Sashe 36
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ne ya ce " bawan Allan nan yana bani tausayi wlh tsawon shekaru A haka Kaiba matacce ba kaiba mai rai ba Kuma ga dukkan Alamu sihiri ne mai k'arfi akayi masa Allah dai ya basa lafiya"Ameen Kawai MD ya ce "Jaber ne ya ce " Bloody ya maganarmu ta rannan Ina takardar sakin Zarah"Ka cire hannunka a maganar kawai "Cewar MD " da mamaki jaber ya ce "ohh haka kace amma dai kasan nine jadanin Shirin ko ?lumshe ido MD yayi kafin ya bud'e ya ce " Eh nace ka cire hannunka kawai "Jinjina kai Jaber yayi ya ce " Hmmmm Na cire daga yau insha Allahu"koda suka isa kd Gidansu ya wuce Ammy ce ta Kallesa ta ce "ya naga kamar akwai alamar gajiya a tattare dakai"eh Wlh Ammy daga Gombe nake " Ammy ta ce "Ah dole ka gaji kam Ya Jikin na Baban to?dan tasan shi kadai ne ke kaishi gombe"Alhmdll Ammy Da sauki za ace yanzu kam an fara samun cigaba sosai" Cikin tausayawa Ammy ta ce "Allah sarki Bawan Allah ana ta kankarar zunubi Allah dai ya basa lafiya nima ina son Samun lokaci naje ba dama ya kamata ace munkoma mun dubasa Allah dai ya basa lafiya Gaskiya duniya ba Gaskiya wlh A kassara mutum shekara da shekaru tsohon Allah wata Allah Dan tsohon nan a k'alla zaiyi uba dani aka kassara bawan Allah a zaune Allah dai yayi mana tsari da makiya na fili Dana boye Shiyasa nake ta ce maka ku dage da addu'a babana mutanen yanzu ba Gaskiya Allah ya kare munkai ya tsaremun kai babana ya k'ara maka zuciyar imanin irin taimakon da kake Allah ya k'ara maka budin da zaka ninka fiye da na da " ameen Ammynah "MD ya fad'a... Washegari Zarah ce zaune tanayiwa Chuchu kitso Wanda dak'yal ta samu ake mata wai batason kitso kodan yawan gashin da sulbi Dan Sai a daure ita Zarah har mamaki take gashin Chuchu sak na India wa amma Kuma gata ita Bak'a ce bata da Haske sosai Bayan ta gama yi mata Wayar ta ce tayi ringing ganin ya Hafiz ne ya sanyata saurin d'auka Hira suka shigayi sosai yake zuba kalamai masu dadi dukda ba maida masa take ba Sosai Dan kunyarsa take ji kawarta ce Hibba ta shigo Bayan sun gaisa da Chuchu Da Asmy da ta gama sallar la'asr kusa da Zarah ta zauna katse wayar tayi tare da kallonta ta ce " Manya daga ina "Murmushi kawai hibba tayi ta ce " Gaku manya turoni akayi Malam Umar ya ce Kije wai "Da mamaki Zarah ta ce " Mlm Umar kuma Niko me zai had'ani dashi kofa magana bayi muke ba "Wara hannu tayi ta ce " Nima kin tambayeni kije kiji"chuchu ce tayi dariya ta ce "Ko shima yana ciki dai wai ya maganar mlm sulaiman dinnan ya kuka kare dashi" Asmy tayi dariya ta ce "Nima na manta nayi mata wannan tambayar " Hibba tayi dariya ta ce "Kila yaga ba sarki sai Allah ya hakura" Tabe baki zarah tayi ce "Ni harnama mance dashi bana yarda ma mu hadu dashi idan ya aika a kirani kuma ba zuwa nake ba " Hibba ta ce"Ki daibi a hankali wlh karya kada ke"chuchu taja tsaki ta ce "kufa duk laifinkune ma da kuke tsorata da irinsu wlh dan sunga ba a kaisu sama shiyasa suke wannan iskancin ya kada ita d'in ya gani wlh sainayi hanyar da za a kaisa sama sai yayi ta aikinsa" duk dariya sukayiwa chuchu wai zaiyi ta aikinsa Hijab d'inta ta sanya har kasa tare suka isa har office d'in Inda hibba ta tsaya daga waje shiga Zarah tayi Bayan ta gaishesa ya amsa tare da nuna mata kujera da ta zauna a sanyaye ta zauna wayarsa dake kan table tayi ringing cikin Sauri ya d'auka Ita dai bataji me sukace ba saiji tayi ya mik'o mata wayar akan ta amsa"Nuna kanta tayi ta ce "Ni,?Eh amshi zakuyi magana " a sanyaye ta amshi wayar tare da karawa a kunnanta "ki sameni a Gidan da na kawoki Rannan karki wuce 30 minutes "ta tsinkayi muryarsa daga cikin wayar" satar kallon Mlm tayi taga hankalinsa baya ma wajen "Murguda masa baki tayi tare da cewa " Idan fa naki ?ki ganni a makarantar yanzu na daukeki ta karfi"tsaki taja tare da cewa "to bazanzo ba aini ba y'ar iska bace " Sosai yayi mamakin jin furucin nata ya ce "Okay nine d'an iskan kenan?turo baki gaba tayi ta ce "oho dai Sai Anjima nidai ba Inda zanje " okay kijirayi zuwana Nan da 1 hour bakizo ba Zakiyi mamakina villager girl kawai"Yana gama Fad'ar Hakan ya katse kiran.......✍🏿