← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 129

Sashe 80

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

a matsayin kaddara da kuma wauta da k'uruciya sosai ita kanta take Danasanin sake ma mugun mutumin nan jiki da tayi Wanda a yanzu ba Wanda ta tsana takejin Haushi sama dashi koda suka isa gidansu Sosai ta iske y'an uwan babanta Na Batsari da Wanda suke Aure a wasu garuruwan duk sunzo kasancewar Baban Zarah yana da yayyu da kanne maza da mata sosai Cikin ladabi da jin kunya Zarah ta gaishe su a sanyaye "Mama Habi ta kamota ta ce " me yake damunki Zarah jibi yanda kika zama kallo d'aya nayi maki nasan bakya cikin kwanciyar hankali me yake damunki?Murmushi Zarah ta kirkira ta ce "Bakomai Mama " Hmmm kodai har yanzu Muguwar Matar nan tana musguna miki "Girgiza kai Zarah tayi ta ce Bakomai Mama " Hmmm ai duk mai hankali yasan ba cikin kwanciyar hankali kike ba Zarah tun farko laifin malam ne tun Bayan mutuwar mahaifiyar Yarinyar nan babu yanda banyi da shi ba akan ya bani ita na tafi da ita katsina mijina ba k'i ba zaiyi amma yak'i ya nuna shi yakeson ya Riki y'arsa baya son zamanta wajen kowa hakan yasa muka hakura muna sane da duk gallazawar da akewa yarinyar nan kawai in banda kar kayi magana ne ace ka fiya fad'a Shikenan yanzu dai komai yazo karshe tunda har Allah ya kawo lokaci zakiyi Aurenki ki huta yanzu fad'amun abubuwan da kike so "k'asa tayi da kanta muryarta na y'ar kakkarwa ta ce " bakomai Mama"ke d'ago ki kalleni nidin kamar uwa nake wajenki karkiji kunya ki fad'amun abunda kike so da choice d'inki na kayan d'akin"kamar zatayi kuka ta ce "Bakomai Mama" Ikon Allah to tashi kije"kamar jira take ta mik'e ta shiga D'akin wasu daga cikin y'an uwa sukayi Dariya sukace "Zarah kenan itadai ba ruwanta har yanzu kunya ce fa takeji" Mama Rabi ko tana d'aki ta cika tayi Fam jin Abunda Mama habi take cewa Daman Chan tasan ba wani jituwa suke ba Habiba ce dake gefe ta ce "Ni Mama wlh mamaki kike ban Wai me kike nufi da barin ayi Auren nan da zakiyi nidai wlh harga Allah ina bak'inciki da Hafiz d'innan da Zarah zata Aure Dan Babban gida ne babansa yana d'aya daga cikin manyan masu kud'in garin nan haba Mama taya za ayi yarinyar da Mukasan yarintarta da komai muka bata shekaru nesa ba kusa ba ace wai tazo ta rigamu Aure muna nan zaune ko gaisuwa babu Wanda yataba zuwa sannan kuma ace tayi Aure Inda zata huta haba Haba Mama ina tuno wannan bakin cikin ji nake kamar na hadiyi Zuciya" da hannu Mama Rabi tayi mata nuni tayi kasa kasa cikin k'asa da murya ta ce "A tunaninki haka zan zuba ido ayi Auren nan ina nan ina ganinku wacce ta tsonemun ido ta rigaku Aure Aurenma kuma gidan Hutu ai abunda bazaiyu bane kusa ido Kuyi kallo wasa na gaba Dole zan saki jiki ayi komai dani saboda idan Abu ya lalace kar a zarge ni kina gani dangin Malam ba wani kaunata suke ba so suke ayi tashin hankali Wanda ni ban shiryawa haka ba ... Zarah ko tana shiga daki ta zunduma duniyar tunani gani take abun kamar mafarki Bikinta da Hafiz Wanda inbanda wannan K'addarar ta afka da ba Wanda zai kaita farinciki amma Kuma yanzu Shine take fargabar Auren to wai yanzu haka zata zuba ido A daura mata Aure kan Aure batasan sanda wasu hawaye masu d'umi suka shiga zubo mata ba Cikin muryar kuka ta ce " Ya Allah ka kawomun mafita a cikin al'amarin nan kafi kowa sanin halin da nake ciki Kaine mai iko akan komai babu abunda ya gagari ikonka ya Allah Kakawo mafita ta yanda ban tsammaceta ba Allah na tuba Ka yafemun Ka cireni cikin kangin rayuwar nan nasan wannan din duk yana cikin jarabawa ta ne ya Allah ka sassautamun jarabowowin nan da suke bibiyata tun yarinta ka kuma bani ikon cinye su kuka ne yaci karfinta Sosai tashiga rera kuka Daren ranar Zarah raba dare tayi tana addu'ar Allah ya kawo mata mafita a cikin rayuwarta..... a halin yanzu y'an uwa da dangi na nesa da na kusa duk sunzo domin ayi kome dasu Maman Asmy ma sosai