Sashe 107
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba daura Aure sukayi dukda ba Abi shara'a ba Amma Naji dad'in ma da Ba wacce y'ar iskar ya haihu da ita ba yarinyar mutunci mai tarbiya da nutsuwa ta haifa masa kuma insha Allahu zahra saita zama tauraruwar mustapha saita kwacesa daga hannun waccen yar iskar yar marassa tarbiya da izinin ubangiji saiya so zahra ya kaunaceta tamkar ransa"Girgiza kai kawai Ammy tayi a ranta ta ce " hakan ta faru da nafi kowa farimciki "kafin ta ce " Ni yanzu damuwata Hajiya bansan me zancewa mutane ba"Barni dasu ni nasan me zance musu zance matarsa ce Zuwan da nayi na aura masa jikar Aminiya ta akwai ubanda ya isa ya ce Ba haka ba "Ajiyar zuciya Ammy ta sauke ta ce Hakane " Haka ko suka fad'awa mutane wanda ba Wanda bai yarda da hakan ba Saidai suce ba a gayyacesu bikin ba Nanfa aka fara shirin yin suna Wanda sosai MD yake rawar kafa ganin mutane sun fara yawa gashi baya samun damar ganin Zahra saboda d'akinta Ammy ta sauketa take kula da ita saboda d'inkin ta Saida ya kira Chuchu ta d'auko masa yaran idan ya gama liliyarsu ya bata ta koma dasu sosai yakeson ganin ,Zahra amma ba dama dinkuna masu kyau Chuchu da Zey suka kaiwa zahra kala"_kala tamkar Lefe kowa dai sai yaba amayar ta MD yake a yanda Ammy tayi musu bayani Asmy ko nan ta dawo take kwana Saboda kula da aminiyarta mamansu ma kullum sai sunzo Dukda sanyin da zahra tayi ana jibi suna Bayan MD yazo part dinsa na gidan yake sauka daman saboda mutane Chuchu Ya kira lokacin tana gefen Ammy dake bawa Babyn ruwa Ya ce "Ki kawo mun triple yanzu " To yaya gani nan"Ammy dake jinsu ta ce "Kice masa Bazaiyi musu hud'u ba " Daga bangaren MD yanajinta ya ce "Kice Hudubar ce zanyi musu" Kallon Ammy tayi ta ce "Yace hud'ubar ce zaiyi musu" Mika mata shi Ammy tayi ta ce "Saiki kai masa su" Zahra ko tanaji tasan da Wanda ake waya daga kwanciyar da tayi ta rumtse ido Tanajin wani iri a ranta rukayya ta dauki d'aya Chuchu ta rik'e biyu koda suka isa part dinsa Gaisheshi sukayi Tare da mik'a masa su "Kamar ko yaushe saida yayi musu addua Sannan yadanyi musu wasa kamar wasu manya Kallon su Chuchu dake shirin fita yayi ya ce " Ku jira ku koma dasu "Dawowa sukayi suka zaune sunzaci y'an mintuna ne amma saida suka kusan shafar awa suna jiransa ga ba damar su tafi saida ya gama liliyar yaranshi ji yake kamar kar atafi dasu Bayan yayi musu Huduba sai sannan ya ce " Zoku tafi da su "Cikin Sauri Chuchu taje ta amshe Su tana Dariya ta ce " Yaya me ka sanya Musu "Namijin d'aya fara mik'a mata ya ce " Yusuf"Sannan ya mik'a mata dayan ya ce "Shi kuma sunan Abba" Macen ya mik'awa Ruqayya ya ce "ita kuma Ammy" Wow Chuchu ta fad'a ta ce "Aiko yaya Harnayi musu nickname " Akhbar,Amar,Ammy kuma little zahra"Murmushi yayi mata ya ce "sunan yayi chuchun yaya Amma takwarar Ammy a sauya bazanso a dinga kiranta da sunan haka ba " hakane yaya Amma ai kaga Ammy ba zahra ake ce mata ba Fatima ake Ce mata"baice komai ba sai lalubo wayarsa da yayi ya ce "Zan miki transfer 10 millions "Kafin jibi ki shirya kayan da za a bawa bak'i jakunkuna, calendar, Turamen