← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 129

Sashe 52

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dukda Zarah ta saba da maganganun Mama Rabi amma wannan Karin kam sunyi mata ciwo sosai Saida ta Goge hawaye Tabbas Rashin uwa Babban gibi ne a rayuwa ta tabbata da mahaifiyarta na raye da murna da farinciki da tarairaya zata tarbeta cike da kewarta da tayi tsawon kwanaki amma yanzu ta dawo Kalmar da za a fara tarbarta da ita ta muzanci Bayan ta Goge hawayen da suka zubo mata cikin k'arfin hali ta ce "Ina yini Mama" Dogon tsaki Mama Rabi taja ta ce "Yinin yana gidan su tsintacciyar uwarki da ba asan asalinta Dan Ubanki nace ina buk'atar gaisuwarkine Munafuka " Duk yanda Zarah taso daurewa kasawa tayi batasan lokacin data fashe da wani irin kuka ba Ta Ruga d'akinta kan katifarta tayi rubda ciki tana Kara fashewa da kuka wannan wace irin jarabace ta Mama Rabi mahaifiyarta da take ma kabari bata barta ba duk irin abunda zata mata baya mata ciwo kamar yanda take sanyo mahaifiyarta ji take yanzu kuma bazata iya jurar zagin da Mama Rabi ke yiwa mahaifiyarta ba dake k'asa kwance sosai take kuka kamar ranta zai fita tana Jin rad'ad'in zafin maraicin da ta tashi dashi na Rashin Mahaifiya ta jima tana kuka kafin bacci ya d'auketa Mama Rabi ko tsaki taja bak'inciki duk ya isheta ga na yaranta gardama_gardama sun giga a gida sunzama sanatoci Ba Aure duk Wanda yazo da anyi tare ya tafi gashi ko takardar sec basu da ita amma yarinyar da taso ta tagayyara ita ce Take neman shige mata gaba bayan ta sauke qur'ani yanzu kuma Hartana shirin gama jami,'a sannan ga Aurenta a sanye "girgiza kafa kawai take ta rasa yanda zatayi kafin ta mik'e ta sanya hijab d'inta tana huci ta ce " wlh bazaiyuba ashe ma na zama banza dole ne a fasa auran nan kuma dole.ne tayi abun kunyar da mashinshini ma nan gaba bazata samu ba dole ne tayi abun kunyar da duniya zata gani ta tsine mata mahaifin nata ma da take tutiyar yana kaunarta saikin zama abun kyama a garesa dani take zancen karamar kwaruwa "ta fad'a tare da fita daga gidan kamar zata tashi sama...Zarah cikin bacci taji dawowar Baba Firgit ta mik'e tare da fitowa tsakar gida cikin farinciki Baba ya tarbi Zarah ya na cewa " Oyoyo Zarah ta Sannu da zuwa andawo lafiya ya gajiya"Alhmdllh Baba na nayi kewarka sosai "murmushi yayi na so da k'aunar y'ar tashi ya ce " Nima nayi kewarki y'ar Amanar Baba yanzu dai bari na zauna na sha labarin makaranta "Dariya tayi ta ce " Aiko Baba zaka shashi"Bayan ya Aje ledar hannunshi a kujera ya zauna itakuma ta zauna tabarma nan suka shiga labari shida y'ar tashi sosai Zarah ta mance da bakincikin da Mama Rabi ta kumsa mata Tabbas da babu Baba da batasan halin da zata shiga ba Amma ko tana cikin bak'inciki idan ta tuna da mahaifinta mai kaunarta sai taji Kashi sittin na damuwarta ya ragu Cikin hirar ne yake tambayarta ya ce "Ina maman taku Naji banji taba tunda na shigo" bansaniba Baba kila ta fita Baba ina khairat bangantaba "Khairat tana makarantar kwana Ajiwa na Turata Dan nafison ta samu ingantaccen Ilimi a Chan boarding