← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 129

Sashe 90

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin Sauri MD ya zame bakinsa dukda yaji zafin cizon da tayi masa amma bai nuna ba har suka isa Abuja zahra a hauka ce take lokacin da suka isa 11pm harta gota kin fita tayi daga motar bayan isarsu gidansa dake Buzu quarters sosai take kuka tana ja masa Allah ya isa Wanda sosai yakejin zafin hakan a cikin ransa Saida ya ciccibeta tukwana ya samu ya fito da ita zullewa take amma ya ki sakinta ya Rungumeta jikinsa sosai yayi Hanyar part din da ita shidai driver kanshi gaba d'aya kulle yake Dan yayi mamakin abubuwan da suka faru yasan dai uban gidan nasa mutumin kirki ne to me zai hadasa da wannan yarinyar har tana ikirarin yayi mata ciki"Sauri barin wannan tunanin yayi ya ce "Ba abunda ya shafeni bane inje inyi ta aiki na " MD bai dire ta ko ina ba sai tafkeken bedroom dinsa dake gidan zahra na ganin haka ta zabura ta mik'e kamar mahaukaciya ta ce "me kake nufi da satoni da kayi Bayan tozartani din da kayi bai isheka ba wlh wannan Karin baka isa ba Saidai duk abunda zai faru ya faru Ka cuce ni Allah ya isa tsakani na dakai Daman kasan da cikinka jikina ka bari na koma gidanmu dashi Dan na wulakanta a idon iyaye na da jama'a sannan kak'i saki na kawai d'anka wulakanta ni nasan Duka da gangan kayi wannan din Allah ya isa tsakani na dakai kuma wlh saina zubar da tsinannan cikin....MD baisan lokacin dayayi saurin rufe mata baki ba cikin muryar tashin hankali ya ce " Karki tsinewa Cikina Mamy look ki tsaya mu fahimci Juna "fusgewa tayi da karfi tace " wace fahimtar juna,ai ba wata sauran fahimta ni dakai Wlh tallahi kaji na rantse saina zubar da kaddararran cikin nan mugu azzalumi macuci Alla ya isa tsakani na dakai"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un MD ya shiga maimaitawa Dan a halin yanzu ji yake babu abunda yake so yake k'auna kuma yasa guri akansa kamar cikin nan dake jikinta da ya tabbatar yanzu sosai yaji k'aunar cikin na musamman Wanda yakejin bazai tab'a iya jure rashinsa ba ga zafin irin yanda take ja masa Allah ya isa "Toshe kunnuwanshu yayi tare da rumtse ido Dan bayajin zai iya jure kalaman da take danganashi dasu " Zarah wata tsanar MD takeji wacce bata tabajin irinta ba A matuk'ar haukace ta mik'e tare da kalle kallen Inda zataga mabugi Dan zuciyarta wata irin tafarfasa take "gaba mirror ta ruga kamar mahaukaciya ta fara warwatsa abubuwan da ta gani a kai tare fara tillawa MD Sosai yakeyi mata kallon mamakin abunda take" Mikewa yayi yana shirin nufar Inda take ta tilla masa.kwalbar turare a kafa ji kake tassss "Auchhh ya fad'a yana kallon kafarsa da ta fara fitar da jini Kallonta yayi yaga yanda take kuka ganin tana shirin Bugawa cikinta wata kwalbar baisan lokacin d'aya take kwalbar ba ya chafke ta hannunta Tare da janyota jikinsa cikin b'acin rai ya ce " Baki da hankali ne.wai Mamy me kike haka illata kanki zakiyi"ka sakeni ina ruwanka da rayuwata ina ruwanka da koma meye zanyi wlh na tsaneka na tsani cikin nan "ta fad'a tana bugar cikinta da k'arfin gaske " a d'imauce MD ya rik'e hannayenta sosai baimajin zafin yankan