atamfofi super Holland da duk abunda kikaga za a raba karki sake ayi harkar karanta kafin gobe komai yazo sannan Jabir yayi wasu jakunkunan anjima zai kawo miki tare da wayoyin da nayi order daga compony duka a sanya a jakar rabon ki tabbatar komai ya tafi successful idan kudinma basu isaba kiyimun waya zanmuku transfer wasu " insha Allah yaya komai zaitafi yanda ake.so"Ajiyar zuciya ya sauke tare da Danna mata transfer Take suka shigo wayar Chuchu koda suka koma Ammy ta tambayesu ta ce "Me.Ya sanya musu" Cikin doki Chuchu ta ce "Ammy baby girl din takwararki ce kuma takwarar momcy Baby boys din kuma wannan Yusuf (Akhbar) wannan kuma Takwaran Abba (Amar)Murmushi Ammy tayi ta ce " masha Allah Ubangiji ya raya "Zahra tana daga kwance kamar tana bacci sosai tayi mamakin karar da yayi mata na sanya sunan mahaifinta tunowa da Baba da tayi ko yana wani hali yanzu ya sanyata Goge hawaye Wurinta Chuchu tayi ta ce " Tashi momcy kinji sunan yaran yayi ko "Bud'e ido tayi a hankali tare da sakar mata murmushi Dan bazata iya magana akan yaran gaban Ammy ba Sai gyada mata kai tayi alamar sunan yayi Ranar suna tunda safe aka yanka gardama gardaman shanaye Guda goma.reras raguna shidda Wanda naman shanayen.duk sadaka aka babbada gidajen marayu da gajiyayyu Sosai MD.ya taka rawar gani a wannan sunan y'an uwan Shima haka uwa uba Ammy data k'asa zaune ta kasa tsaye zahra ko duk yanda bataso tayi kwalliya ba saida Chuchu ta sanyata tun safe take sauyin.latsa latsan kaya hoto ne dai dak'yal ta yarda akayi mata tare da Yaran sannan akayi mata da Ammy da kuma Chuchu da Asmy dukda a sanyaye take saboda sosai taron mutanen ya bata mamaki Sosaifa aka shiga shagali da fidda abinci da baza Naira a bikin triplet gidan Ammy duk Inda ka hanga cike yake da mutane Wasu ma basu sansu ba haka suke zuwa Dan aci banza" Kaji ko yanda kasan Tuwo haka aka maidashi a gidan duk Wanda yaje sunan nanfa tofa ya shaida Sunzo gidan kudi sunzo Inda ba a tausayin naira Duba ga irin Abubuwan da aka rarrabama kansu ya isa mutum girgiza K'atuwar jika mai d'auke da hotunan yaran da sunansu cikinta galleliya Atamfa Holland banda Callender sai Tab d'in yara a ciki Kirar Iphone wacce kudinta ma saiya girgiza mai karatu mutane ganin amfara basu wannan Abun duniyar nanfa aka rude Wasu Dasun fito suke kiran y'an uwansu akan suzo kar ayi basu Babu alamar karewar kayan rabo saboda daman masu uban yawa akayi Chuchu itace gaba gaba kan rabo ita da Asmy duk anshiga busy ga ba ruwansu da wai sai Wanda suka sani Kowa bashi ake saboda ranar farinciki ce acewarsu duk Wanda yazo murna yazo tayasu hakan yasama suka sanya security barin kowa ya shiga amma fa sai anyiwa mutane bincike kafin Su shiga saboda karsu shiga da mugun Abu Chan na Hango *Auren wata tara*Fans Gungunsu guda Ni kaina nayi mamakin Ganin irin yawan sunfi a kirga Wanda ba ma zan iya kiran sunan su ba chan na hango khadyn sp ana yagar cinyar kaza Rachel ko ina kallonta tana zuba wasu kajin a ledar da tataho da ita su ummu suhaif sai washe baki ake banza ta samu,su halimatu ko an sha goggoro yanda kasan itace chuchu su fatima