Sashe 115
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mudan anyi butulu mugu azzalumi macuci insha Allahu karshenka bazaiyi kyau ba saikayi mutuwar wulakanci makaskanci " Harbin da yayiwa Matata ne A kirji ya k'ara rud'ar dani da shigar dani cikin tashin hankali daidai lokacin da naga shigowar zahra D'akin tana shirin shigowa Na ce "Ki gudu zahra karki shigo ki gudu karki yarda mugayen nan su kamaki zahra ina son ki tsira juyawar da zasuyi Su bita tana ji tana gani ta Ruga a guje inaga lokacin da wasu daga cikinsu suka mara mata baya kafin kuma Naji Jiniyar y'an sanda cikin tashin hankali Suka rude mudan yace mu maza mu tafi Harbin nan da nayi ne ya janyo hankalin jami" an tsaro d'aya daga cikinsu ya ce "To shikuma wannan yazamuyi dashi" mu tafi dashi mun kasesa a.hanya suka fad,a suna sungumata kamar wani yaro Cikin boot din mota suka jefani sosai nasha azaba kamar zan rasa rayuwata Kafin bansan Inda suka tsaya ba saigani nayi sun fiddo ni sun jefani cikin daji suna saita ni da bindiga daga lokacin bankara sanin abunda ke faruwa ba duk halin da na shiga na shige shi ne sanadiyar d'an uwa ya kashe mun mata a kan ido na yaso hallaka rayuwata inbanda Allah yasa ina da sauran kwana a gaba "ya k'arasa fad'a cikin hawaye " Kowa dake palourn saida ya girgiza dajin wannan labarin wai Dan uwanka ne yayi maka haka musamman zahra da yau ta had'u da kakanta sannan taji Tarihin mahaifiyarta sosai su Ammy da MD suka jajintawa Baba sannan sukayi Allah wadarai da wannan D'an uwan nasa ranar Baba jinshi yayi cikin wani irin farinciki ganin jinin y'artasa harda jikokinta md ko yasha alwashin saiya kwatowa baba hakkinshi a wajen Dan uwanshi duk inda yake bayan komai ya lafa Baba ta kalli ammy ya ce "Hajiya naji kince Zahra ce maman yaran Nan ko kina nufin ki cemun matar jikana ce "Murmushi dauke da fuskar ammy ta ce "Eh baba matarsa ce Allah ya kawoka a daidai lokacin da muke da bukatarka Kallonsu Zahra tayi har md ta ce "ku bamu waje zamuyi magana"A tare suka tashi Zahra jinta take cikin farinciki marar musaltuwa bayan ammy tayiwa baba tsoho bayanin yanda asalin aurensu Zahra ya kasance saidai ta boye musu na dalilin auren akan matarsa saboda batason Zahra ko danginta suji abunnan abun kunyarta ne Sosai baba yayi mamakin al'amarin ta wani bangaren Kuma yaji Dadi Sosai da ammy ta fada Masa yanzu md yanason Zahra Sosai itace dai take tunanin ko Bata sonshi bazata amince da koma Masa ba sannan batasan ta yanda zasu tunkari iyayenta ba sun tattauna Sosai tsakanin Ammy da Baba har Kaka kafin su tsaida magana akan jibi idan Allah ya kaisu za a tafi garinsu baba ayi masu bayani sannan a Basu hakuri haka ko akayi ranar suka shirya gabaki dayansu Ammy,kakan Zahra,Chuchu,Zahra,da triple dinta sai Hajiya Kaka ,md ne kadai ba a je dashi ba bayan isarsu batsari Kai tsaye gidan bappa suka wuce Wanda Zahra itace ta gwada musu hanya Banda faduwa babu abundan gabanta yake Sosai Aka karramasu Dukda zarha Bata yarda ta had a Ido da kowaba gabanta kawai ke faduwa A sace take Kallon baba da Shima tunda ya shigo ita yake kallo fuskarshi ba alamar walwala ganin da Zahra a tafiyar bappa yasan maganace Mai