← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 129

Sashe 106

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba d'aya MD yana rikice ya rasa wace irin Godiya zaiyiwa Allah s w a da yayi mashi wannan gagarumar kyautar yara Ukku lokaci guda yana Rungume da babyn yayi sujudu shukur sosai yake kwararo yabo da gdy ga Allah s w a Kafin ya bud'e fuskarsa d'auke da murmushi kamar gonar Auduga ya kalli Ammy ta ce "Ammy wai wannan din Duka yara na ne da gaske" murmushi kawai Ammy ke masa Dan farinciki harya mantar da ita wani b'acin rai Ta ce "yaranka ne babana " Daga hannu ya sakeyi ya ce "Allah Alhmdllh Alhmdllh bansan da wasu kalamai zanyi amfani ba wajen gode Maka " murmushi kawai suke Chuchu ma uwar kuka yanzu andawo murmushi cikin d'oki ta ce "Yaya wlh Duka kamarsu d'aya kuma dakai sukayo kama " daidai lokacin da na hannun Ammy ya fara kuka jijjigashi Ammy tayi ta ce "Yi Sauri Babana Kaje gida D'akin nan na kusa da na Chuchu zakaga kayan jarirai kodan ku tafi da chuchun Aje a d'auko duk abunda ya kamata sannan Ka taho da Dabino mai laushi tare da zamzam ka basu " to to Ammy Amma ya jikin nata ita mu bari a fito da ita"Jikinta Alhmdllh Dr ya ce "anwuce d'akin Hutu da ita bazamu samu ganinta yanzu ba allurar bata sake ta ba kuje ku kawo kayan yaran" Mik'a mata Namijin Chuchu tayi shiko MD Kallon yarinyar kawai yake dake tsala kuka yana murmushi wai yau shine rik'e da jininsa sosai yaji k'aunar yaran ta musamman Na ratsa sa wata nurse ta amshi yaran biyu Ammy ta rik'e d'aya Dan Aje a shirya su Kafin a kawo kayan "Cikin doki Ammy ta kira Zey tayi mata albishir Hajiya kaka takeson kira ta mata albishir to bata San taya zatayi musu bayanin zahra ba Hakanan dai Ammy ta lalubo number Hajiya Bayan suun gaisa ta ce " Hajiya Albishir na kira miki addu'ar ki dai ta amsu Matar MD ta sauka yanzu an haifi y'an Ukku"Ammy saida ta kauda wayar daga kunnanta saboda irin. Bud'ar da Hajiya ta rangada kira take "Alhmdllh Alhmdllh Ina kike rukayya maza taho ki kiramun iyayenki muyi musu Babban Albishir Matar Mustapha ta haihu"Ammy lura da Hajiya murna tama mantar da waya ya sanyata katse wayar tana murmushi ta window ta lek'a ta Hango zahra dake baccin wahala sanye da blue din rigar da aka gama mata aiki hannunta biyu Duka sanye da kalula d'aya Karin jinin da aka diba a na MD ne d'aya kuma Karin ruwa ne Goge hawayenta Ammy tayi ta ce "Allah ya baki lafiya zahra ya tashi kafadunki" ba ayi Minti goma ba saiga zey ganin yanda ta fito daga motar kasan ba karamun gudu ta sharara ba cikin farinciki ta ce "Ammy da gaske Ta haihu kuma y'an ukku yayanmu ahima ya zama uba" Murmushi ammy tayi mata ta ce "da gaske zainab kinga ikon Allah ko Yanzu haka Ana ciki ana shirya yaran ana jiran su maryam su kawo kayan da za a sanya musu kinsan a dimauce muka zo " Ajiyar zuciya zey ta sauke tare da goge hawayen farinciki ta ce "Alhmdllh ammy Adduar tsawon shekaru goma ta amsu Ta inda ba ayi tsammani ba ina mamyn take yanzu?tana ciki kinsan cs akayi " wayyo Allah ya bata lfy kaico "ba a dau lokaci ba su Chuchu