akan a nan dan kartayi shiririta " sosai Zarah taji dad'in tura khairat boarding school da Baba yayi Mama Rabi ita ce bata dawo ba sai Bayan isha i koda Malam ya tambayeta ina taje bata fad'a masa ba cewa tayi "makociyarmu ce ta tsohon gidansu Habiba ce ta rasu natafi Sutura ni kuma kaga Ba waya gareniba bare na kiraka ba " Batare da Baba ya kawo komai ba ya ce "Subhanallahi Allah ya jikanta ina su habibar ne naga suma basanan " Tana shiga daki ta ce "Eh basu dawo ba " girgiza kai yayi Dan shi kanshi yawon na su habiba na damunshi Wanda har mutane na cewa Dan ba Y'ayanshi bane yasa yake barinsu sakaka nanko Dan basusan anfi k'arfin shi bane indai ba zaunawa zaiyi gida yayi gadin su ba a gida baya mancewa ranar da ya dinga musu fad'a akan bleaching karshe Rashin kunya Habiba taso tamai duk girmanshi bata gani ba hakan shiyasa ya tsame yaranshi a hankali daga cikinsu kar tarbiyarsu ta gurbata ya mayar da khairat boarding ita kuma Safiya ya barta a Batsari washe gari Zarah tayi aikin gidan kamar ko yaushe idan ta dawo wajen 11 ta gama komai ta koma daki tana Dan dudduba wayarta da bata bari kowa ya Gani ba Asmy ta shigo d'akin Bayan ta zauna bakin katifar Kallonta Zarah tayi ta ce "Yanzu nake tunaninki a raina" nima wlh Naji shiru baki leko ba shiyasa na shigo "suntaba Hira sosai Cikin hirar ne Asmy ta ce " wai Zarah kina shan maganin nan kuwa"wani.magani"Zarah ta tambayeta "Wanda Dr Halima ta fad'a kenan" Ohhhh eh ina sha me kika gani"Bakomai daman Dan nayi maki tuni ne karki manta"murmushi Zarah tayi ta ce "Ai kozan manta da komai bazan manta da maganin nan ba kullum saina sha sa koda kuwa ina gida ne saboda tace ba a tsallaken sha sannan Kinga danaje saya na sayo na Wata biyu Wanda har hutunmu ya k'are ina sha " Ajiyar zuciya Asmy ta sauke ta ce "Alhamdulilla yanzu saura wata nawa wata taran ya cika wai lissaafina ya shige " Turo baki Zarah tayi ta ce "Keda kuka had'a aike zan tambaya" Dariya Asmy tayi ta ce"a a a kedai da kika d'ana Auran kika zama y'ar hannu ai ke zan tambaya"Harara Zarah ta galla mata ta ce "zanyi maganinki " Dariya Asmy tayi wayar Zarah ce tayi ringing tana ganin Chuchu ce mai. Kiran tayi saurin d'auka daga bangaren Chuchu cikin iyayinta ta ce "I really miss uh momcy shine daga jiya zuwa yau harkin manta dani nikam kina raina Kinga ina tashi daga bacci kena fara kira" da murmushi a fuskar Zarah ta ce "Nima kina raina daughter daman yanzu nake niyyar Kiranki kunkoma lafiya ya Ammy na fatan tana lafiya" Ammynki lafiyarta qalau tana gaisheki in banda bama kusa ai da na kai mata Dan jiyama har dare.muna ta hirarki"Sun tab'a Hira sosai da Chuchu kafin Asmy ta amshi wayar itama suka gaisa da Chuchu Bayan sun katse wayar Asmy ta na juya wayar Zarah ta ce "Wlh wayar nan tsada gareta Zarah karki yarda wani gidan nan ya gani idan suka gani zasu iya sace miki wlh ko kuma su miki munafurci wajen Baba ki boyeta sosai" hakane Asmy kinsan yanda za ayi sim Dina zan cire kawai na baki wayar ki boyomun ita gidanku "To ke ki rik'e wacce " akwai kudi a hannuna zan saya keypad Dan nima