Sashe 59
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tabar wajen nan. Wayar" shiru Yusuf yayi Dan maza basa shiga hostel din mata kuma yaga harta shige hostel Hango su Asmy a wajen da yayi ya sanyashi amsa ya ce "badamuwa bari na ba y'an uwanta su kai mata" Yawwa Abokina na gode "su Asmy na karasowa yusuf ya mik'awa Asmy wayar ya ce " Dan Allah Zarah zaki mik'awa wayar idan kun shiga"ba tare da sun kawo komai a ransu ba ta ce "okay" suna shiga Lokacin Zarah na Danna waya "Gado Chuchu taje ta haye tana maida numfashi Dan kanta ke ciwo mik'awa Zarah k'aramar nokiar Asmy tayi ta ce " gashi Akace wai a baki"da mamaki Zarah ta ce "Nikuma" bata k'arasa maganar ba saka makon ringing d'in da wayar tayi Kallon number tayi taga An rubuta oga a jiki Kallon Asmy tayi itama ta Kalleta ta ce "Ki d'auka Inajin ko wayace zakiyi" da wa kuma"Zarah ta fad'a tana turo baki"ki amsa kiji ko meye cewar Asmy a sanyaye Zarah tayi picking call din"Jin shiru ya sanyata cewa Hello "Cikin sayayyar muryarta " Daga bangaren MD saida ya lumshe ido "Jin shiru ya k'ara sanya Zarah cewa " Hello ko ba aji"nan ma shiru Ba ansa dubawa tayi taga har lokacin ba a katse ba cike da jin Haushi ta ce "Zanfa kashe tunda baza ayi magana ba " Sai sannan MD yayi k'arfin halin cewa "Hey" saida gaban Zarah ya bada daram jin muryar da ta jima batajita ba saurin fusgewa tayi tare da hade rai tamau ta ce "waye" Mijinki ne"Ya bata amsa kai tsaye"Waro ido Zarah tayi kafin taturo baki kamar yana gabanta ta ce "Ni ai bani da miji budurwa ce" daga bangaren MD murmushi yayi ya ce "To Mijinki na Wata Tara" Hararar wayar tayi kafin ta maida kunnanta tana turo baki tayi shiru"Chan Bayan few seconds ya ce "na turo a daukeki kince bazakizo ba why?Ta tsinkayi muryarsa "Bana ra'ayi " Ra'ayin me?zuwan?Okay to ni ina ra'ayi "tsaki taja a ranta ta ce " Dan rainin wayau kawai to bazanzoba "a fili kuwa cewa tayi " saika hakura"bansan hakan ba "Hakurin?Eh" To sai kayi kuka"dukda baison yi Dariya saida ya danyi Wanda hartajiyo daga wayar ya ce "Kina son ganin kuka na?Gyada masa kai tayi kamar tana gabansa" magana zakiyi"Eh"saboda me '"Dan naga zaiyi maka kyau ko muni zaiyi maka"yar Dariya yayi ya ce "Aiko har abada bazaki ga kukan nawa ba" Uhm idan kuma nagani fa kace me"Kasaitaccen murmushi ya saki ya ce "bama zaki gani ba Ai har abada " Banda dai cika baki idan kuma na gani fa saikaji kunya ko "Murmushi ya k'ara saki ya ce " Daga ranar da kikaga kuka na zan mallaka maki katafaran gida na dake Abuja Wanda nafiji dashi a Duka gidajena"Dariya da bata shirya ba Zarah ta fashe dashi Dukda Chuchu hankalinta bai kansu saida ta d'ago ta Kalleta bare Asmy dake gefenta "Cikin murmushi ta ce " Nikuma nayi maka alk'awarin insha Allahu sai naga kukanka"Okay haka kika ce kenan"uhm"murmushi ya saki ya ce "Ki rubuta ki Aje " Kaima ka rubuta ka aje"ta mayar masa "Naji yanzu dai ki biyo driver please" Wai me zanyi maka idan nazo"har zai mata Tsawa saikuma ya tuna Lallashinta yakeson yayi tazo cikin k'asa da murya ya ce "Ina son ganin ki ne" Uhm haka dai kace"Hakane ma ai "ki biyosa