sunkadawo tana rik'e da kayyayakin MD fara'a ta kasa barin fuskar sa sai nan nan yake Bayan an shirya yaran nanfa Chuchu ta shiga yi musu hoto Kamarsu d'aya har macen dukansu kuma da dimple d'insu irin na zahra dukda jariraine amma saida suka fito Fari da kammani da kyau duka MD suka biyo dimple din zahra kadai suka biyo nan fa aka shiga liliyar yaran d'aya Bayan daya MD ya d'aukesu ya tauna musu Dabino da zamzam rik'e Namijin dayan yayi yana ta kallonsa kamar zai cinyeta sai Murmushi yake yanajin wani irin farinciki na ratsa sa Ammy bata damu da irin rawar k'afar da MD yake ba ko Kara bayayi saboda tasan dole yayi abunda aka ta roka tsawon shekara goma yanzu Allah ya kawo ai dole yayi rawar kafa ganin yaran sun fara kuka ne ya sanya hankalin MD tashi duk ya rud'e Kallon Ammy yayi ya ce " please Ammy me za ayi musu suna kuka fa "Harararsa Ammy tayi ta ce " Waikai baka da ta ido"Sosai k'eya yayi ya ce "Ba haka bane Ammy kar wani abun ya samesu" girgiza kai kawai tayi koda Chuchu ta kira Asmy ta fad'a mata irin ihun murnar da tayi bana wasa bane farincikin data shiga bana wasa bane Koda ta fad'awa mamansu itama tayi farinciki matuka tana Jinjina ikon Allah tare suka shirya a motar babansu ya taho dasu Kaduna Dan suga jikin na zahra tunda ance musu cs ne "Kafin one hour sun Iso sosai Ammy ta karramasu da girmamasu dukda a Asibiti ne akayiwa juna barka Asmy ko tunda ta rik'e macen taki ba kowa saida tayi hawayen farinciki wai wannan din Duka yaran zahra ne nanfa hankali ya koma jiran farkawar Zahra Dan har yanzu saida su lek'a ta window MD ko tsaye yayi a jikin window din sosai yaji tausayinta ya k'ara kamashi ganin halin da take ciki saida yaga y'an gidan su Asmy tukwana yabar jikin Window din sai wajen 4pm zahra ta farka koda ta bud'e idonta Kallon d'akin ta dingayi kafin ta kalli jikinta da hannunta duk drip yunkurawa tasoyi Dan ta tashi amma ta kasa komawa tayi tana lumshe ido wasu hawaye na zubo mata tunowa da wahalar da tasha dazu bata manta da lokacin da za ayi mata cs ba kasancewar bata ido biyu akayi mata ba yasanyata bata tuna ba har yanzu allurar bata saketa ba saboda bibbiyu take ganin komai daidai lokacin da Nurse biyu suka shigo suka duba ta kafin a sauya mata daki aka maida ita wani koda su Ammy suka shiga Sannu kawai suke mata bata iya magana ba sai daga musu kai Goge hawaye Asmy tayi taje gefenta ta ce "Sannu sis" Itama gyada mata kai kawai tayi tana lumshe ido Dan kanta duk Juyawa yake "MD ko daga jikin kofa yake kallonta Ammy ce ta ce Ku Aje mata yaran ta gansu gefenta aka aje mata su Kafin Ammy ta ce " Bud'e ido kiga kyautar da Allah yayi maki daughter "a hankali zahra ta bud'e idanunta har lokacin ba komai take gani ba " Kallon Yaran ta dingayi dukda ba Sosai taga fuskarsu ba Amma har a ranta sosai taji k'auna da soyayyar yaran na ratsa ta kenan y'an Ukku Ta Haifa kallonsu kawai take Ammy na ganin haka saitayi murmushi ta jima tana kallonsu kafin ta daga hannunta d'ayan dake rik'e da drip Da niyyar ta tab'a na kusan nata Daga tsayen da MD yake ya matso ya ce "Ki bari