← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 129

Sashe 43

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

bud'e masa yake shirin fita saurin ruko hannunshi tayi ta ce "Ina ne ka kawoni nan kuma" ba tare da ya Kalleta ba ya ce sayar dake nazoyi dukda Zarah tasan wasa yake mata bai hanata tsorata ba marairaicewa tayi ta ce "Dan Allah kayi hakuri ka maidani Makaranta Dare nayi " Banza yayi mata ganin ya fita Ya sanyata saurin fita itama ta bishi baya tana karewa katafaran gidan Kallo Aljannar duniya kenan"ta fad'a cikin ranta binshi ta dingayi cikin Sauri duk Inda ya nufa Dan taji akwai karnika a gidan kuma ita daman ba abunda ta tsana sama da k'are ganin yayi mata nisa ga haushin Karen dake tunkarowa ya sanyata saurin Rugawa a guje Aiko nan Karen ya biyota Dan tayi gudu daukarsa bata Gaskiya ihu Zarah ta fasa tare da rugawa taje ta kankame MD tsam ta fashe da kuka tana yarfe hannu ta gama rikicewa daidai lokacin da Karen ya Iso Inda suke yana haushi murmushi MD yayi ya ce "matsoraciya a ransa common kare ya firgita ta Cikin kuka ta ce " Dan Allah ya Musty ka taimakamun kar Karen nan ya cijeni wlh tsoronsa nake please mubar gidan nan Dan Allah "ta fad'a ta na k'ara kankamesa " Shafa bayanta yayi yana Daddab'a cikin sigar lallashi batare da yace mata uffan ba shafa kan Karen yayi Tare da ce masa yabar wajen Lokaci guda Karen yabar wajen Ajiyar zuciya Zarah ta sauke Dan Allah kadai yasan irin yanda zuciyarta ke Bugawa saboda tsoro "matsoraciya saiki sakeni tunda na kori Karen kuma daga yau Kika karayimun musu ko na fad'a magana kika maida ga da abunda zan hadaki ina da ire_irensu sunfi goma" cike da kunya ta zame jikinta daga nashi turo baki tayi Jin Abunda ya ce "wara idanu yayi tare da nuna kanshi da yatsa ya ce " ni kikewa"cikin shagwabar da ta zame mata jiki duk sanda tazo mata ta ce "Nifa ba da kai nake ba " ta k'arasa fad'a hawaye na sauka daga idanunta "Had'iye kukan ya fad'a yana kama hannunta " kamar an d'auke nefa haka ta Had'iye kukan shi kanshi har Dariya taso ta bashi ya fusge "harsuka isa katafaran palourn gaban Zarah na fad'uwa saida ta kusa kauyanci cin karo da hadaddun turkey furnitures d'in da suke shake a palourn komai na palourn y'an waje ne bazaka tab'a cewa a Nigeria kake ba "a rakube ta zauna d'aya daga cikin kujerun palourn tana ta kalle_kalle a wayance Wanda bazaka tab'a cewa tanayi ba a ranta ta ce " Wasu na cikin wahala wasu bama susan anayi ba jifa Dan Allah wannan lafcecen gida da kayan cikinsa kamar baza a mutu ba "zaki iya tashi kije kiyi salla kafin na dawo ga bedroom Chan" ta tsinkayi muryarshi data dawo da ita daga duniyar tunanin da ta Lula Firgit ta Kalleshi kamar mai shirin fashewa da kuka ta ce "Amma kuma ni kad'ai zaka bari a gidan nan ni tsoro nakeji wlh karnikan nan karsu shigo Su cinyeni ni kadai" murmushin da baikai fuska ba yayi ya ce "bazan jima ba zandawo babu abunda zasu maki bazasu shigo nan ba " Badan taso ba ta ce "To Amma karka jima Dan Allah " Ba tare da ya amsa ta ba yayi Hanyar waje tanajin fitarshi ta turo baki tare bin kofar da harara ta ce "Mugu Allah