← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 129

Sashe 2

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kamar yanda ta saba koda yaushe tun asuba da ta tashi tayi sallah bata koma ba nan taci gaba da aikace aikacen gidan Har Safiya tayi wajen 8 da rabi taga su Habiba sun fito Suna hamma tare da d'aukar buta Zasuyi Alwala girgiza kai tayi wai ace Sai yanzu zasuyi sallah Kodan yau sunma tashi da wuri su da har 9 kaiwa suke batace komai saboda bata manta ba ranar da ta tab'a musu magana akan Sallar Safe da suke irin tijarar da suka mata hakan ya sanyata cigaba da Harkokinta Tana cikin d'ora d'umame Khairat ta lek'o Yarinya ce da bazata wuce shekaru goma sha daya ba kallonta tayi tare da cewa " Ina kwana Aunty "Murmushi Zarah ta sakarma kanwartata dan duk cikin gidan itace Ta fita zakka ta ce "

Lafiya qalau khairat Kintashi lfy "Alhmdllh ta fad'a ta na Amsar tukunyar da Take shirin dorawa ta ce " bari na tayaki Aunty"A a a ki barshi khairat zanyi "Amsa tayi ta ce " Nidai saina tayaki Suna cikinyi Mama Rabi ta lek'o Dan Safiya ta gulmanta mata Khairat na kitchen tana taya Zarah Aiki wata uwar ashar ta kawo ta lafta wadda saida cikin Zarah ya d'uri ruwa tuni ta dabarbarce "Kafin da d'ago Mama Rabi ta kife ta da Mari tare da cewa " Dan Ubanki y'artawa zaki sanya Aiki tayi maki kama da kalar Aiki Sau nawa zan fad'a maki Ke kadai zaki dinga aikin gidan nan Eyye tsabar iskanci ma y'arda na Haifa itace zatayi maki aiki"Khairat ce ta mik'e cike da tausayin y'ar uwar tata ta ce "Kiyi hakuri Mama Ba ita ta sanyaniba ni naga ya kamata na tayata"

Tsawa ta daka mata Tare da nuna mata hanyar waje ta ce "Fice ki ban waje kafin na waiwayo kanki" Cikin Sauri ta fita ta bar kitchen d'in ta na gunguni"Zarah ko hawaye ne suka zubo mata Inda Mama Rabi ta shiga balbaleta da masifa Inda ta shiga ba ta nan take fita ba amma bata Ce mata uffan ba harta gama fadanta ta fita girgiza kai tayi tare da mik'ewa taci gaba da abunda ta ke ta na yi ta na hawaye "Bayan ta gama aikin D'akinta ta shiga ta share tare da daura towel ta dauki sosonta da sabulu ta fito Ta shiga wanka Bayan ta fito Nan ta iske Mama Rabi da d'iyan ta suna cin d'umamen Tuwon da ta dafa" bata bi ta kansu ba ta shige d'akinta Tare da Shiryawa cikin Wata Atamfarta da ta d'ansha jiki jin kukan yunwar da cikinta keyi ne ya sanyata mik'ewa tare da fitowa nesa da su ta tsaya tare da K'asa da kanta "Tayi shiru "

Cikin masifa Rabi ta ce "kikazo kikayi mana tsaitsaye Mayya me za a baki" Dagowa tayi idanunta na zubar da k'walla tayi maza ta Goge ta ce "Daman abinci nazo d'auka " Dogon tsaki taja tare da Banka mata harara ta ce "Mun cinye mu Kanmu bai ishemu ba " Khairat ce dukda yarintarta ta ce "Mama ni bari na bata nawa na k'oshi" Harara ta banka mata tare da dankwashinta aka ta ce "inke kin koshi ni ban koshi ba " girgiza kai kawai Zarah tayi ga abinci nan tana gani Bayan ita ta sha wahalar girkawa amma a hanata ga tsabar yunwa da takeji Juyawa tayi ta koma d'akinta tare da dauko d'ari biyun da Baba ya bata ta boye a jikinta hijab ta sanyo tare da Fitowa Tsawa Mama Rabi ta daka mata ta ce "Gidan ubanwa kuma zaki"

“Fita zanjena nemi abinda zanci "ta fad'a cikin rawar murya" koma ciki babu Inda zaki Dan Ubanki so ne kike ki k'ara jamun Zagi a wajen mutane duk abunda nake ba gani ake ba To ba Inda zaki"Amma Mama Ke fa kika hanani Abinci kuma zanje na saya ki hanani fita"ta fad'a cikin dauriya"eh bazaki ba ko fad'a zanyi ki mayar mun?