ina tsoron rik'e wayar nan a gidan nan "Hakane kuma wannanma shawarace Asmy tafada kafin ta ce " Allah dai ya sakawa mutumin nan wlh ga Alamun yana da kirki tunda har ya iya baki waya mai tsada haka "uhm kawai Zarah ta ce Asmy tab'a 3k ta ce idan ta samu Mai shiga kasuwa ya sayo mata key pad sannan ta bata tata ta tafi da ita ta ce idan tanason amfani da ita taje gidansu tayi haka ko akayi da magriba Asmy ta Aiko almajirinsu ya kawowa Zarah wayar Inda ta d'ora sim dinta a ciki kamar jira ake ta d'ora saiga kira ya shigo saida ta kusa katsewa kafin ta d'auka cikin k'asa da murya ta ce " ina yini ya Hafiz "Lafiya qalau my bride kin jini shiru kwana biyu wlh exams ce ta boyeni kinsan nan da wata Ukku na gama sch d'innan" bata San ya akayi ba Zarah taji gabanta ya fad'i cikin k'arfin hali ta ce "Amma karatun naku yayi saurifa yaya hafiz" Oh hakama zakice ai nazata cewa ma zakiyi ranakun basa gudu Naji bama kiyi d'okin da na fad'a maki na kusa dawowa ba ko my Zarah"ba haka bane ya Hafiz Ina farinciki mana ai nafi kowa farincikin son ganinka "sun tab'a Hira sosai kafin Su katse abokinta Yusuf ta kira Inda Shima.suka sha Hira kafin ta katse koda ta kwanta batasan ya akayi ba kawai taji ya Musty ya fad'o mata a rai a hankali ta ce " Ko yana ina "tsawon 3wks kenan rabonta dashi lokaci guda ta saki murmushin da batasan dalilin yinshi ba lumshe ido tayi kafin ta bud'e irin rayuwar da sukayi a gidan ta shiga dawo mata kafin bacci barawo yayi awon gaba da ita batare da ta shirya ba... <KD> " wai honey laifin me nayi maka ne yanzu duk ka daina kulani kuma yaushe rabon ma da ka nemu hakkinka waje na "ta fad'a kamar zatayi kuka " kwantota yayi jikinshi a hankali Dan yasanta da Sanya damuwa a rai ya ce "Nothing My Merah me kika gani" tana shigewa jikinshi ta ce "Ai naga yanzu baka kula dani sosai Kamar da sannan da ko na hanaka fushinka baya zuwa ko ina amma yanzu kafi wata nawa baka kusanceni ba Bayan da ko sati biyu baka jure hakan muddin muna tare" murmushin da ka gani zaka ma'anarshi yayi mata ya ce "Merah kenan na barki ki huta kawai" Kamar zatayi kuka ta ce " nasan har yanzu fushi kake dani Dan Allah honey kayi hakuri nima saidaga baya nayi regret din abunda nayi nasan ban kyauta ba please forgive me my love"ya wuce wannan na fad'a maki bakomai fa kinsan bansan ayita magana d'aya is okay please "Okay Thnks hakkina fa" a ranshi ya ce "Yau rigima kikeji Amera saina hakura da abu ki takalo Alhalin ba iya jurewa zakiyi ba " a fili kuwa cewa yayi "a gajiye nake bacci nakesonyi" Kuka ta fashe dashi na kissa ta ce "Allah ni ban yarda ba Ai nima ina da hakki a kanka Indai bakayi ba bazai tabbatarmun da ka huce ba " Dafe kanshi yayi da hannu kafin ya d'ago ya ce "Idan kikamun abunda bai kamata?ka dau mataki wlh na yarda" tayi saurin fad'a Daren ranar Amera ta yabawa aya zakinta Dan duk kwanakin da ya kwashe da kewar abun akanta ya juye dukda bai samu yanda yake so ba kamar yanda yake samu a wajen Zarah amma wannan Karin ba laifi Amera ta daure tayi jarumta ba raki ba komai har saida
Chapter 52 · 0% Book details