da yayi yana gani ido biyu tana shirin yi masa asarar ciki"Gado ya nufa da ita ta karfi tana fusgewa ya kwantar da ita fusgewa take sosai Kamar mai iska tana kai masa Duka da Allah ya isa "har 3:PM MD da zahra ba Wanda ya rintsa sosai ta haukace masa da tayi nan ta tallabosa dak'yal ya samu ya matseta jikinshi sosai ya rasa yanda zaiyi da ita addu'ar ko yayi ta ba adadi yana tofa mata matseta yayi sosai a jikinsa yanda Bazata iya motsi ba tun tana Kokarin kwacewa harta kasa jikinta ya mutu muryarta ta dishe da kuka a haka ya samu bacci ya kwasheta MD na ganin tayi bacci Ajiyar zuciya ya sauke dukda farincikin cikin dake jikinta bai hana zuciyarsa shiga damuwa ba Ganin irin tsanarsa a idon yarinyar k'iri k'iri kallonta ya dingayi yanda take baccin kasan baccin wahala na kallon cikinta yayi da yaso fitowa Wanda ba kowa zai fahimta ba a hankali ya shafa Cikin ya ce " Allah ya fito mun da ke Ko kai lafiya"Kwata kwata ji yayi bacci ya kauracewa idonsa ranar a zaune MD ya kwana rik'e da zahra da har lokacin take jikinsa duk yanda yaji ta motsa sai yaji har cikin ransa.....bangaren Asmy tunda taga tafiyar zahra ta zaune wajen ta fashe da wani irin kuka Nan Chuchu ta dawo ta isketa ta ce "Ina momcy din "" Ganin yanda take kukan ne ya tsoratata da Chuchu ta ce "Ki fad'a mun Inda take karkice mun sunzo sunkoma da ita" ta fad'a cikin daga murya sai sannan Asmy ta d'ago cikin dakiya ta ce "Wanda yayi mata ne yazo ya tafi da ita " What ya tafi da ita kuma kika zauna a nan kina ganin ina ya tafi da ita"ruko hannunta Asmy tayi ta ce "Na yarda ya tafi da ita d'in ne badan komai ba saidan hakan zaifi mata sassauci iyayenmu bazasu tab'a fahimtar mu ba Chuchu duk nice silar shigar zahra halin nan da take ciki Nina cuceta na zalince ta " ta fad'a tana fashewa da kuka "Sosai kwalwar Chuchu ta chushe ta ce " me kike nufi Asmy Dan Allah ku fiddani cikin duhu kuna rud'ar dani Na kasa fahimtar komai"Ruko hannunta Asmy tayi tana zaunar da ita gefenta ta ce "Chuchu cikin dake jikin zahra ba cikin shege bane cikin sunna ne kamar kowani d'a Saidai nasan ba kowa zai fahimci hakan ba " ta fad'a kukan nadama nacin karfinta karfinta "Da mamaki fuskar Chuchu ta ce " me kike nufi Asmy bangane ba taya zakice haka Bayan ba Aure tayi ba kin sanyani cikin duhu"Goge hawayenta Asmy tayi ta ce "Zanfada maki sirrin da muka jima muna boye miki badan komai ba Saidai bamuyi tsammanin zuwan wannan ranar ba Chuchu zan fad'a maki labarin nan saboda na yarda dake kuma zamu iya magance matsalar nan mu Ukku tunda dukanmu mun yarda da juna kuma munzama tsintsiya madaurinta d'aya amma kafin nan kiyimun Alk'awarin bazaki fitar da maganar nan ba tsakaninmu zaki barta a cikinki kamar yanda muma muka barta cikinmu batare da sanin kowaba" kama hannun Asmy tayi ta ce "karkiyi shakkar fad'amun koma meye Asmy wlh nayi maki alk'awarin bamaiji hatta mahaifiyar da ta haifeni bare wani ki daukeni tamkar yanda kuke da zahra " numfashi Asmy ta ja kafin ta fara labartawa chuchu komai daya faru bata boye mata komai ba har alakarta da zahra Sosai Chuchu ta girgiza dajin wannan al'amarin tamkar almara bata tab'a tsammanin hakan ba