata kwata gani yake ta sauya kamar ba zahrar da ya sani bace a baya mai saukin kai da saurin Sauka ,rasa ma abunda zaice mata yayi sai kallo d'aya dinga binta dashi Mikewa yayi batare da ya sake kallonta ba yayi palourn Yajima yana sake sake a ransa Ya zaiyi da rayuwarsa ne Wai "tunowa da bata ci komai ba ya sanyashi saurin zabura Tare da mik'ewa yafita compound din gidan ma'aikatan dake gadin gidan ya kira Tare da umartarsu su da suyo masa take away na abinci kala biyar " kafin ya juya Dan a cikin biyar d'in ta zab'a Wanda takeso yana palourn har aka kawo abincin A plate ya juye d'aya Bayan daya kafin ya d'auka ya fara d'aukar biyu yayi bedroom d'inta dashi yanda tabarya haka ya sameta ta hade kai da gwuiwa tana kuka shi yanzu baimasan da wasu kalamai zaiyi amfani wajen Lallashinta ba "zaunawa yayi tare da Aje Plate din Abincin Duka biyun a sanyaye ya ce " Ki taso kiyi break fast "Zahra kamar jira take tana gadowa ta kalli abincin da Kallesa D'aukar plate din Duka biyun tayi tare da watsa masa tundaga saman rigasa har kasa ga zafin abincim" MD baitab'a expecting haka daga Wajenta ba Kallon kanshi yayi da kalleta tare da Kallon abincin data bata masa kaya dasu Miyar soyayyan dankalin dukta bata masa farar shadda "Baice mata uffan ba sai barin dakin da yayi tare da komawa Bedroom dinsa shi kanshi yayi mamakin da bai iya cemata komai ba Yasan dai duk duniya Bayan Ammy babu wacce ta isa tayi masa haka a duk fadin duniyar nan ya rabu da ita shi kanshi har mamakin kanshi akan yarinyar yanda harta iya d'aga baki ta dinga gaya masa maganganu son ranta saida ya sake wanka ya sauya wasu kayan kafin ya fito hankalinshi gaba d'aya yana kanta bataci komai ba wani Abu zai iya affecting cikin dake jikin ta " amma yasan ko yaje da wani abincin bazata sauraresa ba "Wayarsa ya janyo tare da dannawa jaber kira Jabir yanajin muryarsa yasan cikin damuwa ya ce " Yadai bloody meke faruwa?Numfashi yaja kafin ya ce "Jabir ina son kayi mani wani taimako? Inaji Jabir ya fad'a daga wayar" Akwai mahaifin yarinyar nan da nake tunanin bashi da lafiya ina son ka binciki Chuchu ta fad'a maka asibitin da yake duk wani taimako daya kamata da ni zanyi kayisa kome ake ciki ka kirani sannan a sauya masa Asibiti duk yanda likitocin sukace idanma waje ta kama a fitar dashi kome kenan na bar maka ragamar kula dashi a hannunka"daga bangaren jabir ya ce "Insha Allahu baka da matsala Aboki amma Bazan tambayi Chuchu ba saboda kartai zargin wani Abu tunani na general hospital d'innan da na gansu a nan ne asibitin da yake yanzu zanje garin na bincika tunda nasan gidansu kaga komai mai sauki ne karka samu damuwa" numfashi MD yaja yanajin yarage y'ar Kad'an daga cikin abunda ke damunsa ya ce "sainajika idan ansamu yanda akeso ka kirani" yinin ranar ba abunda zahra taci a cikinta dukda irin yunwar da takeji har juya ke daukarta amma batajin zata iya cin abunda ya fito daga hannun mutumin nan da takejin tsanarsa a ranta bangaren MD ma hankalinsa tashe yake bai iya sanya komai a cikinsa ba sai fresh milk yinin ranar daga ita harshi Cikin tashin hankali Suka yishi Dan sosai ta d'agawa MD hankali washegari ma haka zahra harta fara fita daga hayyacinta da komai bibbiyu take ganinsa kwana biyu kenan ba abinci cikinta sai ruwa da Takesha yanzu babu abunda take da muradin sama da tasamu hanyar da zata zubar da kadararren cikin nan Kallon cikin tayi Wanda da a haukanta kiba ce ta fara taga harya so ya fara fitowa batasan lokacin da ta fara bugun cikinta da hannu bibbiyu ba iya karfinta sosai take bugun cikin dukda azabar zafin da takeji tana cikin Bugawa taji wata irin azaba batasan lokacin data k'walla wani uban k'ara ba Wanda daga nan bata Kara sanin Inda kanta yake ba ta zube a wajen summammiya MD daga palour ya jiyo Karan da tayi ba shiri ya Ruga d'akin yanda ya sameta ne ya yi tsananin tayar masa da hankali kwance k'asar tiles ga jini da ya ga ya fara fitowa daga kasanta a matuk'ar tashin hankali ya nufi Inda take tare da Fara jijjigata yana kiran sunanta shiru Ba shiri ya sungumeta a guje yayi waje da ita makullin motarsa dake kan centre table ya d'auka cikin tashin hankali yayi waje yana bud'e motar ya sanyata a baya tare da Juyawa gidan Gaba a 360 ya figi motar tare da dannawa mai gadi wani Mahaukacin horn kafin ya isa da motar get
Chapter 91 · 0% Book details