please" Zan duba ta fad'a "Ajiyar zuciya ya sauke ya ce " saikinzo Mamy "Murmushin da bata shirya saki ba ta saki jin ya kirata da sunan da idan ya kira ta ta rasa dalili takejin dad'in sunan Bayan ya katse wayar kallonta Chuchu tayi ta ce " dawa kike waya haka nasan dai ba hafiz bane "Murmushi Zarah tayi mata ta ce " idan fa shine"nasan ma ba shi bane saboda baki sakin jiki kina Hira dashi harda Dariya haka karfa wani ne yake kokarin kwacewa Hafiz da yayana da ba ama sashi a file ba fada "Dariya Zarah tayi ta ce " Baki da dama Daughter bari na shirya zan wuce gidan Aunty "Kallonta Chuchu tayi ta ce " Aunty kuma Kina nufin wannan Karin ma Chan zaki koma nidai wlh banaso "ta fad'a tana turo baki gaba" Dan murmushin dake lotsar da dimple dinta Zarah tayi ta ce "Zan dawo ai daughter Asmy dai tagumi tayi ta Lula duniyar tuni tasan wannan wayar da Zarah take yanda ta sakar masa jiki ko Hafiz bata waya dashi haka Dan tagane mai kiran kallo d'aya Zarah tayi mata taga yanda ta dirmiya a duniyar tunani saida ta sake wanka Kafin ta shirya ta sanya atamfarta mai blue da fari Riga da sicket sannan ta zunbula hijab d'inta blue har kasa batayi make up ba taji wayar ta sake ringing tsaki taja a ranta kafin ta daga tana turo baki ta ce " gani nan fa"tana gama fad'ar hakan ta katse Kallon Chuchu tayi ta ce "Sai nadawo" Okay to momcy a dawo lfy"Tashi Asmy tayi ta ce "Muje na rakaki" tare suka fita Kallon Zarah Asmy tayi ta ce "Naga yanzu kin saki jiki da mutumin nan please kar haka ya baki damar da zaki fad'a masa garinmu saboda ina gudun matsala wlh gabana sai fad'uwa yake ga Hafiz da ya kusa dawowa ga bikinki na k'aratowa Zarah banason Asamu matsala banason na zama silar bullowar wata matsalar" ganin yanda tayi sanyi ya sanya Zarah yin murmushi ta ce "Karki damu sis ba wata matsala da zata faru insha Allahu karki damu ai komai ya kusa zowa karshe" hakane har bakin motar Asmy ta rakata suna isa gidan a bude ta iske kofar palourn tana turo baki ta shiga da Sallama a bakinta cikin miskilanci ya amsa sallamar kasa_kasa k'arasa shiga palourn Zarah tayi cikin sanyi tare da samun guri ta zauna Dagowa yayi ya Kalleta yaga ta wani had'e rai kamar ba itace ta gama Dariya a waya ba kamar ba zai magana ba saikuma ya ce "Ba gaisuwa ko Mamy" Sai sannan ta d'ago ta Kallesa kamar bazatayi magana ba saikuma ta ce "Ina yini" kasa_kasa "banaso tunda saida na roka " Turo baki gaba tayi tare da kauda kai "Ganin miskilanci takeji ya sanyashi kyaleta take away ya sanya aka yo musu kallo d'aya tayiwa abincin tace " na koshi"saboda me?ya tambayeta fuska ba wasa"banason cin abincin waje"Saina ina"Nafison na girka?ta bashi amsa kai tsaye "Okay kiyi hakuri ki daure kici yanzu kafin anjima za a kawo kayan amfani a kitchen din shiru tayi saikuma ta ce " na k'oshi banjin yunwa"Saikinci kinsan banason gardama "shiru tayi saida tayi minti kusan biyar kafin ta dauki take away din tana turo baki" a zuciyarshi ya ce "na lura yau wani miskilanci takeji Aiko gidan kikazo," Yinin ranar Zarah kin sake masa tayi tun Baidamu ba harya dawo kuma yana tunanin ko