Sosai zuciyarta ta girgiza dajin wannan bak'ar chakwakiyar da suka shiga "a Gaskiya Asmy kinyi wauta kawai dai mutanen nan yaudararku sukayi Amma wlh akan wai ciwon cikin perioud karyane Ace anyi aikin million's har Talatin a tunani na kawai suna da wata manufar tasu na Auren a Gaskiya a lokacin da kinyi shawara dani wlh da hakan bata faru ba mai faruwa ta Riga ta faru Saidai a kokonci gaba yanzu ina mafita?,Goge hawayen da suka zubo mata Asmy tayi ya ce " ba wace mafita data wuce mu roki Allah ya warware mana wannan sarkarkiyar "numfashi Chuchu taja wayarta Ce tayi ringing dubawa tayi taga ya jaber ne " Cikin Sauri ta d'auka Daga bangarensa ya ce "Kina ina nazo daukarki ina daidai gaban general din ?waidaman Kaine zakazo shine dazu yaya Ya kirani yace yazo harna tafi nemansa bangansaba daman Nasan da wasa yake bazaizo garin nan da Daren nan ba ka jira ni gefen asibitin Kad'an gani nan" tana gama fad'ar hakan ta katse kiran Tare da Kallon Asmy ta ce "Sis muje na d'auki kayana gida zantafi" Haba Chuchu da Daren nan saikace wacce aka kora ai Ammy ma taganki bazataji dadi ba ki barwa Safiya"Girgiza mata kai tayi ta ce "Bazan iya kai gobe garin nanba sis wlh a tsorace nake Matar nan kinajin tana zata hadamu da y'an daban gidansu Gwara na tafi gida, banso kika bari macucin mutumin nan ba ya tafi da momcy naso mutafi gida tare Ammy bazata tab'a kasa fahimtarmu ba amma dai kome kenan zamuyi waya ki taso muje" Goge hawayenta Asmy tayi tare suka jera Chuchu sai leke take Dan har lokacin a tsorace take Hango Motar jaber da tayi yasa hankalinta ya kwanta Jabir na ganin Asmy saida hankalinsa ya tashi tsoronshi d'aya karta ganesa dayake Chuchu ta shiga gaba Asmy ta shiga baya kwata kwata hankalinta ma baya jikinta Hakan yasa bata gane Jabir ba gashi daman dare ne jakar kayanta kawai Chuchu ta d'auko daga gidan su Asmy tayi musu bankwana suka juya Kd ita da jaber da Daren nan Asmy ko Daren ranar kuka ta kwana tanayi bangaren Chuchu sosai Ammy tayi mamakin dawowar tata cikin dare ga yanda ta dawo duk a firgice ba walwala koda Ammy ta tambayeta meke faruwa ce mata tayi ba komai yin duniyar nan Ammy tayi ta fad'a mata abunda ke damunta ta ce Bakomai "To ya akayi kika dawo yanzu bacin ko d'aurin Auren ba ayi ba " Amfasa "ta bata amsa kai tsaye " subhanalla garinya"a Shagwabe Chuchu ta ce "Dan Allah Ammy mubar maganar nan " Hmmm Allah kyauta "kawai Ammy ta fad'a ta rabu da Chuchu Daren ranar da abun Chuchu ta kwana a ranta sosai labarin da Asmy ta bata ya tsaye mata a rai Juyi kawai ta dingayi amma bacci kam Saidai barawo ya d'auketa...bangaren Zahra koda ta farka ta ganta a hannun MD sosai taji takaici da bak'inciki kamar taga kashi haka ta tashi daga kanshi Tana Danasanin saninsa da tayi a rayuwa Toilet ta nufa MD na ganin haka ya sauke ajiyar zuciya Tare da fita Bayan ya rufeta Dan karma ta gudu ta sanyashi cikin wani hali itama ta saka kanta Sai sannan ya samu damar shiga bedroom dinsa yayi alwala Zahra ko a toilet dinma saida Tasha kuka ba wanda take tausayi take tunawa kamar Baba" yana wani hali?ta tambayi kanta"Sosai ta dinga kuka har ciwon kanta ya
Chapter 90 · 0% Book details