Mamy drip ne hannunki bayason motsawa" Harararsa kasa kasa Ammy tayi ya sanyashi yin shiru amma har lokacin hankalinshi na Wajenta kallonta Ammy tayi ta ce "Zaki iya" gyada mata kai zahra tayi D'aukar shi tayi Ammy ta Aje mata shi a gefenta a hankali zahra tasa hannu ta zagayosa ta matsesa gefenta tana Kallonshi tana kallon sauran Maman Asmy ce ta ce "karfa ki matse sa zahra" Bazan masa komai ba "ta fad'a kasa kasa " Girgiza kai Ammy tayi ta ce 'Allahsrk d'a da uwa kenan sai ALLAH "Dr ne ya shigo Bayan ya duba ta ya tambayeta Saidai ta gyad'a masa kai Dan maganar nauyinta takeji " Ammy ce ta ce "Dr kamarfa har yanzu bata dawo daidai ba " Eh daman bazata dawo daidai yanzu ba ita hakanma da sauki wasu allurar tana dad'ewa tana daukarsu sosai zakiga har suna wasu maganganu kamar marassa kai da ta ido biyu ce akayi mata zata tashi normal amma itama zuwa gobe zata dawo normal please a barta ita da mutum d'aya Ta samu Hutu sosai "Ammy tace zata zauna da zahra sauran duk su koma gida dukda maman Asmy taso zama Wajenta MD ma yaso ace shiya zauna Wajenta Dan hankalinshi yanzu yana ga samun Lafiyarta Ga damuwarshi na abunda za Aba yaran Dan sun fara kuka Sosai Ammy ta kula da Zahra da Yaran tamkar kwai Bayan ta had'a mata Malta da isashshiyar madara Abu mai ruwa ruwa dai ta dinga bata sannan aka bata maganin da tasha dan asamu abincin yaran yazo sai wajen 8pm aka samu ruwan yazo Ammy ta d'ora mata su ta dinga feeding d'insu dukda taji zafi da kunyar ammy haka dai ta daure saboda k'aunar yaran da takeji ta musamman washegari zahra ta dawo normal ta dawo hayyacinta har tana iya zaunawa a danyi Hira da ita dukda nauyin Ammy da maman su Asmy da takeji MD ko ko kallo bai isheta ba Koda yayi mata ya jiki a takaice ta amsa masa da yawwa Wanda baijin dadin hakan ba Ganin yawan matan a d'akin yasanya suka fita shida Jabir shi kanshi Jabir ya girgiza da jin zahra tripplet ta Haifa Sai sannan MD hankalinshi yadan kwanta ganin jikin zahra da sauki sai sannan ya fara tashi sayayyarsa Wanda ba iya yaran yakeyiwa ba hada Momynsu Hajiya ma ranar tazo zo kuga murna da doki Da farinciki Saidai tayi mamakin da ba Amera ta gani ba Koda ta tambayi Ammy ya haka ce Mata tayi kiyi hakuri Hajiya idan muka koma gida za ayi miki bayani su Asmy da mamansu kullum sai sunzo sai yamma suke tafiya Funtua sosai aikin na zahra yayi kyau a kwana na hud'u aka sallamesu suka koma gida Inda Ammy ta ninka kulawar da take mata kafin kace me labarin haihuwar Tripple. D'in MD ya baza gari har internet sosai abokan arziki suke kiransa abokanan kasuwansa dama manya suna kiransa suna masa Barka har gajiya yake da d'aukar wayar wasu daga cikin y'an uwan Ammy ma.dake.india duk sunzo banda y'an uwan Abban su MD na Maiduguri suma sosai suka taho kwansu da kwalkwatarsu ranar daga Ammy sai Hajiya ta labartawa mata abunda MD yayi Dan shaida har videon d'aurin Auren ta nuna mata "Maimakon Ammy taga Hajiya ta daga hankalinta saitaga ta sauke ajiyar zuciya ta ce " na godewa Allah da ba a hanyar banza akayi cikin
Chapter 106 · 0% Book details