mahimmanci hakan yasa ya Kira Yan uwa baba su mama habi kowa duk ya hallara a dakin bayan an gaggaisa cikin mutunci Nan ammy tayi musu bayanin komai game da auren Zahra da sukayi da d'anta a boye har ciki ya Samu har zuwa haihuwarta suma dai Bata fada musu dalilin auren na md ba ta ce dai shirme ne irin na Yara sannan ta Kara kafa musu hujja da nuna musu video din daurin Auren sunyi mamaki matuka da gaske Jin wanna chakwakiyar su mama habi kuwa ajiyar zuciya suka sauke dukda sunji zafin aurar da kanta da Zahra tayi Amma Kuma sunji Dadi da diyan suka kasance y'an halak baba ko cikin bacin Rai ya ce"Kin bani mamaki Zahra ina tarbiyarki,ina iliminki,har ki aurar da kanki ba tare da izinin iyayenki ba kenanma bani da wani amfani a wajenki Dan haka. Ki tashi kibani guri tunda bani da wata daraja a wajenki har Kika iya aurar da kanki ba izininmu ki tashi ki tafi bana bukatar ganinki"Baba ya fada cike da takaici,"Kuka sosai Zahra ta fashe dashi ta ce "Dan Allah Baba kayi hakuri ka yafemun.."Saikuma ta Kara fashewa da wani sabon kukan sosai baba ya nuna bacin ransa matuka.inda su ammy dasu baba har Hajiya Kaka hakuri kawai suke bashi kowa yayi mamakin irin yanda baba ya nuna bacin ranshi kasancewarsa mutum.mai hakuri dakyal da jibin goshi aka samu aka shawo kan baba Amma Kuma saiya gindaya sharadi akan Zahra bazata koma ba zata zauna a wajenshi har lokacin da zata yaye yaran ta mayar musu da Su "Nanfa hankali ya Kara tashi musamman na ammy da Chuchu "Hakuri ammy ta dinga bashi ta ce "Dan Allah malam kayi hakuri munsan mu masu laifi ne a gareka Amma ka sassauta a dauki abunnan matsayin kaddara Dan Allah malam kuyi hakuri a sasinta wlh yaron yayi matukar nadama kuma.yanzu haka Yana son Zahra Yana son idan kun amince ta koma a matsayin matarsa tahar abada Dan Allah malam kuyi hakuri kodan arzikin yaran Nan har ukku dake tsakaninsu"Ammy ta fada hankali tashe "Nanfa baba yace baisan wanna zancen ba Indai Zai yafawa Zahra abunda tayi mashi to zata zauna ne a wajenshi sannan ya Aiko mata takardarta tunda ba aure ne akayi na mutunci ba idan ba haka ba ta tashi ta bisu ya bar musu ita har abada"Sosai hankalinsu ya Kara tashi Banda Zahra ta taji sassauci gwara ta zauna a Nan din kawai "Baba tsoho ne ya saka Baki yacewa "Ammy 'kiyi hakuri Hajiya a barmata sudin Yana cikin fushi ne a Bari su huce kawai"Badan Ammy taso ba dole ta amince musu chuchu ko hada kukan Dan batason tayi kewar Zahra daidai da second yanda takejin zey a ranta haka takejin Zahra tamkar ciki daya suka fito Nan Hajiya Kaka ta gabatar musu da Baba matsayin kakan Zahra Sosai kowa yayi al'ajabi dajin wanna al'amarin baba ko yayi farinciki matuka na ganin mahaifin tsohuwar matar tasa Kuma kakan y'arsa Sosai yaji dadin bayyanuwar ahalin na Zahra dukda sunyi al'ajabi dajin wannan labarin na baba Mai rikitarwa Bayan sunci abinci an karramasu Wajen la'asr suka fito domin tafiya an cika musu ledoji da kindirmo Sosai Ammy da chuchu sukayi sanyi na barin Zahra mama habi da matar bappa suka rike triple chuchu ko ta garkame little Sosai sai kuka take ganin haka ya Sanya Zahra kasa da kanta Tana hawaye sai yanzu takejin kewar su da zatayo