wani abun yayi mata Bayan magriba ya aika driver ya cika kitchen din da duk wani abun girki da za a buk'ata sannan ya cika fridge din kitchen din da kaji da su kayan miya Da sauran abubuwan da bazazu lalace ba a fridge Bayan isha suna zaune a palour Zarah na karanta alqur'ani cikin zuciyarta kallonta MD yayi yaga yanda ta maida hankalinta ga wayar har bata San yayi mata magana ba saida yaje ya amsa wayar kafin firrgit ta dawo hankalinta duba abunda take a wayar yayi yaga qur'ani ne take ciki mayar mata da wayar yayi tare da cewa Ki hadamun cope ki kaimun daki "Yana gama fad'ar haka yayi Hanyar d'akin saida ta gama surar da take kafin ta Aje wayar ta sata airplane cikin k'ank'anin lokaci ta hadamai had'adden tea Wanda yasha ganyayyaki Dan taga ganyayyakin hada tea a abubuwan da aka kawo Bayan ta gama a k'aramun cup ta zuba masa tare da nufa hanyar d'akin da yake saida tayi knoking ya bata umarnin shiga Zaune ta samesa laptop gabansa Dagashi sai kayan bacci a ranta ta ce " bashi da Aikin da ya wuce danna system "A sanyaye ta k'arasa d'akin tsaye tayi kamar bazatayi magana ba saikuma ta ce " gashi"shiru yayi na d'an second kafin ya d'ago ya Kalleta yanda ta wani had'e rai ya ce "A garinku haka ake kawowa miji abinci" Turo baki gaba tayi tare da kauda kai"a ranta ta ce "wani sabon duniyancin kuma da kazo dashi" tsinkayar muryarsa tayi da cewa "Zoki Aje" Ya nuna mata center Table d'in dake gefenshi"Yunkurawa tayi ta Aje zata Mike da hannu d'aya ya Fard'o ta jikinsa wara idanu tayi saikuma ta fara kokarin tashi daga kanshi"a kunne ya rada mata "wannan shashan maganin da kike na meye" Bakomai fa"ta fad'a kamar zatayi kuka Kara janyota yayi jikinsa yace "Ko duk kewa ta ce da kikayi" turo baki tayi gaba ta ce "Allah kiyaye ni nayi kewar...bata k'arasa fad'ar abunda takeson fad'a ba ya had'e bakinsu waje daya.....washegari da shirin sch ta tashi a lokacin yana kwance idonshi lumshe yanajin wata irin nutsuwa da rabonshi da ita tun rabuwarsu ta k'arshe da Zarah itako tana gaban mirror tana shafa ta Cikin mirror din yake kallon yanda take shafa hoda cikin nutsuwa dimple dinta two side ya karema kallo yanda suka lotsa sai sannan ya k'ara karewa fuskarta kallo ba fara bace Chan ba haka ba baka ba irin skin d'inta ne ake kira da choculate colour saboda yanda fatar tata take luf_luf babu kurji ko kwarzano a fuskar kamar bata shiga rana hips d'inta ya dinga kallo da hijab din data sanya ta d'an lafe mata a jiki " zan tafi?muryarta ce ta dawo dashi daga duniyar tunanin d'aya Lula "Nawa zaku fito lectures" 4pm"ta basa amsa"Okay 4:30 driver zaizo "shiru tayi " Bata basa amsa ba dan harga Allah basan kwana gidannan take ba "10k ya kirgo ya mik'o mata " Kin amsa tayi "hade fuska yayi yace " kinsan dai bansan musu"a sanyaye tace "akwai kudi a hannu na shiyasa " To wannan din nake son ki amsa "ya fad'a fuskarsa ba wasa" badan taso ba tasa hannu ta amsa ta ce "Nagode" tana gama fad'ar haka ta fita tana turo baki...tun daga ranar nan kullum Zarah anan gidan take kwana Saboda driver ke kaita sch ya maido ta MD ko koda yaushe yana