← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 129

Sashe 33

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Chuchu ma Yafi goma Banda na Hafiz Shima rututu gabanta ne ya bada daram To me ma zata ce Musu ina zatace ta kwana tsaki taja ta ce mugu azzalumi kawai ya satoni Dan zalinci tana juyi da wayarta kiran Hafiz ya shigo kamar bazata dauka ba saikuma ta d'auka cikin sanyin murya tana ji daga bangarensa ya sauke ajiyar zuciya Tare da cewa "My luv ina kika sanya wayar jiya nayi ta kira Baki d'auka kinsan kin sabarmun sai Naji muryarki nake iya Bacci "cikin sanyi ta ce " Sorry ya Hafiz nayi bacci ne da wuri jiyan ina kwana"Lafiya qalau my love fatan kin tashi lafiya "Alhmdllh yau baka da lectures safe ne " Yanzu nake shirin Tafiya Hankalina bai kwanta bane sai yanzu ya kwanta da Naji muryarki gimbiyar tawa "kasaitaccen murmushi ta saki Wanda ya lotsar da dimples d'inta " Daidai shigowar MD da leda a hannunsu kallo d'aya yayi mata yaga yanda take magana kasa kasa tana murmushi Ledar ya Aje tare da Yin hanyar fita kamar bashi yayi maganarba ya ce"Idan kin shirya kya iya fitowa "bai jira me zata ce ba ya fice katse wayar Zarah tayi Bayan sunyi bankwana taje ta daga Ledar daya shigo da ita latsetsiyar doguwar Riga ce mai.kyau da gyalenta sai brush da kuma take away din Indomie da kwai" tsaki taja tare da cewa "ko wa yace masa ina buk'atar Wasu kayan inbanda tsabar kinibibi har wata indomie ce a take away " ta fad'a tana kuma Jan wani tsakin Brush tafarayowa Bayan ta fito ta Dauki indomie d'in taci Dan yunwa take ji cikinta banda karan yunwa ba abunda yake Tana gamaci cikin minti baifi sha biyar ba tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar daya sayo mata ta ninke tata tare da sakawa cikin Ledar waccen wayarta da d'auka ta hand bag d'inta ta rataya Bayan ta yafa beil din rigar sosai rigar tayi mata kyau ko madubi bata tsaya duba ba ta fito Zaune ta tarar dashi Da kayan exercises jikinsa yana rik'e da remote hankalinshi na kan tv gefenshi taja tsaya ta hade rai kamar bata tab'a Dariya ba Shiru tayi batayi magana ba Ganin Shima bazai yi mata magana ba agogon dake manne a palourn ta duba taga 8:40 gashi 10 take da lectures ya sanyata cewa "ka budemun Na tafi ina da lectures " Baice mata uffan ba kusan 5 minutes hakan sosai ya k'ara Kular da Zarah Chan kuma taga ya Mike yayi Hanyar Bedroom dinsa ta na tsaye ta cika tayi Fam gajiya tayi da tsayuwar ta zauna ta sawa sarauta Allah ido tayi tagumi Ba ayi 10 minutes ba Taji fitowarshi Ta gefen ido ta Kalleshi taga ya shirya cikin wasu K'ananan kaya kauda kanta gefe tayi hanyar kofa taga yayi tare da cewa "follow me" Yayi ficewarsa tsaki taja ta ce "Aikin banza Sai wani shan k'amshi Da gadara da isa yake saikace ba shine jiya ya gama....saikuma ta rufe bakinta ta tashi cikin Sauri tabi bayansa Parking space Taga ya nufa Tana nan tsaye har yazo Inda take daidai Inda take Ya tsaya Tare da bude mata front sit ta ciki Ajiyar zuciya ta sauke Tare da shiga Suka d'auki Hanya cikinsu bamai cewa uffan " Ina ne Inda kiken"ta tsinkayi muryarsa "tana kauda kai ta ce " A B U"Daga haka ba Wanda ya k'ara cewa uffan har Suka isa Bud'ewa tayi ta fita tare da banka masa kofar da karfi kamar zata karye tayi gaba da Kallo ya bita Tare da Jan tsaki Ya ce "Stupid Matsala kawai"Allah ya sanyama tinted ne motar ba Wanda yasan shine ya juya yabar sch din. Zarah ko tana fitowa daga motar taci.karo da Asmy da Chuchu Alamun sun fito daga lectures Bin motar da Kallo Chuchu tayi Itama Asmy haka Zarah ko gabanta saida ya fad'i ganin irin yanda Chuchu kebin motar da Kallo Har sukaga ficewar motar daga wajen da mamaki suke Kallon Zarah Chuchu ce tayi k'arfin halin cewa ..✍🏿
Chapter 33 · 0% Book details