ga Kuma baba tsoho da ko sabawa basuyiba Shima tare zasu koma har mota suka rakosu Wanda chuchu dakyal ta Mika little ta ruga da gudu mota Tana kuka Ammy ko dauriya kawai tayi Tana rike da hannun Zahra ta ce "To takwara mun wuce saimun dawo ganinku"Zahra batasan lokacin da ta fashe da kuka jikin Ammy ba duk kallonta suke Sosai ta dinga kuka Ammy da itama zuciyarta ta kusa karyewa dakyal ta lallasheta ta shige mota da gudu Zahra ta koma ciki Tana kuka girgiza Kai kawai baba tsoho yayi Bayan sun Kara bankwana suka wuce cike da kewa da jimamin barin Zahra chuchu ko har suka Isa gida Tana kuka Dan ba Zahra kadai zatayi kuka ba hada triple da tayi muguwar shakuwa dasu kwana tare tashi tare kullum suna hannunta Ammy ma hakan ta kasance baba tsoho ko Shi kadai yake sake sake a ransa bazaiso abunda mahaifin Zahra ya fada ya faru ba watau na rabuwar Zahra da md yasan muddin Zahra ta rasa yaron Nan to fa tayi babban Rashin miji na gari Dan Shi kanshi yasan yaron mutumin kirki ne tashin hankalin da md ya shiga Najin labarin baro Zahra da da yaran baya musaltuwa Sosai ya burkucewa Ammy kamar Zai musu hauka su kansu mamakinshi suka dingayi yanda yake magana kasan Yana cikin tashin hankali ya ce "Ammy me yasa zaku baromun mata meyasa Ammy na fada maki ina son matata meyasa Zaki maida ita Gashinan kin lalata komai Ammy Ana neman rabani da matata wallahi bazan saketa ba kome zakuyi kuyi haba Ammy saikace Ba d'anki ba kinsan Sarai ina cikin tashin hankali shine saida kikayi yanda kikayi Kika rabani da mamy na Baki hakuri ba iyaka Ammy nayi regrade duk abunda nayi Ammy Amma kikaki hakura saida Kika rabani da matata why Ammy me nayi maki"Ya fada kamar Zai fashe da kuka"Ba Ammy ba hattababa tsoho saida ya tausaya Masa "Cikin kwantar da murya Ammy ta ce "Babu Wanda yafini sonka da Zahra babana nafi kowa kaunarka da Zahra saboda bazanso rabuwarka da itaba duk abunda nayi make nayine saboda tayi daraja da martaba wajenka ka gane amfaninta Amma bawai Dan karabu da ita ba ni zanfi kowa shiga bakin ciki ace ka rabu da Zahra In son Zahra tamkar yanda nakeson su chuchu "To Ammy meyasa Zaki Baro musu ita meyasa Zaki kaita wajensu Ammy yanzu kina gani sun amshe mun mata Ammy duk laifinki ne meyasa tun farko Baki sasintani da matata ta ba Kika dinga jamun Rai ni mamy tun ranar Dana fara haduwa da ita nasan darajarta da mahimmanci ta da amfaninta a cikin rayuwata.."Kasa karasa magana yayi saboda wani daci dayakeji a cikin zuciyarsa "Ammy ce ta ce "ka nutsu baba na dole ne a kaita Wajen iyayenta ayi musu bayani Susan halin da ake ciki saboda su sukafi kowa hakki a kanta kaga ko Baba da kagani shiya haifi mahaifiyarta to baikai dangin mahaifinta da mahaifinta hakki a kanta ba kayi hakuri harsu huce " bai tankawa Ammy ba saboda baima San abunda zaice mata ba Kuma, fuuuu yabar dakin kamar Zai tashi sama cikin tsananin bacin Rai "Chuchu ma Tana kuka ta Mike ta ce "Daman Ammy duk laifinki ne tun lokacin da yace yanason momcy kikakiya yanzu Gashinan kinja iyayenta sun amshe Mana ita"ta fada Tana tashi da gudu ta Ruga"Tagumi Ammy tayi ta ce "Oh ni !Fatima yanzu Kuma laifin Nan duka sun maidoshi kaina.........✍️