sai zazzakewa ake tana sune kirjin biki sunan ammy da amarya zahra gareta yan uwansu ne ai,chan na hango quen faridat suna fada da wata tana cewa zata sa security su fitar da ita batasan yanda suke da md ba to cousine brother dinta ne nikam hajjo ina rike da takarda da alkalami nace zuķ'i,su tsohuwa maman Siddiqa sai shafce zufa ake,su aisha,zainab oum ibisam ,jikalle ruky ,rahama ,maman nana,su nafisa kai sauran bazasu fadu ba wollah anyi kara Maman Khairat ita ce gaba Wajen yi musu jagora Akan suma suje su Amso nasu kason raba su gida hud'u tayi ta ce"Kunga ku bari mu kasu hud'u karsu ganmu gayya guda suce daman kayan suka kawomun kashi d'aya mu fara shiga kafin Sauran tunda Kunga munyi yawa "Ummu shugaba ce tayi k'araf ta ce " Wlh bazaiyu ba maman khairat kawai mu shiga gaba d'aya sanadin wanda suka fara shiga su su samu kawai mu mu rasa wlh bazaiyu ba "Ganin suna shirin yin sama ya sanya maman khairat cewa to shikenan muje mu Duka din Tunda bakusan ayi Harkar da baza a raina mu ba dukansu suka runkuta suka shiga kowa ya fito zaka kalli fuskarsa cike da farinciki sai wage baki suke kowa sai murna yake banda Sherston ghayu da ta fito hawaye jabe jabe da fuskarta wai bata samu rabo ba sosai na tausaya mata ganin yanda take kuka cikin bila'adadin mutane ita kadai ta rasa Allah sarki maman ummy da tausayi cewa tayi Dan Allah mu hada mata ko wani Dan abun ne a bata ,mutanen namu najin haka aka fara sassanfewa chan na hango lolos ta maida nata cikin hijab ta dukunkuneta ,mom shukurama cewa tayi tofa mu ma'assalam dadyn shukura yayi kira ,ummu suhaif da ummu rafi a sukace jiramu muma sun kira bansan yanda yan auren wata tara fans suka wansheba saboda barin wajen da nayi na kutsa ciki chan na hango zahra tasha tsadadden lace da yayi mata mugun kyau yanda kasan matar president Tripple dinta ko sunsha kyau cikin tsatsadan kayansu zey ta kasa ta tsare akan yaran ba a daukarsu kar a jagular su ganin Zahra a matukar gajiye take ga cs dinta da bata warke ba ga kaya masu nauyi da ta sanya ya sanya Ammy da itama tasha kyau kama hannunta ta kaita wani part din ac ta kunnawa dakin bayan ta sanyata tayi wanka ta sauya kaya kan gado ta kwanta daman gajiye take saida ammy taga bacci ya dauketa tukwana ta fita bayan ta rufe mata dakin taro ya tashi lafiya cikin girma da dattako anyi Abu na bajinta da nuna sa a md ma lunch suka shirya hatta abokanan kasuwancin shi na kasashe saida sukazo wajen lunch dinma haduwar da yayi bata baki ne iya maza kadae akayi anci ansha kafin dare ma labarin sunan triplet din,md sun baza duniya sakamakon yan jarida da suka ziyarci wajen event din da wajen sunan kuma md ba boyayya mutum bane da dare abban amira yaga bikin sunan a news cikin tsananin mamaki yacewa matarsa me nake gani haka hajiya itama tana mamaki ta ce "nima abunda na gani md yana da wata matar ne daman bayan amira"cikin tsananin tashin hankali ya dannawa amira kira a layin ta na chan kasar lokacin amira na bacci ringing din wayar ya tasheta cikin muryar bacci ta ce"hello dad cikin tashin hankali ya ce "Kina ina daughter labarin Me nake gani wai