saiya sakamun ta fad'a tana nufar d'akin da ya nuna mata Dan tayi salla Nanma saida tayi kauyanci cin karo da kayan alatun dake dakin ga gaban mirror din dake shake da kayan shafa irir_iri tab'e baki tayi cikin Sauri ta shiga toilet tayi alwala ta fito Bayan ta tada salla cikin Sauri ta bar d'akin Dan ji take a tsorace take palourn ta dawo ta zauna Kan kujera tare da Yin tagumi sai Bayan isha i Taji tsayuwar mota lek'awa tayi ta window taga shine cikin Sauri ta koma ta zauna harya shigo Mikewa tayi ta ce " yawwa nazo mu tafi ya Musty?Batare da ya Kalleta ba ya ce "Sai gobe " yana gama fad'ar haka ya Aje take away din da ya shigo dashi tare da Yin hanyar dayan bedroom d'in da Kallo ta bishi har ya wuce Tana turo baki ta daga wayata da Asmy ke kira daga bangaren Asmy ta ce "Wai kina ina harna dawo tun d'azu " Ina kd "ta fad'a kasa kasa" Kd kuma to me ya zaunar dake "Ya ce sai gobe " ta fad'a tana shirin fashewa da kuka "Daga bangaren Asmy tayi Dariya " Au cewa zakiyi Amarci za a sha keda Angon naki"Dogon tsaki Zarah taja cike da jin Haushi ta ce "Banza y'ar iska Allah kiyaye wannan ya zama mijina " kit ta kashe wayar tana Jan tsuka Daren ranar dai taga MD baida shirin maida ita gashi tunda ya shiga bai fito ba Bayan tayi Sallar isha I a palourn bacci ya kwasheta cike da gajiya gararanbar da suka sha A waje MD ko daman tuni yayi bacci Dan yau akwai gajiya a tare dashi Dan dawowarshi metting kenan daga Abuja suka had'u dasu Zarah washegari Around 10 Zarah ta shirya tana palour Tana jiran fitowarshi ya fito ya maida ita Cikin tsadaddan shaddarsa ya fito yasha shiga ta alfarma ta manyan mutane kallo d'aya Zarah tayi masa tayi saurin k'asa da kanta saboda gabanta dake fad'uwa sosai taga yayi wani irin masifar kyau a sanyaye ta ce "Ina kwana" muntashi lafiya ya fad'a yana karasowa palourn "Tare da cewa " Kinyi break fast ko?gyada mishi kai tayi "eh " Okay to muje a saukeki "Cikin farinciki Zarah ta d'ago ta ce " Thnks "Dan tayi mamaki dazai maida ita cikin Sauri saikuma ta ce " Naga bakayi break ba fa"Eh bana ra'ayi ya fad'a "Dan azumi yake tab'e baki Zarah tayi tare da mik'ewa ta ce " kai ka sani miskili kawai" a tare suka jera suka fito gwanin sha'awa kamar wasu masoya Dan sosai naga matching d'insu Shigowar Mota ya sanyasu tsayawa bin motar MD yayi da Kallo harta karaso parking space d'in yana kallon motar Kafin yaga fitowar Amera cikin shigar da ta saba ta K'ananan kaya driver yana rik'e da Akwatinta shock a wajen Amera tayi ganin mijinta sun fito tare da wata daga cikin gidan lokaci guda idonta ya rufe wani azababben kishi ya taso mata dak'yal ta iya daidaita numfashinta dake sartse mata cikin bala'i da masifa ta tunkaro Inda suke Wanda har lokacin suma kallonta suke musamman MD da yayi mamakin zuwanta Zarah ko tuni cikinta ya Dori ruwa Ganin yanda take tunkarosu " Tsaye Amera tayi tare da daure k'aramun beil din da ta yafa a kugu ta ce "Yau akwai kutumar bura uba a garin nan kace yau akwai tashin bomb a kaduna wanda zai tashi da uban kowa Wace karuwar y'ar Iskar ce wannan Mustapha ?......✍🏿
Chapter 43 · 0% Book details