← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 129

Sashe 66

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

in zakiyi mu'amula da maza dubu ba damuwa ta bace ina kiyaye miki ne fushin ubangiji"Yana gama fad'ar haka yayi parking tare da ficewarsa saboda sun Iso gida Zarah ko sosai jikinta yayi sanyi koda ta shiga cikin gidan harya shige bedroom dinsa tagumi tayi maganganun da yayi mata suna mata yawo a kwalwa ta jima kafin ta mik'e ta shiga tayi sallar la'asr da taji ankira a hanya Bayan ta gama sallah Qur'an ta d'auka tana cigaba da karantawa yunwar da tajine ta tuna mata da bataci abinci da rana ba yaye hijab d'inta tayi Kallon jikinta taayi taga doguwar rigar bata lafe ta ba Sosai taji dad'in ganin baya palourn Kitchen ta shiga ta girka Abu mai sauki sosai taci abincin Wanda har mamakin kanta tayi tasan dai bata da ci da Chan ma bare yanzu Bayan ta gama tayi hamdala kujera ta mik'e batasani ba har bacci ya d'auketa fitowa yayi daga Bedrom d'in sosai yayi mamakin ganinta tana baccin la'ar Wanda bai tab'a ganin haka a Wajenta ba Zaunawa yayi karewa sleeping face d'inta kallo yayi Yajima.yana kallonta wayarsa da tayi ringing ta dawo dashi daga duniyar tunanin d'aya Lula dubawa yayi yaga ,"My Merah"a jiki saida ta gama ringing kafin ya kirata sosai suka sha Hira irin ta mata da miji Wanda yawaici duk Amira ce mai surutun danshi ba ma'abucin son surutu bane har suka gama wayar bacci Zarah take Gashi yana son tashinta amma bayason katse mata baccin dayaje zai tab'ata saiya fasa sai Chan wajen 6 yaji farkawarta Bayan ta wartsake kallo d'aya tayi masa ta kauda kai tare da mik'ewa ta shiga d'akin cikin har isha'i bata fito ba Dan Sallama a Chan tayi tana gama salla ta kwanta bacci ya d'auketa Chan cikin dare taji MD nayi mata abunda ya saba kin biyesa tayi Dan kwana biyun nan abun ba dadi yake mata ba shi kad'ai yayi kidansa da tsalle Shi kanshi MD yayi mamakin yanda bata bashi attention ba ga kuma jin wani dadi da take karawa kwanakin nan haka rayuwa taci gaba Rabi a hostel rabi kuma a gidan MD Dan MD yanzu ya mayar da Zaria gida idan ka ganshi a kd tofa ziyara ce yakai musu A haka dai har wata guda Wanda yanzu wata Guda ya rage karewar yarjejeniyarsu A halin yanzu kallo d'aya zakayiwa Zarah kaga ta sauya saboda wani fresh da kyau da ta k'ara ta k'ara murjewa ga komai nata yayi b'ulb'ul saikuma bacci da take yawan yi Wanda ita kanta har mamakin wannan masifar baccin data sameta yauma tana kwance a gadonsu na hostel Tana bacci Chuchu ma tana gadonta tana karatu a Littafi kasancewar final exams dinsu dake tunkarowa duk sun maida hankalinsu ga karatun da suke Bayan dawowar Asmy daga Lectures Kallon Chuchu tayi ta ce "Badai Zarah yauma bataje lectures ba" Wlhko kinganta nan tun shigowarta da safe tana shiga lectures safe ta fito tun 10 take wannan bacci duba kiga yanzu har 2:15 na tashetama tayi sallah taki tashi sai rabuwa nayi da ita"Karasawa gadon Asmy tayi ta ce "Na rasa dalilin baccin nan da ta tarka na uban meye " ta fad'a tana bubbugar Zarah da karfi dak'yal ta samu ta tashi tana hade fuska Asmy ta ce "Ke yanxu Zarah Dan iskanci saida kikaga karatunmu yaxo karshe zakisa shiririta ki tarki wani bacci Ki dinga kin attending lectures to wlh bazan yarda da haka ba "Sorry uwata nadaina" Zarah ta fad'a tana Mikewa tare da Yin y'ar mik'a tayi hanyar toilet Dan ta dauro alwala "Chuchu ce tadanyi murmushi ta ce " Ai dole tace maki Mama kam yanda kike bada command irin y'ar nan taki"wlh ba haka bane abun ne ya fara bani Haushi bacci bacci saikace kasa"Wlh ko nima abun har mamaki yakeban kamar wacce tse_tse fly ya cixa kokuma wata me ciki ta zauna tayi ta bacci ba control" Gaban Asmy ne ya bada daram jin Abunda Chuchu tace Dan bata tab'a sanin bacci Alamun ciki bane Zarah ma dake fitowa daga toilet saida gabanta ya fad'i saikuma taja tsaki a ranta ga ce "Ni mema zai had'ani da wani ciki Allah na tuba wata takwas bansamu ba sai yanxu" Ta k'arasa shigowa "Daidai lokacin da Asmy ke cewa Chuchu " Ke waya fad'a maki mai ciki tana yawan bacci nidai ban tab'a jiba"Nima a novels karanta wlh "ta fad'a tana y'ar Dariya " Tsaki Asmy taja tace keda kike karanta