← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 129

Sashe 77

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

ce ta shigo d'akin da take kwance kasancewar Asmy ta fita Sayayya kasuwa cike da kulawa ta ce "Taso Zarah ki daure kisha Maganin nan " Goge hawayenta tayi tare da mik'ewa zaune ta ce "To Mama" Girgiza kai Mama tayi ta ce "Yauma kukan ne kikayi ko Zarah?na rasa abunda yake damunki keda Asma'u tunda kuka dawo daga makarantar nan bana gane kanku idan tunanin rabuwa kuke ai baku rabu ba kuna tare Har abada Aure baya raba Abuta to na lura abun naku ma ya wuce yanda nake tunani" Shigowar Asmy d'akin ya sanya Mama kallonta tare da cewa "kema shigo" a sanyaye ta shigo d'akin duk ta rame itama zaunawa tayi gefen gadon dukansu sukayi kasa da kansu kamar wasu munafukai "Mama ta d'ora da cewa " Dan Allah ku saki jikinku ayi bikin nan cikin walwala Ke yanzu Asmy bake ce aminiyarta ba ko ita bata saki jiki ba aike yakamata ace kinzama kirjin biki kin jajirce a bikin kawarki amma sainaga kema din kamar kin fita solancewa sakarcine yanzu ina tsammanin ko rabon katin gayyata baku kaiwa kawayenku ba bacin Anko da baku raba ba wannan Asama kun lakanta hakan da kurewar lokaci To wlh nidai ina fad'a muku tun wuri ku nutsu kusan abunda kuke"a sanyaye Zarah ta ce "Insha Allah Mama" Asmy ma ta ce "Insha Allah Mama zamuyi rabon IV din Tunda da sauran time" Da dai yafiye muku maza ki Shanye ta fad'a tana mik'awa Zarah cup din da tunda taji warin abun taji zuciyarta na wani irin tashi tana kafawa a baki kurba d'aya tayi taji wani irin amai na tunkaromata a Guje ta tashi tare da rugawa tsakar gidan a makwararo ta durkushe nan ta fara sheka amai kamar zata amayar da y'ay'an cikinta daga Asmy har Mama biyota sukayi Inda suka sameta durkushe sai kwarara amai take kamar zata amayar da y'an cikinta.........✍
Chapter 77 · 0% Book details