Girgiza kai kawai tayi tana Jinjina Rashin imani irin na Mama Rabi daki ta Koma tare da zaunawa ta rafka ubann Tagumi Hawayen tausayin kanta na zubo mata yaci a ce Inda sabo ta saba da halin da take ciki......✍🏿

*muje zuwa fans salon na daban ne Kudai kawai Kuci gaba da bibiyar gawurtaccen labarin da yazo cikin gawurtattu*

*ta hanyar comment da sharhi ne kad'ai zai tabbatarmun da labarin ya amshi wajenku ko akasin haka idan kun karanta ku daure Kuyi comment tare da sharing sauran grps masoyan Asali wannan itace babbar kwarin gwuiwar da makaranci ke bawa marubuci*

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Taku har kullum d'ince dai
👇🏿

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

💑 *AUREN WATA TARA* 👨‍❤️‍👨

MALLAKAR

*Hajara L Sadeq*

*FREE PAGE*

🅿️..........*3 & 4*

Tana nan zaune tana jin yunwa har Ukku da rabi tayi cikin Sauri ta mik'e tare da sanya Hijab d'inta Dan daman Allah Allah take lokacin Islamiya yayi turaranta Wanda baiwuce Naira d'ari Ukku ba ta fiddo ta fesa Dan Ita daman Chan ma abuciyar son kamshi ce .

Fitowa tayi ganin ba kowa tsakar gidan Tare da barin gidan Gidansu Asmy ta shiga gaishe da mamansu tayi har k'asa ta amsa mata cikin girmamawa Babansu ne ya fito Shima gaishesa tayi ya amsa mata cikin sakin fuska Asmy ce ta fito daga palour tare da kallonta ta ce.

"Ki shigo yau kece da Shiryawa da wuri Ko y'ar jarabar bata nan " Dariya Kad'an Zarah tayi tare da girgiza kai ta ce "Kiyi Sauri dai yanzu " Kama hannunta tayi suka shiga cikin palourn su mai d'auke da kujeru matsakaita masu kyau sai madaidaiciyar plasma d'insu dake manne a d'akin Suna Kallon tashar arewa24 .

ganin ana maimaicin dad'in kowa ya sanya Zarah maida hankalinta ga kallon da ake Asmy tunda ta shigo ta lura da Idanun Zarah yanda suka fad'a tasan bataci abinci ba gashi tasan ko mutuwa zatayi bazata tab'a cewar bataci ba

Shinkafa da miya taje ta zubo dukda taci abinci Tazo ta Aje gabanta tare da kallonta ta ce "Sauko muci abinci my Besty" na k'oshi Kedai kawai kici mutafi?Harararta tayi ta ce "Aiko kice yau ba zuwa Islamiya Dan Allah sai kinci abincin nan idan ba haka ba Muyi ta zama a haka" Saukowa Tayi Dan tasan kawar tata ta aika Ta ce.

"Uwar y'an jaraba to muyi Sauri" Sai sannan Asmy ta saki fuska ta ce "kokefa my Besty wai kinsan Waec d'inmu ta fito Kuma alhmdllh Duka na cinye yanzu jiran neco kawai muke tunda ita kikayi "

Cikin farinciki Zarah ta ce "Wow alhmdllh sis a Gaskiya na tayaki murna wlh Allah sanya alkhairi kice itama neco tana gab da fitowa muyi ta addu'a"

" Wlhko Besty Kinga murnar da nake "Har suka gama cin abincin suna Hira Inda Bayan sun gama sukayi sallah tare da wucewa Islamiya Dan duk shirye shiryen saukar da zasuyi ne nan da sati biyu ake.

Sai wajen magriba suka bar makarantar Inda daga nan kowa yayi gidansu Tun a Soron gidansu Zarah ta farajin muryar Salisu gabanta na fad'uwa Ji take kamar ta juya Dan tana tsoron mashayin Chan.

dak'yal tayi shahada ta shiga tun daga shigarta Salisu dake kan turmi yana busar sigari ya kafeta da idanu har wani lashe harshe yake Itako hade fuska tayi Tam Cikin muryar y'an maye ya ce "Daman tun d'azu nake jiran dawowarki Amaryata "

dogon tsuka Zarah taja tare da Yin hanyar d'akinta janyo mata hijab yayi Wanda hakan ya k'ular da Zarah batasan lokacin da ta juyoba tare da wankeshi da Mari Salisu da saijin saukar Mari yayi a fuskarsa dafe kumcinshi yayi tare da nunata da yatsa ya ce.

"Ni kika Mara Aiko yau zakisan kin tab'a cikakken d'an tasha Dan uwarki Dan kin samu ma ana sonki Aiko daga yau bazaki k'ara gigin Marin wani ba ya fad'a yana zare belt d'in jikin wandonshi tuni cikin Zarah ya Dori ruwa Dan ba abunda ta tsana irin a tab'a lafiyarta Cikin Sauri Ta maza ta Ruga d'akinta Tare da sanya sakata ta rufe sai huci take.

" Salisu ko tsaye yayi ya na ta banka k'ofar ya ke kamar zai b'allata "Rabi ko shiru tayi Dan abunda yasa bata tanka ba Baba na bandaki tun daga Shigowar Salisu Kasancewar Tattare suka shigo da Zara da ido take masa nuni akan ya bari amma sai dura ashar yake ya na cewa yau sai ya raba Zarah gida biyu .

Baba ne ya fito daga bandaki cikin b'acin rai irin nasu na masu hakuri ya dakawa Salisu tsawa " Juyowa yayi Dan duk iskancinshi yana shakkar Malam saboda mutum ne mai kwarjini Sosai Malam ya shiga F'ada ta Inda ya shiga ba ta nan yake fita ba sulalewa Salisu yayi ya bar gidan Inda ya koma kan Rabi ya ce.
Chapter 2 · 0% Book details