novels dinma har kika sani"Murmushi Chuchu tayi ta ce "Hmm ai wlh ina mamakinku da kikace wai baku karatun novels ai novels duniya ne musamman kika hadu da mai dadi duk wata damuwarki jinta zakiyi ta yaye novels yana yaye damuwa yanda baki tunani wlh Ga dadi jinki kike kamar kiyi tsuntsuwa ki koma duniyarsu" Dariya Asmy tayi ta ce "Haka dai kike cewa nikam gani nake bazan iya zaunawa na karanta ba gani nake bata lokaci ne kema Rashin aikinyi ne kawai" hmmmm bazaki gane bane Matar nan"To Ganar dani "Dariya chuchu tayi ta ce '" Ai tunda kince bazaki iya ba shikenan"a a yanzu dai Naji bani wani na karanta Page d'aya Naji yanda abun yake"okay bari na dubo maki *Ni da yaya Arman* da na karanta kwanaki tun lokacin da ake typing dinsa na saya littafin yayi dadi over yanda baki tunani anzuba zallar Soyayya a cikin book dinnan an zuba basira kede bari ki karanta saikin bani labari "okay ban page d'aya Na gani" Wayarta Chuchu ta bud'e ta shiga tare da mik'a mata "karanta Page d'aya ma kadai ki bani labari "Ansar wayar Asmy tayi ta fara karantawa Zarah dai na jinsu har ta gama salla girgiza kai tayi ta ce "Ana shirin exams kina shirin koya mata karatun Littafi" Dariya Chuchu tayi ta ce "Page d'aya ne fa zata karanta momcy kema ko zaki karanta" Girgiza.kai tayi ta ce "Bani da time d'in wannan Exams na gabatomu ina ni ina fara karatun Littafi " Asmy ita da zata karanta Page d'aya ai batasan ta zarce har page biyar ba saida Chuchu ta warce wayarta ta ce " Yadai naga kinjima bani wayata chat zanyi"Cikin doki asmy tace "wayyo ya zaki lasamun Zuma a baki kuma ki barni Dan Allah ki bani naci gaba please banso ko da second d'aya a wuceni" Dariya Chuchu ta kwashe da ita ta ce "Keda kikace bani da aikinyi ai bazaki cigaba page daya nace ki karanta" ai bansan haka abun yake ba shiyasa nace haka wlh book din tundaga fara karanta Page d'aya ya tafi da imani na tundaga farkon salon soyayyarsu ya burgeni ba k'aramar love za a zuba a book d'innan ba da na lura Dan Allah ki bani na ida please "Dariya Chuchu tayi tace bari dai na tura maki ba Dan halinki ba Ai baki fara komai chakwakiyar love sai nan gaba Ayra da Arman Ai duniya ne Bari dai karna baki labari ki karanta da kanki" Zarah ce ta ce "Ikon Allah to ga wayata nima turamun Idan mungama exams na samu na karanta"Duka ba haka za ayi ba ku bari zansaya muku complete document a wajen marubuciyar saina tura muku ta what's app wannan doc din free page ne kuma.lokacin da na karanta a paid grp dintane Kunga ba Tarawa zanyi ba " Cikin doki asmy ta ce "Nidai fara turamun wannan din Kafin taturo cmplt din wlh marubuciyar ta iya salon labari mai d'aukar hankali" Dariya Chuchu tayi ta ce "Kaji uwar azarzabi ki bari na saya muku mana " A a aban yarda ba please ni bani number marubuciyar ya sunanta na maza na saya kar a barni a baya"Dariya Chuchu ta dake ta ce "aifa inaga haka din zanyi chan ku karata rubuta mata number tayi ta ce " Kiyi save da Hajara L Sadeq ko miss hajo"girgiza kai Zarah tayi ta ce "Kinji uwar ujila nima bani numberta sanda Nasamu time naso karantawa saina tuntubeta" Itama Rubuta mata number tayi ta ce "Na tura miki free page din ta what's app" Okay Thnks daughter "Zarah ta fad'a sai yamma driver yazo daukarta suka wuce Gidan MD tana lissafin sauran lokacin da ya rage mata ya saketa kowa ya kama gabansa sosai ta maida hankalinta ga karatun ta dukda yawan baccin da take bai hanata raba dare tana karatu dukda MD baya barinta sakewa a dare saboda koda yaushe yana nanike ita itako ta rabu dashi ne kawai Dan tasan na bankwana ne yake nan da one months kowa ya kama gabansa da idonsa ma bazai ganta ba tsaye take tana soya awarar kwai a kitchen tunda taji karnin kwan taji zuciyarta na tashi Tun tana daurewa harta kasa da gudu ta fito tare da rugawa palour ta fad'a toilet a guje nan ta fara kwarara amai MD yana palour yana mamakin me ya sameta bai tashi ba ya bita haryaga Fitowarta tana maida numfashi " Sannu"ya furta a hankali ta gyad'a masa kai tare da bajewa kan kujera tana ci gaba da maida numfashi "Baki da lafiya ne" ya k'ara maimaitawa "Girgiza kai tayi tare da yatsine fuska ta ce.........✍🏿
Chapter 66 · 0% Book details