take taka muhimmiyar rawa a bikin nan da za ayi dangin Baban Zarah sai Godiya suke mata na jajircewa da tayi tamkar bikin y'arta za ayi Dan wani irin tsumi takeyiwa Zarah dukda kwana biyun nan ba lafiya gareta ba yauma da Hafiz yazo da dare dak'yal ta samu ta fita cike da damuwa ya ce "Wai Dan Allah me yake damunki ne my Zarah bana gane maki kwannanfa" Kasa tayi da kanta tana maida hawayen da suka zubo mata Dan karya gani kasancewar duhu ne cikin rawar murya ta ce "Bakomai kawai banajin dadi ne" subhanalla ankaiki asibitine"eh Maleria ce" ta basa amsa Dan karya ce saitaje asibiti Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Allah ya baki lfy please kidinga shan magani sosai yanda zaki warke da wuri saida biki ya matso Maleria zatayi mana cikas " Shiru tayi batace komai ba "Kamo hannunta yayi abunda bai tab'ayi ba cikin firgici ta d'ago ta Kallesa Duka hannun nata biyu ya rik'e yana kallonsu tare da murzawa cikin Sauri tayi saurin kwace hannunta ta kauda kai tana hade rai" Sai sannan Hafiz ya dawo cikin hayyacinshi ganin yanda ta had'e rai dukda duhu ne ya ce "Sorry" a sanyaye ta ce "Dare nayi" Okay Good Night dinkunan nan dai sunyi kyau ko?Gyada masa kai tayi dukda ko kallon d'inkin batayi ba saboda yanzu bata wannan take ba "Ajiyar zuciya ya sauke ya ce " Duk abunda kuke da buk'ata keda kawayenku kuyimun waya "Insha Allah " ta fada a sanyaye Bayan sunyi bankwana ta koma gida Nanma saida ta kafa sana'ar tata ta kuka tana jin bata kyautawa Hafiz ba a halin yanzu Zarah bata da wata mafita data wuce Ta Allah Shi kawai take jira yayi ikonsa akan Abun tasan ko giyar wake Tasha bata isa ta tunkari wani da wannan Maganar bare yanzu da biki ya rage saura kwana shida.... "Ammy ba haka bane kiyi hakuri Dan Allah"ya fad'a cikin ladabi"Bani ya kamata kaba hakuri ba Matarka da kayiwa laifi ita ya kamata kaba hakuri"laifi kuma Ammy to me nayi mata "Ohh tambaya ta ma kake me kayi mata Bayan banzatar da ita da kayi Tunda akace tana da ciki baka Kuma waiwayarta ba " Ba haka bane Ammy kumin uzuri please yanzu ina amerar take "Ta tafi Gidansu kasan halinta ba sake mana take ba washegari ta shirya ta ce " zata wuce gidansu Ta kwana biyu ta warke a chan'?"Niko ban hana ta ba nace Allah ya kiyaye nasan duk haushin abunda kayi mata ne yasa ta tafi"Zankirata Ammy ina Hajiya wai tunda na shigo ban ganta ba "Dazu ta fita Ta lek'a gidan Zainab ne " Okay Chuchu fa "bai rufe baki ba yaga shigowarta palourn hannunta rike da waya kai tsaye wajenshi ta nufa fuskar ta cike da fara'a ta ce " Lah yaya yaushe kazo ina yini"Alhmdllh Auta ya gidan"Lafiya qalau ta fad'a tana zaunawa gefenshi tare da cewa "Yaya kazo a Daidai tun safe na rasa shawarar Wanda zan nema bikin momcy ne ya taso za ayi Saturday d'innan ina son ne na tafi wednesday tun gobe ma naso na tafi wlh ammy ta hana wai sai wednesday to shine zanyi mata gudummawar jaka nakirata akan taturo mun hotonta na biki tace batayi ba gashi nafison nayi mata mai hoto to shine nake gani ko hoton waya zaiyi akwai hoton Dana tab'a mata a hostel kuma yayi clear sosai bari ka gani kaga idan zaiyi ayi dashi ko kuma Wanda muka tabayi tare Shima tayi kyau saikaga idan zaiyi a datse ni " ta fad'a tana nuna masa hotonta data tab'a mata da Abaya ta ce Kalli yaya Dan Allah kana ganin zaiyi "Amsar wayar yayi daidai idonshi yakai masa hotonta sanye cikin doguwar Riga Abaya ta yafa beil din rigar Dimple d'inta Duka sun lotsa sakamakon murmushin da tayi a hoton sosai hoton yayi masifar kyau Kallon mamaki ya dinga bin hoton dashi kafin ya d'ago ya kalli Chuchu da itama shidin take kallo ganin yanda ya rik'e wayar gam yana yiwa hoton wani irin kallon mai kama Dana mamaki maida Kallonshi yayi ga hoton Kara murza idonsa yayi Dan son tabbatarwa itadince kuwa koko gizau ne Tabbas ita ce " ya fad'a a ransa "Kafin ya sake Dagowa ya kalli Chuchu a karo na biyu ya ce.........✍🏿
Chapter 80 · 0% Book details